Da zamu koma ga Kur’ani mu tambaye shi kamar haka: - Me ya sa aka halicci aljannu da mutane? Kur’ani zai ba mu amsa cewa: Ban halicci aljannu da mutane ba face sai don su bauta mini”1 Sai mu sake yin tambaya mene ne ma’anar ...
Tabbas Allah mai tsarki da daukaka mai hikima ne ta kowace fuska, sannan dukkanin ayyukansa ya yi su ne bisa asasi na hikima ta karshe, to doron wannan asasi dukkanin samammu Allah ya halicce su ne a bisa doron hikima ta karshe, kamar yadda ya suranta su ...
Allah baya amfana da ibadar wani daga cikin bayinsa da komai, ba tare da banbancin cewa bawan ya yi ta ne bisa son ransa ko kuwa.Sai dai yin ibada bisa zabi na da amfani wajen kara samun kamala da daukaka da shiryuwa a sannu ...
Tabbas abin da aka gano a cikin wannan ayar ta 13 cikin Suratul Sujada mai albarka cewa Allah bai so mutane gaba dayansu su sami shiriya ba, wannan maganar ba haka ba ce, hakika abin sabanin haka ne domin Allah ya so kowa ya shiryu domin samun ...
Akan ayar da aka yi tambaya a kan ta, akwai bayanai da mahanga da ra'ayoyi da dama da aikiyi bayani a kai sai mu za mu yi nuni ne da wasu kawai. 1. abun nufi da mabiya Isa, su ne mutanen manzon Allah akwai mahanga ...
Domin mu yi bayyanin madu’in, zamu yi zance kan mas’alar ta bangare uku: Shin abin da aka ruwaito dangane da gajertar Imam Ali (a.s) haka ne ko ba haka ba? Idan har ya ingata shin gajerta aibi ne ga mutum? Shin mene ne ...
Kallon namiji ga jikin mace wacce ba muharrama ba haramun ne, ko da nufin ya ji dadi ko bai nufin hakan ba. Amma kallo fuska da hannaye idan ya kasance da nufin jin dadi to haramun ne, sai dai idan ya kasance ba da nufin jin dadi ...
Fir'auna sau biyu ya bada umarnin kashe kananan yaran banu isra'ila 1 na farko shi ne lokacin da aka haii Annabi Musa (a.s) ya bada umarnin kashe yara maza don ya takawa rayuwar Annabi Musa (a.s) birki. 2 na biyu kuma ya kasance bayan Annabi Musa (a.s) ...
Wannan ba wani abin mamaki ba ne, domin ba wata hujja ta al’ada da ta hankali da ta hana ‘ya’yan kani su girmi ‘ya’yan wa, mussam idan ya zamana tazara tsakanin yan’uwa biyun ba mai yawa ba ce kamar yadda ya kasnce tsakanin Hasan da Husain (a.s). ...
Dangane da fassara ko tafsirin jimlar {wadribuhunna} ta cikin aya ta 34 suratul nisa, karkatowa ko farkarwa. Dole ne mu ambaci cewa wannan fassarar ko tafsirin bayada tushe da sanadi na fassara, sai ma dai dalilai na lafazi da suke sabani da hakan. 1} Kalmar ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...