advanced Search
Dubawa
12225
Ranar Isar da Sako: 2006/11/22
Takaitacciyar Tambaya
Ku gaya mana wani hadisi game da iyakokin lullubin Mace
SWALI
Ina son wani hadisi game da iyakokin lullubin mace, ko wani hadisi da yake halatta wa mace ta bayyanar da fuskarta?
Amsa a Dunkule

Ayar 31 daga Surar Nur da ruwayoyi masu yawa sun kawo lamarin hijabi lullubin mata da yadda yake, yayin da Allah madaukaki yake cewa: (Surar Nur: 24: 30-31)

"Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce da Muminai mata da su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, kada su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu ko ubanninsu, ko ubannin mazajensu, ko ‘ya’yansu, ko ‘ya’yan mazansu ko 'yan'uwansu, ko ‘ya’yan 'yan'uwansu mata, ko matansu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya (wadanda suke damfare da su) na daga maza wadanda ba sa bukatar mata, ko yara wadanda ba su tsinkayi (sanin) al'aurar mata ba. Kuma kada su buga kafafunsu, domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, Ya ku Muminai!, tsammaninku ku sami babbar rabo".

Kuma ruwayoyi masu yawa sun zo a littafin alKafi na Kulaini da suke magana game da lullubi da iyakokinsa da bayanin abin da ya halatta ga mace ta bayyana shi. Mas’ada dan Ziyad ya ruwaito hadisi ya ce: Na ji Ja'afar an tambaye shi game da abin da mace zata bayyana daga adon jikinta? Sai ya ce: Fuska da Tafuka.

Yana da kyau mu ambaci cewa halaccin bude fuskar mace yana halatta ne idan sun kasance ba a yi musu ado da kayan kwalliya ba, da kayan ado da kawatawa. Ko da yake ban da wasu adon kamar gyara fuska da girar ido wadanda a bisa al’ada ba a ganin su a matsayin wani ado da kawa.

Amsa Dalla-dalla

Lullubi da suturar mace da kame kai suna da muhimmanci mai girma sosai a musulunci saboda muhimmancin wannan mas’ala a tarbiyya da rayuwar al’umma. Kuma surar Nur: 31, ta yi nuni bayyananne a game da wannan lamarin yayin da ya zo a cikinta cewa:

"Ka ce wa Muminai maza da su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu, wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah Mai kididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa. Kuma ka ce da Muminai mata da su kawar da idanuwansu kuma su kiyaye farjojinsu, kada su fito da adonsu sai dai abin da ya bayyana daga gare shi, kuma su dora mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna kawarsu face ga mazajensu ko ubanninsu, ko ubannin mazajensu, ko ‘ya’yansu, ko ‘ya’yan mazansu ko 'yan'uwansu, ko ‘ya’yan 'yan'uwansu mata, ko matansu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya (wadanda suke damfare da su) na daga maza wadanda ba sa bukatar mata, ko yara wadanda ba su tsinkayi (sanin) al'aurar mata ba. Kuma kada su buga kafafunsu, domin a san abin da suke boyewa daga kawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba daya, Ya ku Muminai!, tsammaninku ku sami babbar rabo"[1].

Da yawan mutane suna tunanin cewa fuska da tafuka ba sa cikin wadanda aka ce a rufe saboda samun dalilai kan haka, kuma akwai alamomi cikin ayar kur’ani da take karfafa cewa an togace wasu abubuwa kamar haka:

a. Togace adon da ya bayyana a ayar da ta gabata, ko dai yana nufin wurin ado ko kuma adon kansa, yana nuna mana rashin wajabcin rufe fuska da tafukan hannaye ne.

b. Sannan hukuncin ayar da ta gaba na wajabcin rufe dukkan gefen wuyar riga yana nuna mana rufe dukkan bangarorin kai da wuya da kirji ne, kuma wannan hukuncin bai yi maganar rufe fuska ba, kuma wannan wani dalili ne kan wannan ra’ayin.

 Domin karin bayani kan hakan muna iya cewa; wasu matan larabawa sun kasance suna sanya mayafi sai su dora gefensa a kan kafadu, ta yadda zai zama wani bangare na wuya da kirji sun bayyana, sai musulunci ya gyara wannan halin ya yi umarni da rufe wuya da kirji ta hanyar sanya mayafi a kan dukkan gefen wuyan riga, domin fuska ta kasance ita kadai ce a bude[2].

A kan hakan akwai ruwayoyi masu yawa daga imamai masu tsarki da suke nuna abin da ake nufi da wannan aya mai albarka da yadda ake sanya lullubi da iyakokinsa.

Daga Fudhail dan Yassar ya ce: Na tambayi Imam Ja'afar Sadik (a.s) game da zira’in mace shin yana daga ado da Allah madaukaki ya kawo a fadinsa cewa: “Kada su bayyanar da adonsu sai ga mazajensu” sai ya ce: Haka ne, duk abin da yake bayan mayafi ado ne, da abin da yake bayan awarwaro[3].

Da ruwayar mas’ada dan Ziyad ya ce: Na ji Ja'afar (a.s) an tambaye shi game da abin da mace take bayyanarwa na adonta? Sai ya ce: Fuska da Tafukan hannaye[4].

Daga karshe ya zama wajibi mu yi nuni zuwa ga bayanai biyu:

1. Halarcin yaye fuska ga mace yana kasancewa ne idan ba ta yi wa fuska ado da kayan ado da shafe-shafe ba, sai dai idan ado ne ba mai yawa da jan hankali ba, kamar dai gyara fuska da gira wanda a al’adance ba a ganin sa a matsayin ado kuma ba zai kai ga yada fasadi ga mutane ba[5].

2. Yayin da malamai suka halatta bayyanar da fuska da tafuka wannan ba yana nufin babu matsalar kallon wadannan wurare ba ne ta fuskacin shari’a domin babu alaka tsakanin wadannan lamurran guda biyu, sai dai abin da muka yi bahasi a nan shi ne mas’alar rufewa kawai[6].

 


[1] Surar Nur: 31.

[2] Al’amsal fi tafsiri kitabil Lahil munazzal: J 11, Shafi: 87.

[3] Alkafi: J 5, shafi: 521.

[4] Wasa’ilus shi’a: j 20, shafi: 202, hadisi 25429; babin abin da ya halatta a gani a jikin mace ba tare da jin dadi ko ganganci ba, da kuma abin da ya wajaba a kanta ta suturce shi.

[5] Kalli: Istifta’at na Imam khomain, j 3, shafi; 256, tambaya 33, 34. Duba: Taudhihul masa’il almahshi, j 2, shafi; 929. Duba: tambaya 1185 da 1560.

[6] Duba littafin mas’alar Hijabi na shahid mutahhari: shafi; 164 – 335.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa