An ambaci fuskokin gajiyarwar (kalu balen) da Kur’ani mai girma ya yi wadda zai yiwu na ambaci uku daga ciki: Ya gajiyar ta bangaren yare da bayani Ya gajiyar da fuskacin abin da ya kunsa Sannan kuma ya gajiyar ta ...
Adinin musulunci shi ne cikamakin addinan sama na Allah, bai kebanta ga wasu mutane kawai banda wasu ba, ko ga wani lokaci banda wani ba, sai dai shi musulunci ya zo ne ga dukkan mutane gaba daya, Kuma haka Allah (subhanahu wa ta’ala) ya so ya sanya ...
Cigaba da wayewar al’umma yana daga cikin isdilahohin da suka yadu a cikin tunanin yammacin duniya da malam palsafar siyasar yammacin duniya da aka yi masa fassarori mabambanta daga cikin bayanai da aka yi wa wannan isdilahin, da muna iya gane cewa mahangar da ake da ita ...
Wannan ba wani abin mamaki ba ne, domin ba wata hujja ta al’ada da ta hankali da ta hana ‘ya’yan kani su girmi ‘ya’yan wa, mussam idan ya zamana tazara tsakanin yan’uwa biyun ba mai yawa ba ce kamar yadda ya kasnce tsakanin Hasan da Husain (a.s). ...
Wannan magana ta zo cikin hadisin Manzo (s.a.w), abin nufi da ranaku a nan su ne ranakun sati, amma a mafiya yawan lokuta wannan ruwayar na nufin muhimmancin zamani da wajabcin rashin shakku zuwa ranaku ko rashin kudure su da zai sa a manta su ko muzantan ...
Bisa la’akari da sadanin ra’ayi da bambancin makarantu masu tsara wa mutum hanya mai fuska daya -wato karkata ga bangaren jin dadin duniya zalla da watsi da makomar mutum, Ko kuma watsi da ni’imomin Allah da dukafa ga tarbiyar ruhi shi kadai- shi ya sa addinin musulunci ya ...
Kamar yadda ka sani shi batun raja’a lamari ne yake daga akidojin shi’a imamiya, kuma ita raja’a ma’anarta ita ce: dawowa duniya bayan mutuwa gabanin tashin kiyama, sannan raja’a ba ta shafi kowa da kowa ba, ta kebanci muminai tsantsa da mushrikai tsantsa. Akwai ...
Amir ya bayyana tare da bayani wannan cikin huduba ta uku a nahj da aka sani da shakshakiyya, kamar yadda ya zo daga cikinta “amma wAllah (SW)i ya sanyata … inda a karshe yake cewa … faufaufau (haihata haihata) wancen tsanani ya faru kuma ya kare” ...
Baba shakka kan cewa hakika sahabbai Allah Ta’ala ya kara yarda a gare su ya yarje musu sun bawa lamarin Kurani mai girma minimmanci sosai a lokacin rayuwar Manzo (s.a.w) da ma bayan wafatinsa (s.a.w) kuma sun dauki tutar addini da kyakkyawar koyarwa sama zuwa jama’a. kuma ...
Ya kamata mu san cewa wannan aiki na wasa da azzakari haramun ne a mahangar muslunci sannan dukkanin mai aikata wannan aiki ya na cikin masu aikata manyan zunubai.[1] [2] Istimna”I {wasa da azzakari} kala-kala ne kamar misalin wasa da azzakari ...
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin ...
kafin mu Amsa wannan tambayar yana da kyau a san cewa, su ruwayoyi gaba dayansu, za a iya kasa su kashi biyu, kashi na farko, anace musu ingantattu masu karfi… Akwai kuma wani kashin na ruwayoyi, wadanda ake ce musu raunana, wadanda ba za a iya jingina ...
Duk da yake Annabin Musulunci wanda shi ya fi girma, shi ne mafificin Annabawa, kuma mafi daukakar daraja, to amma wannan Hususiyar tasa (wato girman da ya kebantu da ita) bai zamo wajibi ya zamo dole sai ya tattaro dukkan kebance-kebancen dukkan Annabawa da Manzanni ba, a ...
Abdulqadir Jilani da ake yi wa laqabi da gausul a’azam shi masani ne sufi da aka haife shi a arewacin iran a qarni na biyar, wanda ya mutu a bagdad a qarni na shida. Amma alaqarsa da imam Sadiq (a.s) da savawarsa gare shi to ...
Mafarki wani al’amari ne dake faruwa ga dukkan mutane (a cikin barcinsu) a tsawon rayuwarsu. Sai dai har yanzu malamai ba su iya samun cikakkiyar saninsa ba da yadda yake faruwa. Al’kar’ani mai girma ya bamu labarin Annabi Yusuf (a.s) game da mafarkinsa na gaskiya
Sabo kamar wani jiki ne mai wari da duk sa'dda aka nutse cikin yin sa to sai mutum ya rika jin warinsa ya ragu sakamakon ya zama jikinsa, domin zai daina jin warinsa daga karshe ya dulmuye cikinsa sosai. Kuma idan mutum ya yi azamar komawa daga ...
Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
Kur'ani mai girma ya tabbatar da samuwar aljani kuma ga wasu daga cikin bayanai kan aljani. 1- Aljani halittace da aka yi shi da wuta saBanin mutum shi da kasa aka halicce shi.[1] 2- Yana da ilimi da idraki da tantance Karya daga gaskiya, ...
Duk da cewa zancen annabi Sulaiman (a.s) ya na hikaya ne na daukakar matsayi da kuma yakini da Sulaiman ya ke da shi zuwa ga rahamar Allah marar karshe wanda ba za ka hada da sauran mutane ba, amma ba zaka hada da halin da imam Husain ...