Ayar da ta zo cikin tambaya, tana bayani ne a kan tunani da akida na kafiran jahiliya da suke cewa yaya mata ‘ya’yan Allah ne. Allah madaukaki a cikin wadannan ayoyin ya yi amfani da dalillai wadan da kafirai suka yadda da su domin ya nu na masu kuskuren su dan gane da lika ma Allah yaya mata; saboda su sunfi son yaya maza akan yaya mata, domin atushe suna ganin cewa yaya mata ‘ya’yan Allah ne. a nan Kur’ani ya kawo siffofi biyu wadan da mata suke da su kuma wannan ya na komawane ga halittar su ne ta tausai, na daya alaka mai tsanani da suke da ita ga kayan ado kamar su zinari da azurfa, sai na biyu rashin iyawar su wajen tabbatar da abin da suke nufi yayin gardama ko kuma tattaunawa kuma wannan yana faruwane sakamakon kunyar su. Abun lura a nan shi ne bawai Allah yana nufi ya kaskantar da su ne ba shiya say a halitta su haka ba, aa sai dai abun nufi a nan shi ne ina halittar wadannan halittu da zasu zam ‘ya’yan Allah madaukaki? Amma ba mamaki ya zamo ana nuni ne da cewa su ni'imomine na Allah madaukaki, kamar yadda manzon Allah mai tsira da aminci yake cewa: ya mace kamar furen fulawace mai kamshi wadda na ke turare da shi.
Ayar da ta zo cikin tambaya, tana bayani ne a kan tunani da akida na kafiran jahiliya da suke cewa yaya mata ‘ya’yan Allah ne. Allah madaukaki a cikin wadannan ayoyin ya yi amfani da dalillai wadan da kafirai suka yadda da su domin ya nu na masu kuskuren su dan gane da lika ma Allah yaya mata; saboda su sunfi son yaya maza akan yaya mata, domin atushe suna ganin cewa yaya mata ‘ya’yan Allah ne. wani lokaci kafa dalili da abin da mutun ya yi imani da shi yana da tasiri wajan saurin yaddarsa da abin da saka fada ma sa ta yadda zai sa ya canza tunani. Saboda Karin haske dan gane da abin da muke son yin magana a kai zamuyi ishara ga wannan ayar;[1] shin Allah ubangijinku ya rikama kan sa yaya mata?'' ام '' {am} a cikin ilimin nahawu tana zuwa ne a lokacin tambaya ta inkari wato mai tambaya ya na yi ne bawai dan bai sani ba sai dai dan ya kure wanda yake ma tambayar kuma tan a ba da ma' anar '' بل''. [2]; sai ku ka kadaita yaya maza kawai zuwa kare ku? Wannan ayar ta yi kama da wata ayar wadda take cewa; duk lokacin da a kayima dayan su bushara da samun ya mace wadda suke kamantawa da Allah ; domin dan mutum ya kamata ya yi kama da shi haka kuma dan Allah ya kamata su yi kama da shi – don haka duk zamani da akayima dayan su bushara da samun ya mace sai ka ga fuskokin su sun yi baki suna kuma masu bakin ciki da jin wannan labarin, sai Allah ya tuhumai su sakamakon wannan aikin na su ; shin wadanda suka kirma cikin kayan alatu {zinari da azurfa} ma 'ana kuna masu lika ma Allah yaya mata alokaci guda yaya mata ba su da karfin magana da tattaunawa.
