advanced Search
Dubawa
13754
Ranar Isar da Sako: 2012/04/19
Takaitacciyar Tambaya
me ake nufi da rayuwar addini? Shin akwai karo-da-juna tsakaninta da rayuwarmu ta yau da kulum?
SWALI
Mu fa mun zo wannan duniyar ne domin mu yi rayuwar addini, mene ne ma’anar rayuwar addini? Shin kuma akwai cin karo da juna tsakaninta da rayuwarmu ta yau da kulum?
Amsa a Dunkule

Da zamu koma ga Kur’ani mu tambaye shi kamar haka: - Me ya sa aka halicci aljannu da mutane? Kur’ani zai ba mu amsa cewa: Ban halicci aljannu da mutane ba face sai don su bauta mini”1

Sai mu sake yin tambaya mene ne ma’anar ibada (bauta)? Ibada (bauta) na nufin mika wuya da sallamawa ga Allah madaukaki cikin dukkan ayyukanmu manya da kanana, kai! Har ci da sha, na iya zama ibada matukar an yi su da ingantacciyar niyya kuma a karkashin tsarin Allah kamar yadda addini ya zo da shi.

Amsa Dalla-dalla

da zamu koma ga Kur’ani mu tambaye shi kamar haka: - me ya sa aka halicce mu? Jawabinsa zai zama kamar haka: ban halicci aljannu da mutane ba face sai don su bauta mini. Sai mu ce mene ne ma’anar ibada? Domin a wasu lokutan muna kallonta (Ibada) ta tsukakkiyar mahanga. Kuma muna ganin in an ce ibada bai wuce sallah, azumi da aikin hajji da kuma wasu yan bukunkuna. Ko da yake wadannan abubuwan da muka ambata suna daga cikin ibadodi, amma abin tambaya a nan shi ne; shin Allah ya halicce mune domin wadannan ayyuka kawai? Domin in ya zama haka to rayuwar ta zama kuntatatacciya ke nan.

Sai dai da a ce zamu fadada bincike, mu kuma zurfafa tunani a game da ma’anar ibada zamu samu cewa ita ibada tana nufin mika wuya da sallama komai ga Allah madaukaki.

Mulla Sadar a cikin littafinsa (Asfar-Arba’a) yana cewa: Bautar kowane mutum tana zuwa ne dai dai gwargwadon saninsa da Allah madaukaki’ hakan yana nufin cewa akwai wata damfaruwa ta kai tsaye tsakanin bautar bawa ga Allah da kuma ma’arifarsa (saninsa) da Allah din.

Don haka dukkanin yanda mutum ya yawaita sanin ubangijinsa, to ibadarsa zata kara fadada da kuma zurfi, har sai ya kai zuwa haddin da musulunci ke nufi gare shi; .

Me musulunci ke nema daga gare mu? Shin yana so ne mu yi kuntattaciyyar rayuwa ne, wacce ba ta da karsashi? Kawai mu yi ta sallah da azumi da kuma zikiri? Shin musulunci wannan kawai yake nema a wajenmu? Bayan nan kuma sai me?

Babu shakka ko kadan musulunci ba ibada kawai yake nema a gare mu ba. Shin ko kuwa rayuwar ma’asumai (a.s) ita ma nan ta tsaya? Shin ko kuwa amirul-muminina Ali (as) tun safe har yamma sallah da zikiri yake yi ba ya komai? Ai kuwa tabbas ba haka yake ba. Domin kuwa Imam (as) dan siyasa ne, mayaki ne, masani ne, ma’aikaci ne. Domin duk wanda aka ce aikinsa gina rijiyoyi da magudanan ruwa, da kuma jawo ruwa zuwa gonaki masu fako, ba za a ce ya shagaltu da zikiri ba kawai. Ke nan ina ibadar Imam Ali (as) shin ibadarsa ta tsaya a lokacin da yake karanta du’a- kumail? Shin ibadarsa ta kasance a zahirin iya wannan lokacin da yake tsayawa don sallah? Sallar da in yana yinta a kan cire masa sartse bai sani ba. Tabbas ba nan ya tsayaba. Amirul muminina har lokacin da yake fafatawa da abokan gaba ibada yake, in kuwa ba haka ba mene ne ma’anar hadisin annabi (saw) ‘’karan bartar Imam) Ali (as) a ranar kandak ya fi ibadar mutum da aljan’’ shin wannan hadisin na annabi burga ce kawai ga imam Ali. Saboda me za a ba shi dukkan wannan ladan?

Hakan ya kasance ne sakamakon kyakkyawar niyyarsa ya zama ibadarsa. Kai don haka ma gaba dayan rayuwar mutum yana yiwuwa ya canzata ta zama ibada.

