A lokacin samun canjin turan kiristoci sun samu matsala da ta kai su ga cewa addini yana da tawaya, kuma ba zai iya biyan bukatun mutane sababbi ba a fagen siyasa da zaman tare, don haka sai suka kai ga tunanin raba addini da siyasa.
Sai aka samu baruwan addini da siyasa a matsayin tunani mai ci a yammancin duniya, domin an samu karkacewa a tafarkin addini da suka samu, wanda yake cike da son rai da tsakude, da wannan ne ya kasa amsa bukatun al’umma.
A zamanin sabuwa haihuwa (sabon zamani)[1] na tsakiyar karni na sha biyar miladiyya ne aka fara samun tunanin Rum da Yunan na da a cikin yammancin duniya, sannan kuma a zamanin samun gyara da canji[2] a karnin na sha shida aka samu kafa shi ta hannun ma’abota addini kamar Luta, don haka a lokacin wayewa[3] a karni na 17, da 18 miladiyya sai ya samu gudanawa da kama wuri ta hanyar tunanin amfani da hankali da binciken ilimi. Kiristoci sun fuskanci cewa kiristanci yana da tawaya ba zai iya biyan amsoshin wannan zamanin ba da suka hada rayuwar al’umma, ala’adu, siyasa. Don haka ne suka shelanta cewa addini ya zo ne kawai don nuna alakar mutum da Allah da lahirarsa, ba shi wani abin cewa a fagen siyasa da rayuwa, kuma da wannan ne aka samu yaduwar tunanin raba addini da siyasa, da musanta komawar mutne zuwa fagen addini yayin da suke da tambayoyi kan al’adu da siyasa da rayuwa, sai aka samu bayyanar malaman falsafa na cire addini[4] suka rika zuwa daya bayan daya.
Bisa la’akari da aibn da aka samu game da tunanin kiristanci ana iya cewa akidar cire addini ta samo ne daga ci gaban yamma , domin muna gani a fili sakamakon karkacewar koyarwar addini da bin son rai da ya samu kiristanci ne da aka cakuda su da koyarwar addini sai ya zama ba zasu iya biyan bukatun dan adam ba a kowane zamani, don haka sai addinin isa (a.s) da ba shi ne addinin karshe ba kuma isa (a.s) bai taba da’awar cewa babu wani Annabi (a.s) bayansa ba, ya ma karfafa cewa akwai “ahmad” da zai zo bayansa (a.s).
Amma musulunci addinin karshe ne kuma ya samu kariya daga karkacewa, don haka ba shi da matsalar da ta samu kiristanci taraba addinin da siyasa, sam wannan bisa hakan ba shi da wani wurin zaman a addinin musulunci, sai aka samu wasu masu neman kwaikwayon yammacin duniya suna maimaita irin wadannan maganganun suna masu zaton cewa idan suka kawo wannan tunanin zasu iya sanya duniyar musulmi ta samu ci gaba ne. misali akwai Dr. Jabir Usfur a abin da ya rubuta a mukaddimar littafin “al’islam wa usulul hikam” -da Ali Abdurrazaka ya rubuta- yana cewa: mu muna alfahari da mutane kamar Dahdawi, Muhammad Abduh, da Ali Abdurrazak, kuma da su ne muke koyi, domin sun kasance masu goyon bayan ci gaban wayewar wannan zamanin.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi tehrani, wilayat wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
2. Mahdi Hadawi tehrani, bawarho wa fursish’ho, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na daya, 1378.