ruwan da yake fita daga jikin dan adam idan aka cire Bawali da Maniyyi ya kasu kamar haka:
Na daya: Ruwan da yake fitowa bayan bawali kuma yana da danko kadan wanda ana kiransa Madiyyi.
Na biyu: Ruwan da yake fita yayin jjin dadi tun kafin sha’awa ta kai kokoluwa, kuma kafin fitar Maniyyi, wannan ana kiransa Maziyyi.
Na uku: Ruwan da ke fita a wasu lokuta bayan fitar Maniyyi, ana kiransa Waziyyi. Dukkanin wadannan masu tsarki ne (tsarkakakku ne) su matukar ba su cudanya da maniyyi ko fitsari a lokacin da suke fitonwa ba, kuma ba sa bata alwala ko wanka. [1]
[1] A koma Imam khomain a cikin Taudhihul masa’il (mai hashiya), bani hashimi Khomaini, Sayyid Muhammad Husain, j 1 shafi na 63, daftari intisharat islami, kum, bugu na takwais, shekara 1424. BHW.