Da zamu waiwaya zuwa ga tambayan farko, me taken mene ne ma’anar aikatawa na ayyukan yau da kullum wanda muka saba; kamar ci da sha, me yiwuwa ne muna iya rina su da launin addini, sai ka ga sun zama bautar Allah. Sai dai ana iya yin tambaya cewa ta yaya hakan zai yiwu? Amsar it a ce: da zamu mayar da hankali a kan ka’idodin cin abinci lokacin da muke cin abinci kowane iri to da zai zama ibada ga Allah (swt). Domin ai ba komai aka halasta mana ci ba. Kuma musulunci ya yi hani game da wasu al’amura masu yawa bangaren abubuwan ci da sha. Misali: kamar dukiyar haram, Wajibi ne mu nisance ta kuma tilas dukiyarmu ta zama halaliya, ba zamu ci abin ba face sai mun yi niyyar cewa abincin zai karfafa mana wajen yin aiki, domin cimma burin nan na samun daukaka a wajen Allah, irin aikin da manufarsa sauke nauyin da aka dora mana. Kai hatta barci ma yana iya rikidewa ya zama ibada sai ka ga rayuwar ta rikide tan zama me dadi.

An ruwaito daga annabi (saw) wata rana a masallaci cewa ya fada wa musulmi; idan kuna so ku ga wani mutum daga ‘yan aljanna ku duba na farkon zai shigo (wannan) masallaci (a yanzu), to shi yana daga cikin yan aljanna’’. Ya kasance a tsakanin wadanda suka halarci wurin akwai wani matashi, ya yi kokari sosai don ya ga siffofin ‘yan aljanna, ana nan sai ga wani babban mutum (dattijo) ya shigo masallacin, sai ko matashin ya sa ido game da ayyukansa da shige-da-ficensa, amma bai ga wani abu na musamman da ya kebanta da shi ba, sai ya ce a zuciyarsa wata kila a gida yana yin wasu ayyuka na musamman da suka mayar da shi dan aljanna. Ya yi ta bibiyar wannan babban mutum likacin da ya fita daga masallacin, har ya isa gidansa, da mutumin ya shiga gidansa, sai shi kuma matashin ya tsaya a waje ya kwankwasa masa kofa yana me cewa; ni matafiyi ne, ba ni da masauki, kuma ina so in kwana a wajenku wannan daren, sai me gidan ya yi masa izini ya shiga (gidan). Haka ya cigaba da sa ido ga ayyukan wannan dattijo, har wala yau, bai ga wani kebantaccen abu ba daga gare shi.

Sai ya fada a cikin ransa, ‘’Hakika zancen annabi babu makawa ya samo asali ne game da wani aiki (muhimmi da ya sa shi ya cancandi zamowa daga cikin yan aljanna), Yayin da lokacin kwanciyar bacci ya yi, sai ya ce a cikin ransa (shi matashin) watakila (shi dattijon) zai kwana yana sallah da addu’a da kukan neman gafara; don haka ya kwana bai runtsa ba yana me lura da shi, sai yaga ya sha barcinsa har zuwa sallar subuhi, ya zauna a tare da shi tsawon kwana biyu ko uku, da wani dalili na daban, bayansu, kai daga karshe, sai ya tafi kai tsaye wajen me masaukin nasa ya kwashe labarin duka ya ba shi, sannan ya ce masa; me ye aikinka wanda ka canccanci shiga aljanna saboda shi? Sai mutumin ya ce: ban sani ba shin ko ni dan aljanna ne ko kuwa, ba wani abu nake yi na daban ba, amma sai dai nakan yi iya kokarina inga cewa ayyukana sun zama don Allah! Haka nan, nakan dage ko-da-yaushe ka da in aikata sabo ko kadan.

Don haka ba komai ba ne ya kai manzon Allah babban matsayinsa face wannan sababi kawai.

Ke nan ka ga rayuwar addini na nufin; mutum ya gudanar da ayyukan sa gaba daya har da kananunsu na yau da kullum da niyyar ikhlasi, kuma ya zama sun yi dai-dai da tsarin Allah. A sannan zaka ga rayuwarsa ta canja ta rikede ta addinin Allah. Kuma tasirinta zai bayyana a cikin dukkan samuwarsa.

Da yawa mukan ji ana fadi; ku shigar da albarka ga rayukanku, kuma kamar yanda Ayatollah Uzma Sayyid Baha’uddini (ra) ya kasance yana cewa ku jarraba wadannan mas’alolin har sai kun sami masaniya game da ita’’.

Haka nan kuma kamar yanda Allamah Sayyid Tabatab’i yake cewa: ku yi aiki da ruwayar nan da ke cewa: duk wanda ya tsarkake aikinsa ga Allah kwana arba’ain Allah zai bubbugar da hikima daga zuciyarsa kan harshensa, ku yi wani aiki kwara daya tak don Allah ku maimaita shi tsawon kwana arba’in idan har ba ku ga biyan bukata ba samammiya a cikin wannan ruwayar to ku tsine mini. Wannan yana nuni a kan tsananin sakankancewarsa da samun natija.

  1. Alzariyat 56
  2. Alsayyid bn Tawus, Ikbalul A’amal shafi-467 Darul Kutubul Islamiya Tehran 1367.
  3. Almajilisiy, Muhammadu Bakir, Bihar-al-Anwar juz 67 shafi 249 Muassasat-al-Wafa, Beirut, Lebanon, 1404 h.k.
  4. An nakalto daga Allamah Tabataba’i

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa