advanced Search
Dubawa
7887
Ranar Isar da Sako: 2012/05/14
Takaitacciyar Tambaya
Shin hadisin da ke cewa “duk wanda ya mutu ba shi da bai’ar imamin zamaninsa (Imaminsa) ya yi mutuwar jahiliyya” daga manzo (s.a.w) yake kuwa?
SWALI
Akwai rawaitaccen hadisi daga sunna cewa “duk wanda ya mutu ba shi da bai’ar imami zamaninsa (Imaminsa) ya yi mutuwar jahiliyya” a fili yake cewa wannan hadisi na nuna muhimmancin bai’a, shin manzo (s.a.w) ya yi wannan magana ne ba tare da nufin a yi mubayi’a ga wani ba? Kuma sannan me ya sa manzo (s.a.w) bai ce a yi bai’a ga wani bayansa ba? Kamar yadda Ahlus sunna ke fada.
Amsa a Dunkule

Bai’a na da bangarori biyu, mai bai’a (sauran mutane) da wanda ake yi wa bai’ar (wato su ne manzo (s.a.w) da imamai (a.s)). Tare da cewar manzo (s.a.w) shi ne hujja kuma shugaba, don haka shi za a yiw mubayi’a a matakin farko wato shi ne farkon wadanda za a yi wa mubayi’a ba shi zai yita ga waninsa ba, ruwayoyi da suka zo daga litattafan shi’a sun karfafa hakan Kamar yadda mai tambaya ya kawo, kuma babu makawa cewa ruwayoyin ba wai kawai kara zube ba wanda da ansan hakan shi ke nan, a’a, bin hanyar tare da tafiya akai shi ne ainihin abin nufi wato bin manzo (s.a.w) ko Imamin zamani lokacin da yake raye.

Akan wannan ne nake cewa shi hadisin bawai kawai an rawaito cewa ai manzo (s.a.w) shi ne farkon wanda za a yi wa bai’a ba, da sunan wanda aiki ya fada a kansa ba (fa’ili) ba kuma shi ne mai yi wa wani ba (maf’uul). Amma idan muka dubi dangantakar hadisin da nuni kan sanya halifa a bayan manzo (s.a.w) a ban kasa wanna ya tabbata tare da dalilai masu yankan shakku cewa manzo (s.a.w) ya sanya Imam Ali (a.s) halifansa bayansa, wannan mun yi bayaninsa sosai ciki mafiya yawan tambayoyi, duba nan kasa ciki bayani a fayyace.

Amsa Dalla-dalla

Amsa wannan tambaya na bukatar bayanin wasu lamurra kamar

 1. Ma’anar bai’a
 2. Matsayin manzo (s.a.w) cikin al’ummar musulmi
 3. Rawaitattun ruwayoyi daga Ahlul-baiti (a.s) kan wajabcin sanin imamain zamani

1-MA’ANAR BAI’A

A Kalmar larabci bai’a na nufin cinikayya, sun kasance idan akabi manzo (s.a.w) ko Imami suka karba daga wajansa, shi kuma ya ba su tare da karfafarsu, ya yi kama da aikin mai saye da siyarwa.

 Amma a ma’ana ita bai’a wani sanannen alkawari ne ake yi wa manzo (s.a.w) ko imamin zamani wajan mika masa wuka da nama cikin kowane lamari ba tare da jayayya ba.[1]

Daga nan zamu kara gane cewa ita bai’a na da bangarori biyu bangaren farko shi ne ke bayyana bangare na biyu, kuma bangaren farko shi ne wanda ake yi wa mubayi’a (manzo (s.a.w)da Imami) bugu da kari manzo (s.a.w) shi ne ma’auni mai shiryarwa kuma shugaba, wanda shi ne ma’aikin da aka aiko kuma imami kama yadda ya zo a kur’ani “Muhammad bai kasance uban kowaba daga mazajenku sai da shi ya kasance …[2].

Wannan aya na nuna manzo (s.a.w) shi za a yi wa bai’a bawai shi ne zai yi wa wani ba (shi ne mai siyarwa ba wai mai siye ba)ta haka ne muka samu kur’ani na yi mana magana bisa waccen bai’ar (siyarwar) kamar yadda ya kara da cewa “lallai wadannan da suka yi maka mubayi’a, ba kai suka yi wa ba sun yi wa Allah (SW) ne …”.[3] da kuma fadin sa madaukakin sarki cewa “hakika Allah (SW) ya yarda da muminai da suka yi maka mubayi’a …”.[4]  wannan na karfafar litattafan da aka rawaito daga litattafan shi’a cewa duk wanda bai san imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar jahiliyya “idan ya mutu bai san Imamin zamaninsa ba ya yi mutuwar jahiliyya”.[5] sanin hadisin ba wai shi ne muhimmi ba, bin hanyar da take ita ce zakasan Imamin zamaninka shi ne manzo (s.a.w) ko Imaminka a lokacinsa, akan wannan ne hadsin baya nufin manzo (s.a.w) ne mai bi ba, a’a shi ne wanda za a bi da sifar wanda aiki ya fada a kansa, ba wai a sigar mai aiki ba.