A hakika wannan ayar kamar yadda muka ambata a baya na nuna kuskure ne na mushrikan zamanin jahiliya. Su ne mutanen da suke bakin ciki domin samun labarin an Haifa masu ya mace, amma a lokaci guda kuma suna daukar mala'iku a matsayin ‘ya’yan Allah mata, Allah madaukaki a cikin wannan ayar ya na cewa; shin wadanda suka girma cikin kawa da ado, kuma a lokacin magana ko tattaunawa ba su da karfi ko ikon isar da manufar su, su ne ku ke ce wa ‘ya’yan Allah amma yaya maza su ne ‘ya’yan ku?. A nan kuma sai Kur’ani mai girma ya kawo siffofin mata guda biyu wadan da mafiya yawan mata suna da su domin yaya mata hallitune masu tausai na daya so mai tsanani da sukema kayan ado {zinari da azurfa}, da kuma rashin iya tabbatar da abin da suke son tabbatarwa ya yi magana ko gardama saboda kunyar da suke da ita. amma za a yi samun wasu matan da ba su damu da kayan ado ba {zinari da azurfa} sannan kuma son kayan ado dai dai kwarkwado ga ya mace ba laifi ba ne, sai dai musulunci ya na nufin wasu matan ne da son kayan ado da na kawa da suka mamaye su fiye da hadi sai ka ce cikin su suka girma {kayan adon}. Wani sanannen abu ne akwai wasu matan da ke da ikon da karfi na magana ta hankali, amma wannan ba yana nufin cewa da yawa mata ne ke da wannan ikon ba sai dai abun da yafi yawa shi ne idan zaka hada mata da maza to zaka samu mata sun fi maza kunya kuma wannan kunyar ke hana su magana don haka ne maza suka fi su karfi da iya isar da sakon da suke bukata.
Bukata a nan shi ne ta yaya ku ke alakanta ma Allah yaya mata ku kuma ku dauki yaya maza?[3].
Ba mamaki ya zam haka cewa su kabilun larabawa mutane ne da suke son yin galaba kan abokin gaba ya yi magana ko yayin yaki kuma suna tagama da jarunta da fasaha dan haka wadanda ba su da wadannan siffofin suna cikin kawa ne, don haka ne Allah madaukaki ya ke hukunta kafirai domin sun lika masa yaya mata. [4]
Abun lora a nan shi ne Allah ba wai yana nufin ya kaskantar da yaya mata ne bas hi yasa ya halitta su hakan ba, sai dai yana nufin ina shi ina wadannan halittun da za ace su yayan sa ne? a cikin maza ma hakan zai iya faruwa misali namijin da bukatar sa shi ne yaci ya yi barci ya kuma bukaci mace shin zai iya zama iri daya da Allah?[5]
Kuma zai iya yiyuwa cewa su yaya mata ni 'ima ce ta Allah madaukaki kamar filawa mai kamshi; shin donmi ba ku son samun wadannan yayan? Manzon Allah mai tsira da aminci ya na cewa; ya mace filawa ce mai dadin kamshi wadda na ke amfani da turarainta. [6]
An rawaito wani mutum yana kusa da manzon Allah sai ana bashi labarin anyima sa haihuwa dajin wannan labarin sai kalar fuskar sa ta juya sai ma'aiki mai daraja ya tambaye shi mi ke faruwa ne? sai mutumin ya amsa ma ma'aiki cewa; alherine. Sai manzo ya ce; ka fadaman miya faru ne. sai mutumin ya ce na baro gida ne matata na yin nakuda, sai labara ya saman cewa matata ta Haifa man ya mace. Sai manzon Allah ya ce; kasa zata dauke ta kuma sama zata yi mata inuwa kuma Allah zai bata arzikinta, ‘ya mace fulawace mai da din kamshi wadda na ke amfani da turarainta. [7]
[1] Zukhraf. 16, 17 .
[2] Tabrasi majma'aulbayan fi tafsirulkur'an, fasarar masu fasara jildi na 22, shafi na 200. Yadawa farahani, Tehran. 1360 s
[3] Makarim, nasir, tafsire namune. Jildi na 21, shafi na 25-29. Darulkitab islamiya. Tehran. Bugu na 21
[4] Kashani, mulla fatahi ali, tafsir manhajlsadikin fi ilzam mukhulifin, jildi na 10 shafi na 241 wurin said a littafi na Muhammad Hassan alimi, Tehran, 1366
[5] Kureshi, sayid ali akbar, tafsirinihsanulhadis, jildi na 10, shafi na 18, buyande bissat, Tehran 1377s.
[6] Sheikh saduk, man la yahzarulfakih, jildi na 3, shafi na 481, h 4693 bugawa jame mudarisin, 1413k
[7] Kulaini, alkafi, jildi na 6 shafi na 6 darulkitabulislami, Tehran 1365s