Please Wait
Dubawa
37000
37000
Ranar Isar da Sako:
2010/02/23
Takaitacciyar Tambaya
Ta wace Hanya ake mangance maita da kanbun baka?
SWALI
Na jima ina fama da wani mummunan yanayi da na ke ji a tunanina! Shi ne da zarar na yabi wani mutum, sai ya shiga wani yanayi na cutuwa. Alhali a duk sanda zan yi yabon, zai kasance ne bisa soyayya da kauna, ba ni da wata mummunar manufa ta boye. Ko da ‘ya’yan ‘yar\'uwata idan na nuna masu kauna a zuciyata, wani abu maras kyau kan samesu. Sannan mutane da dama na mun kallan hakan (maye), harma na shahara da hakan. Kuma ni ban san yanda zan yi in rabu da hakan ba. Ina ganin mummunan yanayi (na maita) ya samu gindin zama da gurbi a gurina!!! Ku taimaka ku nuna mani yadda zan rabu da wannan halin.
Amsa a Dunkule
Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita, inda ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Al’kur'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka shude. Wasu malamai a wannan zamanin suna ganin wasu daga cikin mutane suna dauke da kurwa ta daban ta maita. Kuma ruhinsu ya na da tasiri sarrafa abubuwa daga wani guri zuwa wani gurin, fiye ma da haka. Yana da damar aika sako, kamar tarwatsa haske matsananci. Hakika duk wani Bil-Adama yana da irin wannan kurwar. Sai dai kurwar wani ta fi ta wani karfi bisa wasu dalilai na dabi'a da kan haifar da wasu sauye-sauye na zahiri da na badini. Tsirinsu na iya haifar da sauyi ba tare da shi mutumin ya sani ba. Domin dakushe tasirin maita a musulunci ya tanadi wasu hanyoyin neman kariya da ambatan Allah da yin sadaka.
Amsa Dalla-dalla
Wasu mutane sun dauki maita (kambun baka) da tasirin da ta kan haifar a matsayin tatsuniya maras tushe. Sai dai shi Alkura'ani bai dauki maita a matsayin tatsuniya ba. Bugu-da-kari ya ma bada misalai na tabbacin hakan. Alkur'ani ya kawo inda hakan ya tabbata daga tarihin magabata. Bincike na ilimi ya tabbatar da cewa kurwar mutum tana da wani gagarumin tasiri mai bam mamaki wajen samar da wani yanayi mai kyau ko maras kyau. Lalle Alkura'ani ma ya tabbatar da akwai maita. Ya nuna wasu alamu da suke gaskata abin da tarihi ya tabbatar na daga cikin abin da Alkura'anin ya zo da shi na daga al’umman da suka gabata. Wasu malamai a wannan zamani suna ganin wasu daga cikin mutane suna dauke da kurwa ta daban (maita). Kuma ruhin yana da tasirin sarrafa abubuwa daga wani guri zuwa wani gurin, fiye ma da haka yana da damar aika sako, kamar tarwatsa haske matsananci. Hakika duk wani Bil-Adama yana da irin wannan kurwar. Sai dai kurwar wani tafi ta wani karfi, bisa wasu dalilai na dabi'a da kan haifar da wasu sauye-sauye na zahiri da na badini, tasirinsu na iya haifar da sauyi ba tare da shi mutumin ya sani ba. Domin dakushe tasirin maita, Musulunci ya tanadi wasu hanyoyin neman kariya ta hanyar ambatan Allah da yin sadaka. Wasu masu masana suna ganin wannan kurwar ta kan iyi tasiri a kan wasu ta hanyoyin kulunboto ko siddabaru. Mutane da yawa suna bayyana cewa sun taba ganin hakan ya faru ta yanda su kan kashe dabba ko su girgiza wasu ababe, ko su dakatar da wani inji ko ya daina aiki. Dan haka gani suke bai kamata a ci gaba da inkarin irin wadannan ababen ba. Gani suke ya kamata a yadda cewa wannan abun akwai shi, domin kuwa ilimi da hankali duka sun tabbatar da wanzuwarsa.[1].
