Abin da ake nufi da Kalmar ”Rawukan da suka sauka a Farfajiyarka” su ne Shahidai, wadanda suka yi Shahada tare da Shugaban Shahidai (A.s) a Filin Karbala.
Wadannan su ne Dalilan da suke Tabbatar da haka;
- A bisa Al’ada masu Ziyara wadanda suke da Rai ba a Kiransu da Sunan arwah. (Rayuka)
- Ita wannan Ziyara Zance ne daga wanda ya kawo Ziyara, a bisa Al’ada ba zai Zamo da mai Zance da wanda ake Zance da shi, a kira su da suna Daya ba.
- Dukkan Addu’o’in Ziyara da aka ruwaito ga Imam Husain (A.s) babu yin Sallama ga masu kai Ziyara Gare shi.
- An Ruwaito Ziyarar Ashura ne tun Kafin a Bisine Wadanda suke Kwance na yanzu a wurin, wannan ya nuna kenan, Kalmar Rayuka ba ta Nufin dukkan Wadanda suke Kwance a wurin.
- Daga cikin Kalmomin Shaidu da ke cikin wannan Ziyara zamu iya Fahimtar cewa Kalmar Rawukan Wadanda ake musu Sallama, su ne Shahidai wadanda suka yi Shahada tare da Shugaban Shahidai a Filin Karbala, domin yazo a cikin wani wurin, za’a yi Sallama ta Musamman ga Wadanda suke tare da Imam: (Amincin Allah ya Tabbata ga Husain da Ali Dan Husain da Yayan Husain da Sahabban Husain”
Kuma Kari aka haka shi ne cewa ai Ita Ziyarar Ashura, a Dunkule ta Kunshi yin Sallama ne ga Shugaban Shahidai da “ya” yansa da da Sahabbansa, da kuma bayyana so, da cika Alkawari ga Imam, da kuma Nesantar Makiyansa.
- Yazo a cikin wata Ziyara ta Ashura, Kalmar da take cewa: Amincin Allah ya Tabbata a gare ka da kuma Rawukan wadanda da suka sauka a Farfajiyarka, (Hallat da Anakhat) suka yi Jihadi don Allah a tare da kai, suka sayar da rawukansu don Neman Yardar Allah a cikin al” amarinka[1] Acikin wannan Jumlar wasu Suffofi sun Fito, irin su yin Jihadi a Hanyar Allah, tare da Shuigaban Shahidai (as) da yin Shahada don neman Yardar Allah tare da Shugaban Shahidai.Wadannan Siffofi sun zo ne bayan Siffanta su da Kalmar (Hallat da Anakhat) wato Sauka a Farfajiyar Shugaban Shahidai (as)
daga wadannan Kalmomi za a Fahimci cewa[2] Kalmar Rayuka da a ke nufi shi ne Rawukan Shahidai Wadanda suke tare da Shugaban Shahidai.
- Yazo a cikin wata Addu’a ta Ziyarar Ashura, banda waccan da ta Shahara[3] Ana cewa: Amincin Allah ya Tabbata a gareka, ya Baban Abdullah Al Husain, da wadanda suka taimaka maka suka ba da taimako, suka Tayaka da Kawukan su, suka Mika Wuyayen su a wajen Kariya gareka, ….Aminci ya tabbata a gareka ya Shugaba na, (Aminci ) ya tabbata a gare su , da Ruhinka da Ruhinsu da Turbarka da Turbarsu , Aminci ya tabbata a gareka, ya dan Shugaban Halittu, da wadanda suka yi Shahada a Tare da kai.
Daga wadan nan kalmomi za’a iya fahimta a fili cewa Kalmar rawukan da ake nufi su ne shahidan da suka yi shahada a tare da shugaban shahidai.
- Yazo a cikin wata Ziyara ta Shugaban Shahidai (as) Bayan an Karanta Ziyarar Imam Husain da Aliyyul Akbar (AS) sai a Fuskanci Shahidan Karbala a karanta wannan Ziyarar…….kuma Zamowar a cikin Dukkan Addu’o’in Ziyarori ga Shugaban Shahidai, babu yin Sallama ga masu Ziyara ko ga Wadanda aka Bisne su a wurin, zamu samu Natijar cewa abisa la’akari da Gamammiyar addu’o’in Ziyarori na Ashura da sauran Ziyarori na Shugaban Shahidai, ba tare da wani Kokwanto ba zamu iya cewa Kalmar Rawukan da ake Sallama a gare su Acikin Ziyarar Ashura su ne Shahidan da suke tare da Shgugaban Shahidai (as) (a lokacin shahadarsa).
[1] Sayyid Ibn Tawus, Ikbalul A’mal Juzu’i 3 Shafi-70
[2] Itace Ziyarar da take da irin Ladar Ziyarar Ashura, ga wanda ba zai iya yin dukkan Ladubban Ziyarar Ashura ba (na yin Kabbara da La’anta 100 da yin Sallama 100 da yin Sujuda da Sallah da yin Addua bayan ziyara) Mafatihul Jinan.
[3] Za’a iya Fahimtar hikimar Jinkirta Fadin Kalmar yin Jihadi da Shahada, sai bayan an Ambaci Kalmar (Hallat da Anakhat) Wadanda suke nufin Sauka, cewa Kalmar Rayuka na nufin Shahidan da suka yi Shahada a Ranar Ashura A tare da Shugaban Shahidai (as) .