 


[1] majlisy Muhammad Bakir, mirathul ukuul cikin sharhin akhbar aali Muhammad bolume 20 page 356, darul kutubul islamiyya, bugu na biyu tdahran Iran 1404 AH

[2] suratul ahzab, 40

[3] suratu fat’hi, 10

[4] suratu fat’hi 18

[5] hurrul Aamily, Wasailush shi’a bolume 16 page 246, yadawar mu’assasatu ahlul bait (a.s)

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • Yiwa mace auren dole da hukuncin Dan da ta haifa.
  4426 احکام و شرایط ازدواج 2017/05/22
  A auren dole idan bayan an yi auren (ko da kuwa gwargwadon sakan ne) sai matar ta ji cewa ta yarda da auren to ya inganta, amma a ko wane hali Dan da ta ambata ba zai zama ba na shar’a ba, domin samun Karin bayani a ...
 • Wadananne ne muhimman siffofin tafsirin Kur\'ani na wannan zamanin?
  4008 Ilimin Kur'ani 2019/06/16
  Tsarin tafsirin wannan zamani na da kebance - kebance da kuma da nagartar da babu ita a cikin tafsiran da suka gabata: ta bangaren amsa shibuhohi da warware tambayoyi da lamurran da suke kai- kaiwa a kasuwar tunani da kwakwalen mutane, bisa dogaro da tafarkin yin amfani da ...
 • Mece ce alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s)?
  24389 نشانه های ظهور 2012/07/24
  Bahasi kan alamomin bayyanar Imam Mahadi (a.s) yana daga bahasosi masu zurfi da wuya ta wata fuska wacce tana bukatar karanta dukkan ruwayoyin da suka zo game da haka, sai dai abin da aka fahimta daga ruwayoyi –ko da kuwa a dunkule ne- shi ne kasa wadannan ...
 • mece ce mahangar musulunci a kan samuwar halittu masu rai a sauran duniyoyi?
  9625 آسمان و زمین 2012/07/24
  Akwai tunanin cewa a cikin sauran duniyoyi shin za a samu halittu masu rai ko hankali, daya daga cikin tambayoyin da dan Adam ke neman bayanin su, amma har yanzu bai samu ba. Wasu bayanai a Kur’ani na nuni da samuwar wasu halittu masu rai a duniyar ...
 • Tarihin Adam (as)
  16380 2019/06/16
  Amsa Filla-Filla: bayani kan rayuwar wasu nau”in mutane da aka fara halitta a bayan kasa, da kuma sanin shekara nawa kenan da halittar su zuwa wannan zamani da muke ciki? To hakika babu wata aya da ta yi bayanin hakan cikin kur”ani. Allama daba”ba”i cikin tafsirinsa na ...
 • Shin jagorancin malami sakakke ba kuwa yana nufin a yi gaban kansa a hukuma ba ne?
  5425 گستره عمل ولی فقیه 2012/07/24
  Jagorancin malami wani isdilahi ne na fikihu da yake nuni da fagagen aiki da jagoranci da kuma wadanda suke karkashin wannan jagora, kuma babu wata iyaka a wannan fagen. Sai dai wannan ba yana nufin cewa babu kowace irin iyaka ko wasu ka'idoji a aiwatar da jagoranci ...
 • Saboda Allah madaukaki ya fada a hadisin kudsi cewa: duk wanda na kashe shi, to ni ne diyyarsa?
  14433 انسان و خدا 2012/07/25
  Bayanin da aka ambata shi wani bangare ne na hadisin kudsi da aka sani da ya zo kamar haka: “Duk wanda ya neme ni zai same ni, wnadaya same ni ya san ni, wanda kuwa ya san ni ya so ni, wanda ya so ya yi bege ...
 • mene ne bambanci tsakanin Dabi’u da Ilimin Dabi’a?
  15117 Halayen Nazari 2012/07/25
  dabi’u a luga jam’I ne na ‘’kulk’’ dabi’a/hali/al’ada. Gamammiyar ma’ana saboda kasancewarta al’ada ko hali mai kyau ko mummuna. Amma ‘’Akhlak’’ dabi’u a cikin istilahi ma’anarsa malaman akhlak sun ambaci ma’anoni masu yawa. Bai yiwuwa a gwama tsakaninsu yanda ya dace. Amma sai dai musulmi ...
 • menene hakikanin ma’anar salla?
  32606 Halayen Aiki 2012/07/25
  Salla daukakace ga duk mai san daukaka, ita ce hanya kai tsaye ba tare da shamaki ba, domin ita ce ganawa da ubangiji. Kamar yadda ya zo a Kur'ani mai girma cewa “hakika ni ne ALLAH wanda ba wani ALLAH sai ni to ku bauta ...
 • mi a ke nufi da zayuwar a barzahu kwana daya ko kuma kwana goma?
  10458 برزخ 2012/11/21
  Wannan ayar na nuni da halin da mujurumai suka samu kan su bayan an busa kahon tashin kiyama suna tambayar junan su kwana nawa mu ka yi a duniyar barzahu? Mujurumai sana tunani a duniyar barzahu kwana daya ko kuma kwana goma su ka yi sai wasu ...

Mafi Dubawa