An ruwairo daga Amirul mu’minina (as) yana cewa:" Maita gaskiya ce kuma ita addu'a gaskiya ce".[2] Mai tafsirin Amsal yana gani tawasuli da addu'a su kan yi tasiri wajen bata tasirin maita. Su kan hana ko su dakushe tasirinta[3]. An ruwaito daga Ma'aiki (sawa)[4] ya ce: "Lallai maita kan shigar da mutum kabari, ta kuma shigar da rakumi tukunya. Kuma an ruwaito cewa Annabi (sawa) ya wuce ta makabartar Baki'a sai ya waiwaya ya kalli sahabbansa. Ya ce: "Na rantse da Allah mafi yawansu sun mutune sakamakon maita" [5] .
Sannan Allah Ta'ala Ya ce wa Annabinsa: "Kuma wadanda suka kafirta sun yi kusa su zamar da kai da kaifin idanunsu” [6]. Allama Tabataba'e yana cewa abin da ake nufi da “zamar da kai da kai da kaifin idanunsu” watau kamu wa da maita. Ana nufin shi wani nau’i ne mai tasirantuwa da rai, da babu wani dalili na hankali da ya kore yiwuwar hakan. Kusan ta yiyu a samu dalilai da kan tabbatar da hakan. Domin ruwayoyi ingantattu, sun tabbatar da hakan[7]. Kuma Allah Yana cewa a bisa harshen Yakub (as): "Ya ku ‘ya’yana, kada ku shiga ta kofa guda daya, ku shiga ta kofofi daban-daban, amma ba zan iya hana Allah ya yi maku komai ba domin babu hukuncin sai na Allah, a gareshi ne masu dogaro kan dogara" [8]. Duk masu tafsiri sun yi ittifakin cewa dalilin wannan nasihar shi ne; ‘yan uwan Annabi Yusuf dukkansu kyawawa ne, duk da cewa kyawunsu bai kai na Annabi Yusufu ba, amma suma ‘yan uwansa ne. Masu kyawun jiki ne kuma karfafa. Don haka wannan uba mai tausayi yake jin tsoron su dauki hanya daya kasantuwar yawansu ya kai mutum 11, saboda kada su ja hankalin jama'a, kuma alamunsu yana nuna cewa su baki ne, ba mutanen Masar ba ne, kada a masu hassada ta hanyar kura masu ido. [9].
Imam Ja'afarussadik (as) yana cewa: " Da za'a nuna maku kaburbura da kun ga mafi yawan matattunsu, maita ce ta kashe su, domin hakika maita gaskiya ce" [10]. Alhali bincike na ilimi da hankali da gwaji sun tabbatar da cewa lalle dan Adam yana da kurwa mai ban mamaki ta ruhi da ke da tasiri wajen aiwatar da alheri ko sharri da kan haifar da abu mai kyau ko mai muni.
HANYAR YIN MAGANI DA RIGA-KAFI.
Yarda da maita ba yana nufin yarda da al'adu, tatsuniyo da aiki da surkulle kamar yadda jahilai ke yi da sunan Musulunci ba. Shi musulunci ya tanadi neman tsari ta hanyar ambatan Allah kuma ya yi wasicci da yin sadaka dan samun kariya daga tasirin maita. Imam Jafar Assadik (as) ya na cewa: " Maita gaskiya ce, kuma ba zaka iya tseratar da kanka ko wani daga gare ta ba. A duk sanda ka tsoraci wani abu, sai ka ce: 'Ma-sha- Allah! Laa Kuwata illa billahil Aliyyil Azeem”, sau uku. Ya kuma ce: "Idan dayanku ya yi ado ko kolliyar da ta burge shi, kafin ya fita daga gidansa sai ya karanta Falaki da Nasi, insha-Allahu babu abin da zai cutar da shi [11]. An kuma ce yin layar Ayatul Kursiyu hade da ayar “Wa In yakadul lazina kafaru” ana yawo da su, su kan bada gagarumin kariya.
