Ya zo a cikin muhimman litattafan fiqihu {hukunci} cewa mustahabbi ne a cikin tashahud na biyu karanta wannan zikiri kamar haka: {Bissimillahi wa billahi walhamdulillahi wa khairul asma' lilLah, ashhadu an la'ilaha illallah wahdahu la sharikalah, wa ash'hadu anna muhammadan abduhu wa rasuluh, arsalahu bil-haq bashiran wa ...
Wa’azi yana nufin isar da sakon Allah (s.w.t) zuwa ga jama’a. Kasantuwar sakonin Annabawa a dunkule abu guda ne, sannan sakon Fiyayyan Annabi (s.a.w) na masamman ne, da ya zo da nufin shiryar da bil Adama don fitar da shi daga duffai zuwa ga haske. A bisa haka ...
Wannan lamarin ba zai yiwu ba ga hukumar duniya ta Imam Mahadi (a.s) saboda dalilin faduwar wadancan hukumomin yana komawa zuwa ga zaluncin wadannan hukumomin ko kaucewarsu ga asasin adalci, ko kuma saboda yaudarar mutane ta hanyoyin isar da sako wacce ta haifar da bambanci tsakanin mutane ...
Dalilan shugabancin malami (wilayatul fakih) suna bayyana cewar, fakihi shi ne wanda yake jagorantar al’umma ta musulmi, kuma yake maye gurbin imamai ma’asumai (amincin Allah ya tabbata a gare shi) a zamin da imami yafaku (boye). Ta wannan matashiyar wilayatul fakih (Shugabancin malami) tana da abubuwan da ...
Majalissar kwararru ta zaben shugaba ta hada fakihai {wato masana a cikin fikhu} a cikin dokokin tsarin mulkin na jamhuriyyar musulunci ta iran a bisa doka ta 107, ya tanadi zabe wanda a keyi duk bayan shaikara takwas {8}domin zabar shugaba da kuma lura da yanda yake ...
Hujr bin Adi Al-kindi; ya na cikin sahabban manzon rahama {s.a.w} sannan bayan wafati ya kasance cikin kebantattun sahabban imam Ali (as) mai cika alkawali, hakika hujr bin adi ya halarci yakokin da imam Ali {as} ya jagoranta bayan wafatin manzon rahama ya kuma taimakawa imam da ...
Sama da shekaru dubu ne malaman shi’a suke yin bincike kan mas’alar jagorancin malami, wasu kamar abussalah halbi, da ibn idris hilli, sun yi bayani dalla-dalla game da sharuddan malami mai maye gurbin imami ma’asumi a wannan zamani, wasu ma sun yi bayani kan ayyukan da suka ...
Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...