Ba yadda za a wani aiki ya fita daga iradar Allah mai hikima, wannan iradar ta Allah tana nan a ko da yaushe a rayuwar mutum a kowane lokaci da zamani, da dukkan dokokin rayuwa ba tare da ta cire wa mutum zabin da yake da shi ba ta takura masa zabar hanyar da bai yi nufi ba. Don haka babu wani abu da zai wakana a rayuwar mutum sai da nufin Allah da iradarsa ta tun azal mai gudana ta hanyar zabin mutum.
Tasirin Allah na daga hikimar Allah madaukaki ba ya fita daga dukkan duniyar halitta ko a rayuwar mutane, don haka ne muka samu sunnar Allah tana gudana a duniyar samuwa tar da halartar iradar Allah a domain a dokoki rayuwa, ba zai yiwu a kauce wa iradar Allah ba don samun ci gaban mutum zuwa ga kalama, wannan kuma shi ne mafi dadewar dokar Allah a rayuwar halittunsa tun azal da take hukunci da komai.
Gano wadannan dokokin da samun su cikin rayuwar halittunsa ba ya takaituwa da tasirin da ake gani a rayuwar zahiri kawai, da yawa daga abubuwan zahiri da badini, na bayyane da na boye dukansu akwai tasiri – a sane, ko ba sane ba- a dukkan wata mas’ala, da faruwar wadannan lamuran da bayyanarsu duk yana karkashin samun izini da zartarwar Allah ne a fili a cikin dukkan rayuwar daidaikun mutane.
Da wannan bayanin ne zamu ga cewa ba zai yiwu a samu kowace irin tawaya ba ta fuskacin ubangiji wanda yake shi ne mai baiwa baki daya. Daga karshe kuma iradar mutum da zabinsa cikin zabar hanyar da ya ayyana wa kansa ita ce ake gani a matsayin asasi don tabbatar iradar Allah madaukaki, kuma ya kasance yana da tasiri wurin gina dan Adam da kalamar mutum.
Don haka amsa ita ce: ba zai yiwu wani aiki ya fita daga iradar Allah mai hikima ba, wannan iradar ta Allah tana nan ko da yaushe a rayuwar mutum a kowane lokaci da zamani, kuma ko da mutum ya kasance yana da hadafi maras kyau ne, to duk da haka zai samu inaya da ludufin Allah, kuma zai samu taimakon daga rabon iradar Allah a wannan hanyar da ya zaba, wannan zabin ne yake ba shi dama ta musamman. Kuma daga mafi girman ludufin Allah ga mutum shi ne ya bar shi ya zabi hanyarsa da kansa, amma duk da haka Allah madaukaki da tausayinsa da rahamarsa maras iyaka ba ya jingina mutum da kansa, yana kuma tanadar masa da yanayi ne da zai zabi abin da ya fiye masa.
Kuma dukkan abin da mutum yake so a wannan duniya –tare da la’akari da mafi girman maslahar da yake so- zai samu amsa daga Allah madaukaki, kuma wannan lamarin yana nan a cikin rayuwar kowane mutum, shin wannan abin da yake nema na duniya ne ko na lahira, tare da hakan zamu samu cewa iyakar da mutum yake da ita game da burinsa na duniya, da kuma karo da juna da ake samu tsakanin abin da yake buri na duniya da kuam abin da yake hadafi na rayuwar lahira madaukakiya, sai mu ga mutum yana kauce wa wannan abin da yake so na duniya, yana fuskantar hadafin da yake shi ne asasin halittarsa na rayuwar dawwama ta lahira.
Don haka babu wani mai hukunci a rayuwar mutum sai iradar Allah ta azal mai gudana ta hanyar zabin mutum, wannan iradar kuwa tana kasancewa a cikin wasu yanayoyi da sharuddan ayyanannu ne a wannan duniya, wannan kuwa domin samun shiryawa hanyoyin da dan Adam zai samu kamala.
Muminin mutum sakamakon sanin sa da hakikanin zahirin rayuwar duniya mai hukunci kan duniya yana ganin wannan duk yana daga tausayin Allah ga bayinsa ne da ludufinsa, yana fahimtar hakikanin hakan gare shi, yana neman sa’ada da arzuta da dacewa ta har abada daga wurin Allah madaukaki a dukkan yanayin da ya samu kansa cikinsa, wannan mutumin bayan ya kai ga matakin sallamawa da yarda da Allah, to daga karshe sai ya fita daga dukkan wani abu na bukatar jin dadin duniya, ya kai ga saduwa da mafarar kudurar Allah da rahama maras iyaka.