Please Wait
74183
Daga tarin ayoyi da ruwayoyi da kuma tafsire zamu iya anfana da cewa a cikin lamarin kisan kai da annabi halliru ya aikata wato kashe yaro matashi, ba ya aikata hakan bane domin son rai da fushi ba, sai dai dan yana da tabbacin cewa a cikin kisan a kwai hikima da masalaha, musamman ma wanda ya aikata kisan yana daya daga cikin bayin Allah muminai wanda zuciyar sa ke cike da rahama da tausayi.
Kaman yadda shin kansa annabi halliru (a.s) ya ba annabi musa (a.s) amsa yayin da yake tsogumi akan aikin da annabi halliru ya aikata sai ya amsa masa da cewa: iko da hikimar ubangiji suna sama da kowa ne abu kuma hankali dan adam ba zai iya gano hakikanin iko da kuma hikimar Allah madaukaki ba. Ta haka ne zamu gane cewa hankula ba su da iko ko kuma ba su ikon hukunci akan al'amarin ubangiji madaukaki, sai dai iko da izinin sa sune saman hankula. Saboda haka kadaka yi hukunci da zahiri da kuma hankalin ka, don haka duk abunda ka ga na aikata ka amshe shi da hannuwa biyu.
Ta wata fuskar tabbas kisan da annabi halliru ya aikata wato kasha yaro matashi, wani ummar nine na musamman daga Allah madaukakin sarki don haka annabi halliru ya aikata ummar nine na Allah madaukaki, ba wai ya aikata ganin damar sa bane.
Wani lokaci Allah madaukakin sarki yana aikata abunda yaga ya fi dacewa koda kuwa afili ya saba da hankalin mutane.
Akan haka akwai tari ayoyi da ruwayoyi da suka yi bayanin wannan masalahar kamar haka:
1} saboda iyayan yaro sun haifu shi a cikin musulunci domin iyayan shi musulmi ne, saboda haka in ya kafice anan gaba ya zamo murtaddi ke nan kuma hukunci sa kisa ne {saboda haka annabi halliru ya kasha shi} domin ya samu sauki azaba ranar kiyama.
2} Allah madaukakin sarki yasan cewa cigaban rayuwar yaron awannan duniyar hasara ce gare shit a fuskar duniya da lahira. Inda yaci gaba da rayuwa zai kafirtadda iyayan sa kuma sakamakon haka duk zunubinsu zai hau kan sa ne.
3} rayuwar yaron zai hana iyayan sa samun alheri wato haihuwar ya mace wadda ta hanyarta ne annabin Allah ya fito. Amma da kasha yaron iyayan sa sun saura a matsayin su na masu imani kuma Allah ya ba su diya mace mai imani da tausa har suka samu dacewa da su zama kakani na saba'in na annabi mai tsira da aminci.
Daga karshe: hikimar rashin barin wannan yaron ya rayu, shi ne masalahar samar da annabin Allah da sauran annabawa masu tsarki.
Afili yake cewa sunnar Allah ta ginune akan iyayan annabi su zamo masu imani. Saboda haka da yaron ya rayu ya zamo ta hanyar sa ne iyayan sa suka kafirce, to da ya zamo sanadin toshe hanyar ken an.
Idan a ka lura da bayane da ke cikin tafsire da ruwayoyin da suka zo, dake magana a kan kisan kai {kashe yaro sabon balaga[1]} wanda annabi halliru ya aikata za aga cewa kisan baya faru bane sakamakon fushi ko gardama ba, sai dai annabi halliru ya aikata kisan ne batare da tattaunawa ko jayaiya atsakani shi da yaron matashi[2] ba. Saboda haka afili yake a yi kisan ne ba domin fushi da daukar fansa ba, don haka mai tambaya zai fahimci cewa duk da babu wani dalili a fili ko kuma abunda ya tunzura shi, tabbas akwai hikima da dalili na musamman don haka annabi halliru ba yabi son rai shi ba ne. musamman ayayin da aikin ya auku ne ta hannun mutumin da a cikin kur'ani aka kira shi da. Bawa daga cikin bayin mu wanda muka cika zuciyar shi da rahamar mu, sannan mun sanar da shi ilimi daga cikin ilimomi na musamman[3]. In akan lura da wannan ayar za aga cewa babu yanda son rai zai sa wannan bawan Allah ya aikata abunda ya sabama shari'a. sai dai miye hikimar tausai a nan? Ta yaya zamu iya yadda cewa mutun kamar annabi halliru zai kashe yaro matashi wanda bai jima da balaga ba? Wannan yana bugatar amsa wadda zata zo nan gaba.
