"Ashsharab" abin nufi duk abin sha "Addahiru" abin nufi mai tsaki mai tsarkakewa wannan kalma an yi amfani da ita a cikin ayoyi daban-daban a gidan aljanna ana samun abin sha mai tsarki mai dadi iri-iri mai yanayi kala-kala, hakika Kur'ani mai girma ya kawo maganar sa ...
Ma’aunai da magwajai da kulainy ya kawo basuyi daidai da hadisin ba sai dai ta kebantane da hadisan da ya samo har ma da aka tauye kawai, bawai yana nufin wannan awon ya hau kan kowane hadisi ba domin sanin hadisi ingantacce ta hanyar bangarori uku da ...
Matanin da ahlussunna suka cirato daga sahihul Muslim da Turmuzi da musnadi Ahmad wanda ke cikin wannan littafan ya zo ne kamar haka “littafin Allah da ‘yan gida na” kuma wannan shi ne matanin da ya shahara a wajen ahlussuna. Amma akwai wani matanin da ba wannan ...
samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa. Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ...
A wajen malaman lugga: T R J M, wadannan nan ne bakaken da suka hada Kalmar tarjama, wato jam’in (tarjiman) shi ne wanda yake yin tarjama, yake fassara magana, ana cewa wane ya tarjama maganar wani: ma’ana ya bayyana shi ya fayyace shi, haka ma, wane ya ...
Sharuddan asasi na jagoran musulunci sun hada da: ilimi, adalci, ikon tafiyar da al'ummar musulmi. Kuma a asalin doka ta dari da tara ta kundin tsarin dokar jamhuriyyar musulunci an yi nuni da wadannan sharuddan kamar haka: Sharudda da siffofin jagora: 1- siffantuwa ...
dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
Tarin ayoyi na Kur’ani da Attaura da kuma bayanan tarihi a kan yajuj na nuni da cewa wannan a’umar ta rayu ne a yankin arewacin asiya sai dai sun ta kai ma yankin kudu da yamma hare hare masu tsanani. Amma lokacin da Zulkarnaini ya yi bango ...
Wannan ba wani abin mamaki ba ne, domin ba wata hujja ta al’ada da ta hankali da ta hana ‘ya’yan kani su girmi ‘ya’yan wa, mussam idan ya zamana tazara tsakanin yan’uwa biyun ba mai yawa ba ce kamar yadda ya kasnce tsakanin Hasan da Husain (a.s). ...
Kur'ani ya zo da salon bayani kala-kala dangane da halittar Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda za a iya fahimtar cewa halitta Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi ta kasance bisa wasu matakai mabanbanta daya bayan daya, kamar yadda zai zo:
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...