Wani hadisi ya ruwaito cewa Manzon Allah (sawa) ya na nema wa Hassan da Husaini (as) tsari daga sharrin maita da wannan addu'ar: "Ina nema maku tsari da Kalmomin Allah cikakku da da sunayensa daga dukkan sharin namiji da na mace daga maita mai firgitarwa, da sharrin mai kyashi idan ya yi kyashin. Sai Annabi (sawa) ya waigo ya kale mu ya ce: "Haka ne Annabi Ibrahimu (as) ya ke nema wa Annabi Ishak da Annabi Isma'il (as) tsari”. [12] [13] [14] Dangane da abin da ka fada na halin da kake ciki kuwa na cewa da zarar ka yabi waninka sai kurwarka ta kama shi nan take sai ya cutu, to ai baka da tabbacin cewa kai ne ka cutar da shi? Watakila da ma akwai wata matsala sai kuma ta faru a lokacin da ka kale shi, wata kila shi ya sa kake ta yawaita nuna damuwar ka. Koma dai mene abin da ke faruwa ba laifin ka ba ne, musulunci ba zai kama ka da ko wane irin laifi ba. Bayan gudanar da binciki mun sami ruwayoyi da suke bada mafita domin kubuta daga wannan halin da kuma gudun cutar da wasu. Ga kadan daga cikin wadannan hadisan. Idan wani abu a jikin dan uwanka mumini ya burgeka, sai ka tuna [15] ka karanta surar Fatiha da Kulhuwallahu da Falaki da Nasi, da Ayatul Kursiyu, sai kuma ka ce: "Masha'allahu" da "Tabarakallah" ka kuma ce "Masha Allahu Laa kuwata Illah Billah" [16]

[1] Tafsirul Amsal fi Kitabil Munazzal. J 1 Sh 18 da 562 ـ 56 .
[2] Nahajul Balagah, Huduba ta 400.
[3] Nahajul Balagah, Huduba ta 400.
[4] Biharul Anwaar، j 60, Sh 20.
[5] Tafsirin .ihajuz Sadikeen. Zuju'e 9, sh; 391.
[6] Suratul Kalam aya ta 51.
[7] Tafsirul Mizan j 19, sh 388.
[8] Suratu Yusuf aya ta 67.
[9] Tafsirul Amsal fi Kitabil Munazal j 7, sh 260.
[10] Biharul Anwar j60, sh 25.
[11] Biharul Anwaar j 9, sh 128.
[12] Kamar yadda yazo a ruwaya.
[13] Alkaafiy, j 2, sh 56.
[14] ] Almuktabis min "Shour Cheshemiy".
[15] Littafin Dibbul A'immah na Muhammad bn Sulaiman bn Mihraan, daga Ziyaad binu Hurun Al-abadiy daga Abdullahi binu Muhammad Albajaliy daga Abu A Abdullahi (as) yace: "Duk wanda wani abu ya burgeshi a gurin dan uwansa mumini, to ya yi kabbara, domin ita maita gaskiya ce. Muhammad binu Makki ya ruwaito daga Usman binu Isa daga Husaini binu Mukhtar daga Safwanul Jammaal daga Abu Abdullahi, ya ce: "Da za'a tona maku makabarta zaku ga mafi yawan matattun maita ce ta kashesu. Domin ita maita gaskiya ce. Duk wanda wani abu yaburgeshi a gun dan uwansa sai ya ambaci Allah a kansa, idan har ya ambaci Allah ba zai cutar dashi ba. Zuj: 92, sh: 127. [16] Littafin Makarimul Akhlak. Dangane da maita Mu'ammar binu Kallad ya ce: "Na kasance tare da Imam Rida (as) a garin Kusana wanda shj ya, sai ya badani kudin umurceni in saya masa turaruka. Da ya da karbesu sai ya kallasu, sannan ya ce muna: " Ya Muammamar. Maita gaskiya ce. Rubuta Suratul Fatiha da Kulhuwa da Falaki da Nasi da Ayatul Kursiyu ayi laya sai a sata a kwalba, ko makamancinsa. An ruwaito daga Abu Abdullahi (as) yana cewa: "Maita gaskiya ce. Kuma ba zaka iya amintar da kanka ko wani daga gareta ba. Idan kana tsoran wani abu, sai ka ce: "Masha Allah la kuwata illa billahil Aliyul Aziim, sau uku". Sannan idan waninku ya shirya zai fita daga gidansa, kana shirin ya burgeshi, to ya karanta Falaki da Nasi. Idan ya yi hakan da izinin Allah babu wani abu da zai cutar dashi. An kuma karbo daga gareshi (as) cewa duk wanda wani abu na abokinsa ya burgeshi, sai ya sa masa albarka. Domin maita gaskiya ne.
[16]Duk wanda wani abu ya burgeshi a gun dan uwansa, to ya albarkaci abin (yace tabarakallah) domin ita maita gaskiya ce. Biharul Anwaar j 92 sh 128. Aljawaami'u na Dabrasi, daga Annabi (sawa) ya ce: "Duk wanda yaga wani abu ya burgeshi sai ya ce: "Allah Allah Masha’Allah Laa Kuwata Illa Billah." To babu abinda zai cutar dashi. biharul Anwaar. J 92, sh 133.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga