Wannan ba wani abin mamaki ba ne, domin ba wata hujja ta al’ada da ta hankali da ta hana ‘ya’yan kani su girmi ‘ya’yan wa, mussam idan ya zamana tazara tsakanin yan’uwa biyun ba mai yawa ba ce kamar yadda ya kasnce tsakanin Hasan da Husain (a.s). Domin lamarin ya dogara da yanayi da dabi’a da kuma halitta da zauki. Na farko ke nan. Na biyu, idan muka kaddara cewa Kasim da Abdullah su ne kanana a kan ‘ya’yan baffansu Husain (a.s) watau Sajjad da Aliyul Akbar (a.s). Sai dai wannan ba ya nufin duk ‘ya’yan Imamu Husain sun girmi ‘ya’yan Imamu Hasan (a.s), akwai wanda ya grime su shi ne Hassanul Musanna bin Imamu Hasan (a.s) wanda mai littafin Bihar ya ruwaito game da shi cewa: “Hasan dan Hasan ya halarci Karbala tare da baffansa Husain (a.s), bayan kashe Husain (a.s) an kakkame saura iyalansa sai Asma’a bin Karijata ya kwance shi daga cikin daurarru ya ce: Wallahi ba wanda zai daure ‘ya’yan Kaulah ina raye. Sai Umar bin Sa’ad ya ce: ku kyale wa Abu hassa’an (Asma) dan yar’uwarsa. Da ma an daure shi ne jina-jina da sara da suka ko’ina a jikinsa. An ruwaito Hasan bin Hasan (a.s) ya je neman auren daya daga cikin ‘ya’yan baffansa Imamu Husain (a.s), sai Imamu Husain (a.s) ya ce: “Ya dana zabi wacce ka fi so”. Sai Hasan ya ji kunyar ba da amsa. Sai Imamu Husain (a.s) ya ce masa to ni na zaba maka ‘yata Fadima ita ce ta fi su kama da mahaifayata Fadima ‘yar Manzon Allah (s.a.w)[1].