Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
Gaskiya tana nufin hanya matsakaiciya, wato ana nufin maganar daidai da bin hakika, gaskiya ita ce sanya komai da hikima bisa mahallinsa da ya dace da shi. Sannan bin gaskiya da tafiya kanta bisa tafarkinta a fagen tunani yana nufin tanadin makamin ilmi da mantik ...
Hankali shi ne hujjar Allah ta addini wacce ya ba wa mutum, hankali ke yi wa mutum jagora har ya kai shi ga samun cikakkiyar kamala, Shari`a hujja ce ta fili wacce take hana mutum gurbata da cutaya kuma ta kai shi ga samun cika da rabauta. ...
Sallar firgici, ko sallar Daren Binnewa, salla ce da ake yin ta ga mamaci a farkon lokacin da aka binne shi, don haka ne ma ake kiran ta da salar firgici, domin yayin da mutum yake barin wannan duniayr bai saba da waccan duniyar sabuwa ba, kuma ...
Allama Majlisi (RA) ya ruwaito a cikin littafinsa Biharul-Anwar cewa: Wani mutum ya zo wurin Imam (a.s) sai ya ce da shi “Ya sarkin muminai, ka bani labarin mene ne, Wajibi, da, Abin da yafi wajaba, Abin mamaki da abin da yafi ban mamaki, abu mai wuya, ...
Wannan magana ta zo cikin hadisin Manzo (s.a.w), abin nufi da ranaku a nan su ne ranakun sati, amma a mafiya yawan lokuta wannan ruwayar na nufin muhimmancin zamani da wajabcin rashin shakku zuwa ranaku ko rashin kudure su da zai sa a manta su ko muzantan ...
Ma’aunin shiga aljannan shi ne imani da aiki na gari.Dan shi’a ma zai shiga cikin aljanna bisa sharadi, kasantuwar sa dan shi’a kadai ba zai zama dalilin shigar sa allajannan ba, ya zama lallai ya yi aiki da abin da zai tabbatar da cewa ...
samuwar karkata daga nau”in bidi”a da ridda tsakankanin sashen sahabban manzon Allah {s.a.w} bayan wafatinsa. Na farko: daga mahangar littafai na tushe na al”ummar musulmi faruwar hakan wani abu ne da aka sallamawa da babu kokwanto ko shakka ciki sannan kuma sam bai kebantu da littafan shi”a ...
An samu ruwaya game da kallon mace wacce ba musulma ba ga mace musulma daga imam Sadik (a.s) yana cewa: Bai kamata ba ga mace musulma ta yaye lullubinta a gaban mace bayahudiya ko kirista, domin su suna ba wa mazajensa bayanin siffofin jikinta
Ruwayoyi masu yawa sun nuna fifikon matsayin ilimin Imamai (a.s) a kan Annabawa, dalili kan wannan maganar shi ne kadaitakar haske da kadaitakar badinin Imamai (a.s) tare da Manzon Allah (s.a.w), saboda shi Manzon Allah (s.a.w) ya fi baki dayan Annabawa, sannan kuma ilimin Imamai an samo ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...