advanced Search
Dubawa
6865
Ranar Isar da Sako: 2012/03/15
Takaitacciyar Tambaya
Shin maganar cewa kowane mutum ana haifarsa da dacensa haka ne kuwa?
SWALI
Shin da ake cewa kowane mutum yayin haihuwarsa ana haifarsa da dacesa ya inganta kuwa? ina neman karin bayani a fadadamin maganar dace.
Amsa a Dunkule

Muna da ruwayoyi da dama da suka yi magana kan ana haifar mutum ne da dacensa, ya zo a ruwayoyi cewa Allah (SW) na fadawa iblis “ban halittarwa dan Adam zuriyarsa ba face sai da na halitta maka misalinta, babu wani daya daga dan Adam face yana tare da shaidanin da ke tare da shi”[1] a wata ruwayar kuma an rawaito daga Manzo (s.a.w) ya ce “babu daya daga cikinku face an wakilta masa makusanci daga aljanu” sai na kusa sukace: harda kai ya rasulllahi? Sai Manzo (s.a.w) ya ce: e harni, sai dai Allah (SW) ya rinjayar dani a kansa yasallama min (ya musulunta) baya umarnina da komai sai alheri.[2] abin da Manzo (s.a.w) ke nufi cikin wannan ruwaya shi ne mutum ya yi kokarin tsare kansa daga wannan abokin wajan kokwantonsa da razaninsa, yadda yake tare damu a rayuwarmu, kuma mu yi kokarin kare kanmu daga tasirinsa da dukkan abin da ya makirta mana duba da abin da Allah (SW) yake yi na turo annabawa da mursalai domin shiyar da dan Adam, alokaci guda shi kuma shaidan da yayansa ba zasu zauna hannu rabbana ba idan mun duba, zasu dinga iya matukar kokarinsu game da duk abin da zai yiwu wajan juyar da dan Adam zuwa bata. Karara wannan a fili yake shedan ya samu nasara kan wasu mutane, su ne wanda suka kau da kai daga ambaton Allah (SW) suka gafala daga gareshi.

Dangane da wannan ne Allah (SW) madaukaki yake fada cikin Kur’ani mai girma “kuma wanda ya makanta wajan hukuncin mai rahama, zamu lullbeshi da shaidani ya zamo abokinsa”[3]

 


[1] Majlisy Muhammad albakir, bihar, bolume 60, page 306, mu’assasatul wafa’a Beirut, Labanon 1404

[2] Majlisy Muhammad albakir, bihar, bolume 60, page 298, mu’assasatul wafa’a Beirut, Labanon 1404

[3] Suratuz zukhruf, aya ta 36.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

  • mene ne Hikimar Tashahud da Kuma Sallama?
    11544 بیشتر بدانیم 2013/08/15
    Asirin da ke boye a cikin tashahud shi ne daidaita abin da harshe ke furuci da shi da kuma abin da zuciya tai imani da shi wato daidaita furuci da kuma aiki alokaci daya, ta wata fuska kuma shi ne fita daga wannan tsarin na duniya da ...
  • mene ne bambanci tsakanin Dabi’u da Ilimin Dabi’a?
    15739 Halayen Nazari 2012/07/25
    dabi’u a luga jam’I ne na ‘’kulk’’ dabi’a/hali/al’ada. Gamammiyar ma’ana saboda kasancewarta al’ada ko hali mai kyau ko mummuna. Amma ‘’Akhlak’’ dabi’u a cikin istilahi ma’anarsa malaman akhlak sun ambaci ma’anoni masu yawa. Bai yiwuwa a gwama tsakaninsu yanda ya dace. Amma sai dai musulmi ...
  • Menene dalilin fifikon Imaman Shi\'a kan sauran annabwa baki Daya banda Manzo mafi girma Muhammad (s.a.w)?
    5530 انسان کامل 2017/05/20
    Ya zo a cikin koyarwar addininmu cewa ba za a samu wani daga cikin magabatan Annabawa da wasiyyai (a.s) da waliyyai (r.a) wanda zai fi Imam Ali (a.s) matsayi ba, sai dai matsayin Annabta, amma ta wani Bangaren fa Imam (a.s) ya gaji baki Dayan ilimin da ...
  • Shin Shedan (Iblis) daga mala'iku yake ko aljanu?
    24433 جن 2012/07/24
    Akwai sabani mai yawa kan cewa shedan aljani ne ko mala'ika, da mahanga daban-daban. Asalin wannan sabanin yana komawa zuwa ga halittar annabi Adam (a.s) ne yayin da Allah ya ba wa mala'iku umarnin su yi sujada sai dai shedan ya ki yin sujada.
  • Mece ce alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s)?
    25096 نشانه های ظهور 2012/07/24
    Bahasi kan alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s) yana daga bahasosi masu zurfi da wuya ta wata fuska wacce tana bukatar karanta dukkan ruwayoyin da suka zo game da haka, sai dai abin da aka fahimta daga ruwayoyi –ko da kuwa a dunkule ne- shi ne kasa wadannan ...
  • Me ake nufi da Koma wa malami, da koyi?
    8853 بیشتر بدانیم 2012/07/24
    Marja’anci da ma’anar kasancewar malami makoma ne shi a karbar fatawa wurinsa a fikihu yana kishiyantar ma’anar koyi da malami ne. Domin a ma’anar koyi yana nufin wanda bai kware ba kan wani lamari ya koma wa wanda ya kware, wato yana nufin ke nan a koma ...
  • Daga cikin matanin hadisin sakalaini guda biyu da aka rawaito wannan ne daidai?
    5857 نبوت و امامت از خاندانی پاک 2017/05/21
    Matanin da ahlussunna suka cirato daga sahihul Muslim da Turmuzi da musnadi Ahmad wanda ke cikin wannan littafan ya zo ne kamar haka “littafin Allah da ‘yan gida na” kuma wannan shi ne matanin da ya shahara a wajen ahlussuna. Amma akwai wani matanin da ba wannan ...
  • Saboda Allah madaukaki ya fada a hadisin kudsi cewa: duk wanda na kashe shi, to ni ne diyyarsa?
    14777 انسان و خدا 2012/07/25
    Bayanin da aka ambata shi wani bangare ne na hadisin kudsi da aka sani da ya zo kamar haka: “Duk wanda ya neme ni zai same ni, wnadaya same ni ya san ni, wanda kuwa ya san ni ya so ni, wanda ya so ya yi bege ...
  • Shin mutum mai yawan tafiya zai yi kasaru kan hanyarsa ta tafiya ko dawowa wacce ba ta kai kwana goma ba?
    6444 2019/06/16
    Maraji”an takalid masu daraja, sun tafi kan cewa mutanen da tafiye tafiye ya kasance matsayin sana”a garesu to wajibi ne su cika sallah su kuma yi azumin ramadana halin tafiyar sai dai cewa game da adadi da gwargwadon tafiyar da za ta kasance da wannan hukunci na ...
  • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
    6150 نقش احزاب و نهادهای مدنی 2012/07/24
    Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...

Mafi Dubawa