Ya zo daga wani bangare na ruwayoyi cewa annabi musa (a.s) a yayin da yaga wannan abunda da ya faru {wato kisan kai} ya kasance a cikin mamaki saboda yana kallon abun ta fuskar zahiri kuma yana ganin wani abune wanda bai dace ba sai ya ce ma annabi halliru; miyasa zaka kashe mutumin da bai aikata sabo ballantana ya can canci hukunci? Wannan aikin baa bun yarda ba ne kuma aiki ne marar kyau. Acikin wannan yanayin ne sai annabi halliru ya fara bada amsa a takaice kamar haka; iko da hikimar Allah tan a sama da dukkan hankalin dan adam kuma ba zai iya gane ummarni da bugatuwa da ubangiji ba. Don haka hankula ba za su iya gane hikimomi na ubangiji ba, ummarni da iko na ubangiji suna sama da hankulla. Don haka kadaka yi hukunci da zahiri ko kuma hankalin ka. Don haka duk aikin da ka ga na aikata to ka amshe shi da hannuwa biyu[4].
Idan mu kayi dikka a cikin hadisin zamu fida sakamako kamar haka:
1} lamurra suna ginuwa ne akan abu biyu abunda yake fili da wanda yake kan hakikanin abu, in aka dubi abu ta mahangar abunda yake afili sai a abubuwa masu kyau da rashin sabo su bayyana in ta bangarin hakika kuma sai mumunan abu da sabo su bayyana saboda haka bai zai yiwu ba a kowa ne lokaci a yi hukunci da abunda yake a fili ba.
2} wani lokaci Allah madaukakin sarki saboda wasu masalahohi wadanda suke boye sai ya yi hukunci da abunda yake a bayyane ya kyale wanda yake aboye kamar azabtarwa da bada sakamako.
3} tabbas kashe yaro matashi wani ummarni ne na Allah madaukaki, saboda haka annabi halliru ya kasance mai zartar da hukuncin Allah ne da kuma Allah bai ummarce shi ba da bai kasance mai aikata wannan aikin ba {wato kisan kai}. Ya kasance mai aikata ummarni Allah madaukaki[5].
Tambaya; shin Allah madaukakin sarki da yabada ummarni da akashe yaron wannan zai iya zama hukunci kafin aikata laifi? Jawabin wannan tambayar zai zo kamar haka.
1} idan iyayen da suka haifi mutun sun kasance muminai sai shi mutumin bayan ya kai shaikarun balaga, sai ya bar addinin iyayen sa wato musulunci, to hukuncin sa shi ne hukunci murtaddi na fitira, don haka in namiji ne hukuncin sa kisa. Ya zo da yawa a cikin ruwayoyi cewa: koda yake a bayyane a cikin kur'ani, mahaifi da mahaifiyar yaron sun kasance muminai, amma dan su ya kasance kafiri ne ta yadda ba wata hanyar da ta saura mashi wajen haskaka zuciya da ganin hasken shiriya an buga masa tambarin taurin kai na rashin karbar gaskiya[6]. ta wata fuska duk da cewa aiyukan yaro a fili yayin da yake wasa da yara basa nuna kafircin sa {kamar yadda annabi musa a. s ya kafa dalili da wadannan halayai na fili masu kyau, wadanda suka nuna yaron tsarkakake marar zunubi}. Amma hakikanin abunda ke cikin zuciyar sa na akida da aiki, su suke tabbatar da kafircin sa {kamar yadda yake ga ilimin ubangiji kamar kuma yadda ilimin ya bayyana ga annabi halliru a. s}. Daga karshe, kashe yaron shi ne sakamakon san a abunda ya zabama kan sa a cikin wannan duniya, saboda haka abunda ya fi shi ne a takatar da rayuwar sa ta duniya.
2} Allah madaukakin sarki yana da masaniyar cewa cigaba da rayuwa da raron zai yi bad a wani amfani sai dai hasara ta duniya da lahira musamman kokarin da zai yi wajan batar da iyayen sa masu imani da kuma rusa zuriyar su wajan hanata {zuriya} kaiwa ga albarkacin duniya da na lahira kuma al'umma da zuriyar sa zasu zamo cikin rashin aminci, don haka masalaha shi ne ya rasa rayuwar sa, kamar yadda mutum yake kiyaye abunda zai anfane shi fiye abunda zai cutar da shi kuma ya zabawa kansa makomar sa. A wannan bangaren duk da cewa munsan mai daukar rai mala'ika azara'ilu ne da masu taimakama sa, sai dai Allah da nufin sa anan ya sa wani wakili {wanda zai dauki rayuwar yaro} daga cikin bayinsa wanda ke dauke da ilimi na musamman daga wuri Allah wato annabi halliru (a.s).
