Gaskiya tana nufin hanya matsakaiciya, wato ana nufin maganar daidai da bin hakika, gaskiya ita ce sanya komai da hikima bisa mahallinsa da ya dace da shi. Sannan bin gaskiya da tafiya kanta bisa tafarkinta a fagen tunani yana nufin tanadin makamin ilmi da mantik ...
A mahangar Shi'a, jagorancin malami a lokacin boyuwar Imam Mahadi (a.s), shi ci gaba ne na jagorancin imamai ma'asumai (a.s), kamar yadda su ma jagorancinsu ci gaba ne na jagorancin manzon Allah (s.a.w). ...
Zamu iya kasa mutanen da suka riki musulunci zuwa jama'a gida biyu ne: 1- Jama'ar da ake kira jahili mai takaitawa ko kafiri mai takaitawa, ana nufin su ne wadanda kalmar gaskiya da sakon gasiya na sama na adinin musulunci ya je musu, suka san ...
Dangantaka tsakanin malaman Shi’a da mahukuntan daular Safawiya da ma mahukunta na wasu dauloli da nufin raunana Shari’a ba ne. Dalilan yin hakan su ne samar da mamora da kyakkyawan manufa ga al’umma da yin wannan alakar kan haifar don taimakon jama’a da yada Mazhabar Shi’a da ...
Yayin da masu biyayya ga addinin Isa (a.s) suka haramata wa kawukansu wannan ni'ima ta samuwarsa a cikinsu, har ya samu hawa zuwa sama, sai manzanninsa da 'yan sakonsa suka ci gaba d aisar da sakonsa, kuma suka fuskanci wahalhalu masu yawa a kan hakan.
Bayani kan menene (hulul) shiga jiki da ittihadi (hadewa) hulul a harshen larabci ya samo asali daga kalmar halla da ma’anar sauka[1] amma Kalmar ittihad ita kuma tana da ma’anar abubuwa biyu su hade su zama abu guda daya[2] Kashe kashen ...
Mutumtakar Mutum A Tare Da Samuwar Sa Take, Ta Yanda A Dukkan Yanayi Ba Zai Yiwu A iya Raba Ta da Shi Ba, Sabanin Shi Musuluncinsa shi Ba a Danfare Da Samuwarsa yake Ba, Sai Dai Zuwa yake Yi, Wato zamu iya Suranta Samuwar Mutum Wanda Ba ...
Game da Tayar da Wanda ya Mutu a cikin Wata Duniya ta Daban ba wannan Duniyarmu ta Kasa ba, ya Wajaba da Farko mu san cewa ita Kasar da za a Tada Mutane a Cikinta ta Bambanta, Bambanci mai Girman Gaske kuwa daga irin abun da muke ...
Dalilin gaskata Annabawa a kowa ne zamani shi ne abin da karantarwarsu ta kunsa wadda don ita suke bayyana mu’ujizozi da kan gagari a kwaikwaya. Su wadannan mu’ujizozi suna daga cikin hujjoji bayyanannu da ke kiran mutane zuwa ga imani. Bayan haka akwai bambance-bambance na zahiri tsakanin ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...