advanced Search
Dubawa
46008
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Ta yaya Mutum zai iya samun ikon fassara Mafarki?
SWALI
Ta yaya Mutum zai iya samun ikon fassara Mafarki? Shin ko akwai Hadisi a kan haka?
Amsa a Dunkule

Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa.

Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya[1], kuma Allah ya hore masa fassara mafarki[2]. Kamar yadda ya fassara mafarkin abokan zamansa na kurkuku, da mafarkin Sarkin Misra, a wajen kurkuku ke nan dai fassarar mafarki, ko tawilin mafarki[3], a bisa irin kalmomin sunaye na Alkar’ani, shi al’amarine tabbatacce, na hakika, kuma wannan din wani ilimi ne wanda Allah ya sanar da wannan annabin, Annabi Daniyal yana daga cikin wadanda Allah ya ba su ilimin fassara mafarki[4]. Kuma hakika Kur’ani ya ambaci wasu shaidu na wasu Annabawan da Allah ya karfafa da gaskanta ingancin mafarkansu[5].

Game da rarraba ruwayoyi na nau’in mafarki, za mu ga kaso biyu na abubuwa da ake gani a cikin barci.

Wasu abubuwn da ake gani a cikin barci mafarkine na gaskiya, wasunsu kuma na karya ne[6]. ruwayoyi sun ambaci cewa; “Hakika mafarki na gaskiya wani yanki ne daga cikin yankin Saba’in na Annabaci”[7] shi irin wannan ilimin ba ana samunsa ne ta hanyar koyarwa da koyo ba, sai dai yana bukatar tazkiya da tsarkake rai, a saboda haka ne babu masu samun irin wannan baiwar sai yan mutane kadan kawai.

A cikin wasu littattafai na fassarara mafarki an ambaci wasu asasi da ka’idoji, sai dai ya wajaba mu lura da cewa wadannan asasin da ka’idojin, ba su ne komi da komi ba, kuma ba na gama gari ba ne, domin suna canzawa, a saboda bambaci su masu yin mafarkin, da wasu sharudda na daban. A saboda haka ba zai yiwu mu isa ga tabbatacciyar natija ba daga abubuwan da suka zo a cikin wadannan littattafaiba.

 


[1] Suratu yusuf, aya ta 4

[2] Suratu yusuf, aya ta 101

[3] Suratu yusuf, aya ta 101

[4] Littafin biharul anwar, wallafar allama majlisiy, juzu’I na 16, shafi na 371

[5] Suratus saffat, aya ta 105, da suratul fathi, aya ta 27.

[6] Littafin alkafiy, na kulayniy, juzu’I na 8, shafi na 91. bugun kamfanin, darul kutub al islamiyya.

[7] Littafin man la yahdhuruhul fakih, juzu’I na 2, shafi na 586

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • Meye matsayin jagorancin malami a tsarin siyasar musulunci?
    8086 کلیات 2012/07/24
    A zamanin boyuwar Imam Mahadi (a.s) "jagorancin malami" wani asasi ne tabbatacce kuma doka gama gari ta duniya wacce take daga tsarin siyasar musulunci, kuma matsayin malami dole ne ya kasance a matsayin jagora a matsayin shugaba mai yanke hukunci da bayar da umarni kuma ya kasance ...
  • Wadananne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani na wannan zamanin?
    6496 Ilimin Kur'ani 2019/06/16
    Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin tafsiran da suka gabata: ta bangaren amsa shibuhohi da warware tambayoyi da lamurran da suke kai- kaiwa a kasuwar tunani da kwakwalen mutane, bisa dogaro da tafarkin yin amfani da ...
  • mene ne ma’anar Takawa?
    17318 تقوی 2012/07/25
    Takawa wani karfi ne cikin ruhin mutum mai tsawatarwa da hana shi aikata ayyukan kuskure, kamalar takawa na kasancewa in an hada da nesantar abubuwan haramun, kamar nesantar shubha. Kuma ita Takawa tana da marhaloli da rabe-rabe, da kuma alamomi, zamu bijiro da su a jawabi na ...
  • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
    16001 معاد و قیامت 2012/11/21
    Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
  • Shin hadisin da ke cewa “duk wanda ya mutu ba shi da bai’ar imamin zamaninsa (Imaminsa) ya yi mutuwar jahiliyya” daga manzo (s.a.w) yake kuwa?
    9625 گوناگون 2012/07/26
    Bai’a na da bangarori biyu, mai bai’a (sauran mutane) da wanda ake yi wa bai’ar (wato su ne manzo (s.a.w) da imamai (a.s)). Tare da cewar manzo (s.a.w) shi ne hujja kuma shugaba, don haka shi za a yiw mubayi’a a matakin farko wato shi ne farkon ...
  • Shin mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru kan hanyarsa ta tafiya ko dawowa wacce ba ta kai kwana goma ba?
    9278 2019/06/16
    Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
  • mene ne gwargwadon tasirin Allah madaukaki a rayuwar mutum?
    16378 Irfanin Nazari 2012/07/25
    Ba yadda za a wani aiki ya fita daga iradar Allah mai hikima, wannan iradar ta Allah tana nan a ko da yaushe a rayuwar mutum a kowane lokaci da zamani, da dukkan dokokin rayuwa ba tare da ta cire wa mutum zabin da yake da shi ...
  • A zaben jagora malami ba kai tsaye ba akwai matsalar kai-kawo, to yaya za a warware wannan?
    7661 انتصاب یا انتخاب 2012/07/24
    A yanzu haka a jamhuriyyar musulunci ta Iran ana ayyana ‘yan takarar majalisar Khubrigan ta hannun shura Nigahban ne. To akwai batun sukan cewa Jagora shi ne yake ayyana ‘yan shura Nigahban, su kuma suke ayyanar cancantar shiga takara ga ‘yan majalisar khubrigan, su ‘yan majalisar khubrigan ...
  • yaya halittar mutum take a a mahangar musulunci?
    10480 Sabon Kalam 2012/07/23
    Ta mahangar Kur’ani mutum halitta ce da yake fizguwa zuwa ga ubangjinsa bisa fidirar halittarsa, kuma yake da jawuwa zuwa ga jiki, wannan halittar tana jansa zuwa ga ilimi da sani da alherai, a daya bangaren jiki tana kiransa zuwa ga sha’awa da sharri. Rayuwar mutum wani ...
  • Shin zan iya samun dama game da yin wani aikin na biyu bayan wanda nake yi
    7035 دنیا و زینتهای آن 2012/07/25
    Shari’a ba ta hana mutum yai koyi ko ya kware kan wata sana‘ar ba bayan wacce yake yi ko ya iya ko yin aiki sama da yadda ya saba abin kawai da shari’a ta hana kuma take kara tsoratarwa a kansa shi ne son duniya da nace ...

Mafi Dubawa