Ta wata fuskar, aikin da annabi halliru (a.s) ya aikata, ya ginu ne akan ikon takalifi da kuma na dabi'a na ubangiji {irada tashri'I da irada takwini} wanda suka tabbata akan yaro, don haka wannan kisan kamar sauran kisan da suke afkuwa yayin hadari da sauran su. {sai dai bambamci wannan kisan da hadari shi ne hadari bayana karkashin iko na takalifi ba wato irada tashri'I, amma wannan kisan da sauran rasa rayuka wanda suke afkuwa bata hanyar hadari ba wato mutuwar al'ada za'a iya ganin abun ta fuska biyu wato tashri'I wa takwini suna dauruwa ane akan iko da izini na ubangiji mai girma}.
Imam sadik (a.s) yana cewa: annabi halliru ya kasance cikin tunanin cewa kada wani shamaki ya shiga tsakanin shi da aikin da aka dora ma sa, har kuma ya rasa ladar aikata hukuncin Allah; wato kashe yaro matashi {wanda farawar sa da garshen sa suna karkashin masalaha da lutufi na ubangiji ba wai cancantar mutum ba}. Musamman zartar da hukuncin shi ne zai zamo sanadiyar zamun rahama na iyayen yaron {domin annabi halliru ya sani cewa kamar yadda ya zo a cikin kur'ani Allah zai ba iyayen yaro da wanda yake mai tsarki kuma wanda zai hada kan mutanen gida su} sai kuma ta wannan hanyar ce annabi halliru zai samu dama isar da sirrori da bayyana hakika da ilimi na Allah madaukaki zuwa ga annabi musa (a.s). Abun lura anan shi ne yayin da annabi halliru yake bayanin hikimomi sai yake cewa: ina jin tsoron kada yaron a cikin rayuwar shi ya sa iyayen sa su kafirta; wato a cikin aikin ba son rai da son zuciya sai dai cewa duk abunda na aikata tare da izinin ubangijine, a cikin wannan aikin ikon Allah da goyan bayan sa suna tare da ni sai dai bambamci anan shi ne Allah bai suffantu da siffar tsoro, amma halliru da makamanci sa sun siffantu da siffofin tsoro {hadaya a cikin aikata hukunci jin tsoro akan rashin da cewa a aikata ummarnin Allah} [7]
Domin Allah madaukakin sarki duk da yana da ilimin cewa anan gaba yaron zai kasance mai aikata sabo, bai bashi dama har ya aikata aikin ba domin shi da kan shi yaga mumunan aikin shi? Shin wannan ba tilastawa bane? {wato jabr}
Duk da cewa anyi bayani a baya abunda zai haskaka mana anan shi ne {a} asalin rayuwa na hannun Allah kuma shi ne mai ba da tag a mutum ba tare day a can canta ba.don haka mutum bai da ikon tilastawa wajen cigaba da rayuwa da kuma tambayar miyasa za a yanke masa rayuwa.
{B} Allah madaukakin sarki a bisa hikimar sa da masalahar say a yi nufin zai da rayuwar yaron, amma akwai wasu dalillai da zamu kawo kamar haka.
1} yaron ya kasance mai laifi ne ta fuska biyu. {a} murtaddi a fitira, {b} yana da ikon rusa ikidodin iyayain sa. Allah ya sanin idan ya bashi dama ba zai kyara munanan ayukan sa ba kuma bai daina kafirci ba, saboda haka ne ma aka zartar masa da hukuncin kisa[8].
2} idan da yaron ya rayu da zai aikata niyyar sa ta jawo wasu ya zuwa kafirci, saboda haka akwai cutarwa domin kuma domin kare wannan cutarwar da sauran abubuwan da zasu biyo baya marar sa kyau, sai akayi hukunci akan kawo karshen rayuwar wannan abun halitar.abunda zamu iya fahimta a zahirin ayar shi ne yaron ya kasance yana da alamomi na idan yakai ga balaga cikin sauri zai fada cikin mumunan aiki da sabo kuma ya kama hanyar halaka iyayan sa wato mahaifi da mahaifiya.
3} kamar yada yake a cikin aya ta 81 ta suratul kahafi: Allah ya kaddara zai yi sakamako gun iyayain yaron wanda ya kasance batace da yaro wanda zai zamo abun koyi. Abun fahimta anan shi ne ba rashin kashe yaro bayan halakar da iyayai sa da zai yi da kuma rashin zartar da hukuncin ridda akan shi zai zamo wanda zai toshe hanyar zuwan alkhairi ga iyayain. wannan ya zo a cikin ruwaya cewa; Allah ya yi nufin ba iyayain yaro ya mace wadda zata Haifa da na miji wanda ta hanyar sa ne salsalar su za ta yadu kuma su zamo sune tushe na annabawan Allah guda saba'in wanda duk asalin su ya fitone daga wannan yar mace[9].
