Dangane da rada sunan (Ya’asin) akwai zantuka da aka ruwaito da ke nuna rashin yardar Imamai (a.s), game da amfani da sunan ga mutane. Kan hakan za mu iya kawo ruwayar da Imam Sadik (a.s), ya ke ce wa: “Muhammadu dai an muzu izini su rada, to Yasin fa wanene ya musu izinin?! Ya na nufin sunan na Annabi ne (s.a.w).[1]
Wannan ruwaya bata da salsala mai kyawu don haka masana ba su yi aiki da ita ba. Don haka bata da karbuwa. Sai dai hankalin mutum shi zai yi hukunci a irin wadannan wurare da babu tilas ko kunci. Idan ya yi amfani da taka tsantsan wajen amfani da wasu kyawawan sunaye –ga su nan da yawa- da babu wani hani kan amfani da su, to sai ya kyale wannan sunan.
[1]. Kulaini Muhammad bin Ya’akub a Alkafi j 6 sh 20, hadisi na 13, “ Daga mutanemmu masu yawa daga Ahmad bin Muhammad bin Khalid bin Isa bin Safwan ya daga zuwa ga abu Abdullah (a.s). an buga darul kutubul Islamiya, dab’e na huhdu 1407 HK.