advanced Search
Dubawa
12863
Ranar Isar da Sako: 2010/06/30
Takaitacciyar Tambaya
mene ne gwargwadon tasirin Allah madaukaki a rayuwar mutum?
SWALI
mene ne gwargwadon tasirin Allah madaukaki a rayuwar mutum?
Amsa a Dunkule

Ba yadda za a wani aiki ya fita daga iradar Allah mai hikima, wannan iradar ta Allah tana nan a ko da yaushe a rayuwar mutum a kowane lokaci da zamani, da dukkan dokokin rayuwa ba tare da ta cire wa mutum zabin da yake da shi ba ta takura masa zabar hanyar da bai yi nufi ba. Don haka babu wani abu da zai wakana a rayuwar mutum sai da nufin Allah da iradarsa ta tun azal mai gudana ta hanyar zabin mutum.

Amsa Dalla-dalla

Tasirin Allah na daga hikimar Allah madaukaki ba ya fita daga dukkan duniyar halitta ko a rayuwar mutane, don haka ne muka samu sunnar Allah tana gudana a duniyar samuwa tar da halartar iradar Allah a domain a dokoki rayuwa, ba zai yiwu a kauce wa iradar Allah ba don samun ci gaban mutum zuwa ga kalama, wannan kuma shi ne mafi dadewar dokar Allah a rayuwar halittunsa tun azal da take hukunci da komai.

Gano wadannan dokokin da samun su cikin rayuwar halittunsa ba ya takaituwa da tasirin da ake gani a rayuwar zahiri kawai, da yawa daga abubuwan zahiri da badini, na bayyane da na boye dukansu akwai tasiri – a sane, ko ba sane ba- a dukkan wata mas’ala, da faruwar wadannan lamuran da bayyanarsu duk yana karkashin samun izini da zartarwar Allah ne a fili a cikin dukkan rayuwar daidaikun mutane.

Da wannan bayanin ne zamu ga cewa ba zai yiwu a samu kowace irin tawaya ba ta fuskacin ubangiji wanda yake shi ne mai baiwa baki daya. Daga karshe kuma iradar mutum da zabinsa cikin zabar hanyar da ya ayyana wa kansa ita ce ake gani a matsayin asasi don tabbatar iradar Allah madaukaki, kuma ya kasance yana da tasiri wurin gina dan Adam da kalamar mutum.

Don haka amsa ita ce: ba zai yiwu wani aiki ya fita daga iradar Allah mai hikima ba, wannan iradar ta Allah tana nan ko da yaushe a rayuwar mutum a kowane lokaci da zamani, kuma ko da mutum ya  kasance yana da hadafi maras kyau ne, to duk da haka zai samu inaya da ludufin Allah, kuma zai samu taimakon daga rabon iradar Allah a wannan hanyar da ya zaba, wannan zabin ne yake ba shi dama ta musamman. Kuma daga mafi girman ludufin Allah ga mutum shi ne ya bar shi ya zabi hanyarsa da kansa, amma duk da haka Allah madaukaki da tausayinsa da rahamarsa maras iyaka ba ya jingina mutum da kansa, yana kuma tanadar masa da yanayi ne da zai zabi abin da ya fiye masa.

Kuma dukkan abin da mutum yake so a wannan duniya –tare da la’akari da mafi girman maslahar da yake so- zai samu amsa daga Allah madaukaki, kuma wannan lamarin yana nan a cikin rayuwar kowane mutum, shin wannan abin da yake nema na duniya ne ko na lahira, tare da hakan zamu samu cewa iyakar da mutum yake da ita game da burinsa na duniya, da kuma karo da juna da ake samu tsakanin abin da yake buri na duniya da kuam abin da yake hadafi na rayuwar lahira madaukakiya, sai mu ga mutum yana kauce wa wannan abin da yake so na duniya, yana fuskantar hadafin da yake shi ne asasin halittarsa na rayuwar dawwama ta lahira.

Don haka babu wani mai hukunci a rayuwar mutum sai iradar Allah ta azal mai gudana ta hanyar zabin mutum, wannan iradar kuwa tana kasancewa a cikin wasu yanayoyi da sharuddan ayyanannu ne a wannan duniya, wannan kuwa domin samun shiryawa hanyoyin da dan Adam zai samu kamala.