Daga karshe hikimar rashin ba yaro damar cigaba da rayuwa shi ne, masalaha ta asalin tsatson manzon Allah mai tsira da aminci.
A bayyane yake cewa sunnar Allah ta ginune akan cewa iyayain annabawa dole ne su zamo masu imani {bayani annabin da iyayain sa suke kafirai}. Saboda haka da yaron yaci gaba da rayuwa har ya zamo sanadiyar kafirtar iyayansa to da ya toshe hanyar wanzuwa ta sunnar Allah. Don haka wannan tambayar bata da ma'ana cewa miyasa Allah bai bar yaron ba kuma miyasa bai sa tsatson manzon Allah ya bayyana ba?
Shin saboda imanin iyayai yaro ne yasa Allah yai masa sauki wato yabar duniya kafin ya aikata laifi don haka zai cancan ci azaba? Ko kuwa sabada Allah yana da ilimin cewa anan gaba zai kasance mai aikata sabo saboda haka za'a hukunta shi?
Da wadannan bayanan ne zamu fahimci cewa kisan akan shi yaron da wanda ya aikata kisan wato annabi halliru da kuma iyayan wanda aka kashe yana da amfani domin zai zamo rahama ne gare su baki daya.
A} amfani na farko da kisan zai yima yaron kamar haka:
1} isa ga hukuncin sa na ridda tun anan duniya kuma ta yiwu ya zamo sakamakon samun saukin sa a ranar lahira.
2} da yaci gaba da rayuwa har ya zamo sanadiyar kafircewar iyayain sa to da nauyi da zunubi na iyayain yah au kansa.
3} kafircin akida yana haifar da miyagun aiyuka da kuma ya na ga mutum ga sabo. Don haka rife littafinsa da akayi tun yana karami zai zamo rufe littafin sa kenan na miyagun aiki har abada, a ranar kiyama ba za a hukunta shi da aiyukan da bai aikata ba yayin da yana rayai[10].
4} baya iya biyan hakokin iyayain shi wato ya zamo mai cutarwane gare su, kuma cutar da iyayai yana kara zunubi kuma yana jayo la'anar iyayai akan yaro.
B} amfanin da iyayain zasu samu kamar haka:
1} kiyaye imanin su.
2} sakamakon tausayi na uba da kuma rahama ta uwa zata sa iyayan su gaza daurewa wajan kare ikidarsu yanda daga karshe zasu rabu da imanin su. amma in ba yaro hankalin su zai kwanta.
3} hakuri a cikin jarabawar Allah da yadda da gaddara shi yana sa mutum ya samu daukaka.
4} mai makon yaro marar ji mai mummunan aiki. Sai suka samu yarinya mai tsarki da tausayi wadda zata kawo masu albarka.
5} samun rabo na zama kakanin annabawa saba'in, da kuma amfanuwa da gafararsu.
C} amfanin da wanda yai kisan zai samu kamar haka:
1} samun damar aikata ummarnin Allah da ya yi.
2} sanadiyyar saukar albarka a gidan mumini da ya yi.
3} samun dama wajen bayyanawa annabi musa (a.s) wani sashe na sirrin wahayi da ilimin gaibi da wasu abubunwan da suke boye.
Imam sadik (a.s) ya bayyana wannan ni'imomi kamar haka; Allah yana da sanin cewa idan yaron ya cigaba da rayuwa zai zama sanadiyyar kafircewar iyayain sa kuma ya zamo fitina a cikin al'umma. Sai Allah ya daura nauyin kisan sa ta hannun annabi halliru wanda daga karshe wanda aka kashe da wanda yai kisan da iyayain wanda aka kashe za su zama cikin lutfi da karama ta ubangiji mai girma.
[1] Gulam ;shine wanda gashin fuska ya fara fito masa {mu'ujam mugayisllugah}
[2] Safi, jildi na 2,
[3] Kahfi, 65.
[4] Faiz kashani, safi, jildi na 3, shafi 253, ruwaya daga imam sadik{a. s} .
[5] Nurusakalain, jildi na 3, shafi na 283 zuwa 284
[6] Tafsirin majma'ul bayan ; nurusakalain, jildi na 3, shafi na 286; tafsirin ayashi; ; tafsirin safi, jildi na 3 shafi na 255.
[7] Illali alyashi; nurusakalain, jildi na 3 shafi na 284{hadisin imam sadik a.s}
[8] Duk da cewa abunda ya shafi ridda da kuma cewa annabi halliru ya zartar da hukunci akan abunda yake bayyane garesa{duk kuwa da cewa awancan zamani babu hukuncin shari'a} wannan mahangace ta wasu.
[9] Nurusakalain, jildi na 3, shafi na 286 da kuma 170 zuwa 173
[10] Illalishaye'I; tafsirin safi, jildi na 3, shafi na 256.