Suratu kausar sura ce da take da ayoyi guda uku, abin da ya fi shahara gun malamai shi ne an sauke ta a garin makka; sannan dalilin saukar ta shi ne yayewa manzon rahama (s.a.w) damuwar da yake ciki sakamakon mauta da gorin da wasu cikin kuraishawa ...
Bama musun yiyuwar wannan ruwaya kai tsaye sai dai wannan ruwaya ba a cika samunta ba sai a litattafan da suka yi nisan zango da zamanin amirul muminin (a.s) nisanda mafi karanci shi ne shekara dubu, marubucin <Auwal musha sheen> na daga marubutan karshe ya ciro wannan ...
A auren dole idan bayan an yi auren (ko da kuwa gwargwadon sakan ne) sai matar ta ji cewa ta yarda da auren to ya inganta, amma a ko wane hali Dan da ta ambata ba zai zama ba na shar’a ba, domin samun Karin bayani a ...
Addinin muslunci na ganin tsarin tausayi da jin kai da tausasawa ita ce hanyar da ta fi tasiri fiye da ragowar hanyoyi, duk da cewa a wasu wurare ya zama tilas idan yaro aikata wani nau'in kuskure a ladabtar da shi ta hanyar dukansa a sakamakon aikin ...
A cikin wasu daga cikin jigon litattafan Ahlussunna akwai wasu ruwayoyi kan wannan lamari wadanda suka doru kan wasu dalilan da ba za su zama karbabbu ba: An rawaito Manzon Allah (s.a.w) “Ya Allah! duk wani musulmi da na zaga to ka sanya zagin da ...
Da farko dai: Hakika wadannan gungun ruwayoyin, ko dai sun zo ne a saboda (Takiyya), ko kuma don wani lokaci ne na musamman, wanda babu wani amfani, ko tasiri, na yin juyin juya hali ta yin amfani da makami, dadin dadawa kuma, akwai kuma wasu ...
Hakika shedan na da zuriya kuma su ma la'anannu ne kamar yadda yake la'ananne, domin su ma bisa hakika sun bi tafarkin sa kuma sun yi riko da hanyarsa da salonsa wajen batarwa da kokarin kautarwa daga tafarkin gaskiya, sun dogara da wannan hanyar a wajen batar ...
Ya Dan’uwa mai girma muna masu baka hakuri sakamakon jinkirin da aka samu wajen aiko maka da amsar tambayarka/ki a sakamakon yanayin ayyuka da suka sha kanmu. “Ammar Dan Yasir Dan Aamir” ana yi masa alkunya da ‘Abu YaKazan” kuma ya kasance abokin rantsuwa ne shi (wato ...
Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na ...
Daga cikin abin da za a iya fahimta daga wanan ruwayar shi ne cewa, isa ga matsayin tauhidi, yana isar da mutum zuwa ga mukami na kariya da masuniyya, kuma isa ga wanan mukamin bazai yiwuba, idan ba a ketaro ta hanyar wilayah ba, madubin da ta ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...