Please Wait
10648
- Shiriki
Akwai amsoshi daban-daban tsakanin fatawoyin malamai kamar;
AYATULLAHI KHAMNA’IY (MZ);
Idan ta wakilta shi a kan komai hatta a sadaki da mudda babu matsala mutukar an cika sauran sharudda kamar izinin uba, kaka, ko wa, ga yarinya budurwa, don cika ihtiyadin wajibi, auren ya inganta;
AYATULLAHI SYSTANY (MZ);
Babu matsala auren ya yi;
AYATULLAHI MUKARIMUSH SHYRAZY (MZ)
Idan wakili ne hatta a sadakin da muddar hakan ta gudana tun a daurin auren, auren ya yi
AYATULLAHIL UZMA GULFAIGANY (MZ)
Zaman mutumin a matsyin wakilinta ya wadatar da niyyar matar wajan komai hatta sadaki da mudda, sai idan bayan daurin auren matar ta ji muddar da sadakin ta amince, aurenta ya yi,
AYATULLAHI DAHRANY (MZ)
Ida ta ba shi duk wata cikakkiyar damar wAkilcin auren kan kowane sadaki a kan kowace mudda auren ya yi, Idan kuma ba ta ba shi irn wannan wakilcin ba aure na iya inganta tare da saninta ga sadakin da muddar, hatta ma yardarta ga auren
Domin bukatuwa zuwa cikakken bayani zaku iya duba
1- (sharuddan kulla auren mutu’a) tambaya ta 1238 (mauki’iy: 1225)
2- (auren mutu’a wajan budurwa) tambaya ta 2190 (mauki’iy: 2315)
3- (bayar da sadaki a auren mutu’a) tambaya ta 13237 (mauki’iy: 3494)
4- (sanin sharuddan auren mutu’a) tambaya ta 7454 (mauki’iy: 7664)
Duba mauki’in fatawoyi (Lamba 974)