Littattafan riwaya da na tarihi sun tabbatar cewa dan’adam wanda ke kan doron kasa bai kasance an same shi daga Habilu da Kabilu ba, shi dai an same shi daga dan Annabi Adam (amincin Allah ya tabbata a gare shi) na uku mai suna Shisu ko Hibatullah.
A yanzu haka a jamhuriyyar musulunci ta Iran ana ayyana ‘yan takarar majalisar Khubrigan ta hannun shura Nigahban ne. To akwai batun sukan cewa Jagora shi ne yake ayyana ‘yan shura Nigahban, su kuma suke ayyanar cancantar shiga takara ga ‘yan majalisar khubrigan, su ‘yan majalisar khubrigan ...
Marja’anci da ma’anar kasancewar malami makoma ne shi a karbar fatawa wurinsa a fikihu yana kishiyantar ma’anar koyi da malami ne. Domin a ma’anar koyi yana nufin wanda bai kware ba kan wani lamari ya koma wa wanda ya kware, wato yana nufin ke nan a koma ...
Akwai ra’ayoyi mabanbanta masu sabani da juna dangane da karanta littatafan Dr. Ali Shari’ati. Akwai masu wuce gona da iri, akwai masu tauye shi. Sai dai daidaitaccen ra’ayi kan batun shi ne ra’ayin Sayyidul Ka’id Ali Khamana’i. Wannan shi ne ra’ayi madaidaici kuma mafi adalci a wannan ...
Addinin karshe shi ne addnin da aka aaiko da ma'anar cewa bayan wannan addini babu wani addin da za a sake aikowa ko wani dan sako da zai zo. Kamalar addini yana daga cikin sharuddan cikar addninai, da kuam sharadin cewa addinin karhen ba yadda ...
Musulmai tun bayan tafiyar manzon allah (s.a.w) sun rabu zuwa bangarori biyu; a- bangaren farko sun tafi kan cewa za a dogara da ahalin gidan manzo (s.a.w) da komawa zuwa gare su wajan ilimin fikihu da sauran iliman addini da na ...
Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
Lafazin akwati yazo cikin wani bangaren hadisi da mai littafin bihar ya rawaito, hakan yazo cikin fadinsa madaukakin sarki “hakika alamar mulkinsa ita ce akwati da zai zo muku dashi, acikinsa akwai nutsuwa daga ubangijinku”, wasu daga malaman tafsiri sun fassara ma’anar akwati da cewa ita ce ...
An rawaito hadisi rafa’i daga manzo (s.a.w) da kamanni biyu, daya ya kunshi shari’a da wajabcinta ko daukakar lamarinta kan mutum kamar na aikin da ke kan kowane baligi cikin mutane, na addinin musulunci, a daya bangaren kuma hadisi rafa’I, girman nauyin shari’a wato takalifin hukunce hukuncen ...
Allama Majlisi (RA) ya ruwaito a cikin littafinsa Biharul-Anwar cewa: Wani mutum ya zo wurin Imam (a.s) sai ya ce da shi “Ya sarkin muminai, ka bani labarin mene ne, Wajibi, da, Abin da yafi wajaba, Abin mamaki da abin da yafi ban mamaki, abu mai wuya, ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...