Muminin mutum sakamakon sanin sa da hakikanin zahirin rayuwar duniya mai hukunci kan duniya yana ganin wannan duk yana daga tausayin Allah ga bayinsa ne da ludufinsa, yana fahimtar hakikanin hakan gare shi, yana neman sa’ada da arzuta da dacewa ta har abada daga wurin Allah madaukaki a  dukkan yanayin da ya samu kansa cikinsa, wannan mutumin bayan ya kai ga matakin sallamawa da yarda da Allah, to daga karshe sai ya fita daga dukkan wani abu na bukatar jin dadin duniya, ya kai ga saduwa da mafarar kudurar Allah da rahama maras iyaka.

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

  • menen hukuncin kallon fim din biki mai tada hankali da sa sha’awa.
    9742 2018/11/04
    Kallon wannan fim din laifi ne kuma ya haramta, kuma lalle ne ki nisanci sake kallon sa, amma dangane da kallon farko wanda ba ki san me ya ke cikinsa ba shi ma kin yi laifi tun da tun a farko ya kamata ki gasgata babarki da ...
  • A Wane lokaci tarihin musulunci ya fara?
    8723 تاريخ کلام 2019/06/16
    Bayan aiko Manzon Allah (s.a.w) zuwa lokacin da iyakancin zagayen fadin daular musulunci ta kasance a iyakancin wani yanki daga kasan saudiyya a yanzu, a sakamakon karancin adadin musulmai da kuma Karancin faruwar mihimman abubuwan (da za‘a ayi amfani da su a KirKiri tarihi), kari a kan ...
  • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
    8097 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
    Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...
  • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
    8205 Tsare-tsare 2012/07/24
    Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
  • iyakokin daular musulunci zuwa ina ne a fikirar siyasar musulunci?
    20175 Tsare-tsare 2012/07/24
    Musulunci yana da kalmomi da suka hada da "kasa" da kuma "yanki" da "al'umma. Kasa a tunanin fikirar musulunci wuri ne guda daya, kuma dukkan iyakokin da ake da su ba su da wani tasiri wurin rusa kasancewar kasar musulunci da musulmi abu guda ne. kuma wannan ...
  • Me ye matsayi da girman da ke qarqashin xabi’u a fagagen wassanin motsa jiki?
    8733 Halayen Aiki 2012/07/25
    Musulunci bai bar kowanne vangare daga cikin vangarorin rayuwa kara zube ba saboda kasancewarsa gamammen addini ga dukkan duniya, matuqar wannan vangaren zai taimaka ma xan Adam a yunkurinsa na samun kamalar da zata masa jagora zuwa ga rabautar duniya da lahira. Kamar yanda ya ...
  • shin Allama Majlisi na daga cikin wadanda suka habaka Daular Safawiyawa, kana mai yaba wa mahukuntanta?
    6032 تاريخ بزرگان 2012/07/24
    Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya da ma mahukunta na wasu dauloli da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da mamora da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da ...
  • mene ne bambanci tsakanin Dabi’u da Ilimin Dabi’a?
    16558 Halayen Nazari 2012/07/25
    dabi’u a luga jam’I ne na ‘’kulk’’ dabi’a/hali/al’ada. Gamammiyar ma’ana saboda kasancewarta al’ada ko hali mai kyau ko mummuna. Amma ‘’Akhlak’’ dabi’u a cikin istilahi ma’anarsa malaman akhlak sun ambaci ma’anoni masu yawa. Bai yiwuwa a gwama tsakaninsu yanda ya dace. Amma sai dai musulmi ...
  • don me ake kiran annabi Muhammad (s.a.w) amintacce?
    4670 تاريخ بزرگان 2019/06/12
    Amintacce shi ne kishiyan mayaudari, watau ana nufin mutumin da ba ya yaudarar jama’a, kuma kowa ya natsu da shi ya dogara da shi bisa kyawun dabi’unsa. Idan muka waiga zuwa ga halayen Annabi (s.a.w) ta mu’amala da daidaku da al’umma tun a samartakarsa, zamu ga amana ...
  • mene ne hanyar debe kewa da Kur’ani
    10175 Halayen Aiki 2012/07/25
    idan ya zama tilawar da mutum zai yi ta Kur’ani don neman kusanci ne zuwa ga Allah, da tadabburi da bibiyar aiki da shi, to zai zama tilawar ta kusantar da shi ga manufar Kur’ani sosai, zai zama son Kur’ani zai tsananta. ...

Mafi Dubawa