Da farko dai: Hakika wadannan gungun ruwayoyin, ko dai sun zo ne a saboda (Takiyya), ko kuma don wani lokaci ne na musamman, wanda babu wani amfani, ko tasiri, na yin juyin juya hali ta yin amfani da makami, dadin dadawa kuma, akwai kuma wasu ...
Yin ridda ita ce bayyana fita daga addini, mafi yawanci tana kasancewa ne tare da bada gudum mawar wasu. Horon mai ridda baya game wanda ya fita daga addini amam ya boye hakan bai bayyana shi ba don kar mutane su sani. A bisa wannan tushen horon ...
Bahasi kan alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s) yana daga bahasosi masu zurfi da wuya ta wata fuska wacce tana bukatar karanta dukkan ruwayoyin da suka zo game da haka, sai dai abin da aka fahimta daga ruwayoyi –ko da kuwa a dunkule ne- shi ne kasa wadannan ...
An samu ruwaya game da kallon mace wacce ba musulma ba ga mace musulma daga imam Sadik (a.s) yana cewa: Bai kamata ba ga mace musulma ta yaye lullubinta a gaban mace bayahudiya ko kirista, domin su suna ba wa mazajensa bayanin siffofin jikinta
Lalle shi shedan daidai gwargwardon yanda ya zo a cikin Kur’ani yana da zarafin da zai iya salladuwa a kan dukkanin ‘yan Adam face bayin Allah nan da aka tsarkake. Su wadanda aka tsarkake, su ne wadannan da suka kai ga manyan–manyan mukamomi ta yanda shedan ba ...
Wannan hadisin babu shi a cikin littattafan Shi'a, sai dai cewa wsu daga malamai sun yi nuni da shi. Wannan hadisin an same shi a littattafan ahlussunna ne kawai a littafin sunan Abu Dawud (wanda yake daga manyan littattafan hadisin Sunna) kuma bisa zahiri wasu sun nakalto ...
Majalissar kwararru ta zaben shugaba ta hada fakihai {wato masana a cikin fikhu} a cikin dokokin tsarin mulkin na jamhuriyyar musulunci ta iran a bisa doka ta 107, ya tanadi zabe wanda a keyi duk bayan shaikara takwas {8}domin zabar shugaba da kuma lura da yanda yake ...
An rawaito cewa lokacin Allah madaukaki ya hura wa Annabi Adam daga ransa sai ya ta shi mutum madaidaici sai ya zauna ya yi atishwawa, sai aka yi masa ilhama da ya ce:≪alhamdu lillahi rabbil aalamin≫ “godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai” sai kuwa ya fadi ...
Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
Hujr bin Adi Al-kindi; ya na cikin sahabban manzon rahama {s.a.w} sannan bayan wafati ya kasance cikin kebantattun sahabban imam Ali (as) mai cika alkawali, hakika hujr bin adi ya halarci yakokin da imam Ali {as} ya jagoranta bayan wafatin manzon rahama ya kuma taimakawa imam da ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin ...