Please Wait
14949
Yana inganta a samu tazara a tsakanin annabawa masu shari”a, wato a aiko wani annabi kafin shekara dubu, sai wani annabin ya zo bayansa acikan shekara dubun, kuma wannan mas’alar ba ta warware hadisan da suke karfafa cewa ita duniya ba ta zama ba tare da hujjar Allah a cikinta ba, domin hujjar Allah da ake nufi ya shafi annabawa da imamai da halifofin annabawan.
Hakika ya zo a cikin hadisai cewa duniya ba ta zama ba tare da hujjar Allah ba, wanda zai tsaya da hujjar Allah, ko dai wanda yake a fili a sarari sananne, ko wanda yake a boye a cikin tsoro, don kada hujjojin Allah da dalilansa su rushe.kuma ishara tazo a cikin hadisai a kan hujjojin Allah bayan annabi Isa (a.s) tun daga sham’un dan hamunis safa har ya kare da imamul hujja (A.T.F).
Yana inganta a samu tazara a tsakanin annabawa masu shari’a, wato aiko wani annabi kafin shekara dubu, sai wani annabin ya zo bayan sa a cikan shekara dubun, kuma wannan mas’alar ba ta warware hadisan da suke karfafa cewa ita duniya ba ta zama ba tare da hujjar Allah a cikinta ba, sai dai ba ya inganta a ce kwata-kwata babu shi hujjar Allah din, a ce a duniya babu shi.
A saboda haka a bisa lalura wajibi ne ya zamo akwai hujjar Allah a kowane lokaci da zamani don duniya ta iya wanzuwa da shi, ko dai wanda yake a fili a sarari sananne, ko wanda yake a boye a cikin tsoro”.
Akwai wasu hadisai da suka yi nuni ga jerin sunayen halifofi da annabawa bayan annabi isa (a.s) har zuwa wannan lokacin namu, su ne: sham’un dan hamunissafa, shi kuma sham’un ya yi wasiyya ga yahaya dan zakariyya, shi kuma yahaya dan zakariyyaya ya yi wasiyya zuwa ga munzir, shi kuma munzir ya yi wasiyya zuwa ga sulaimat, shi kuma sulaimat ya yi wasiyya ga burdat, zuwa ga annabi (s.a.w) annabi ya yi wasiyya ga ali har wasiccin ya kare ga imamul hujja (A.F) .[1]
Kumail Dan Ziyad Daya Daga Cikin Sahabban Amirul Muminin As, Ya Ruwaito Cewa: Amirul Muminin Ya Rike Hanuna Ya Fitar Da Ni Zuwa Ga Makabartar Jaban
Da a ka wayi gari sai yaja dogon numfashi sannan ya ce: bayan ya ambaci maganarsa mai tsayi har ya iso inda yake cewa : na rantse da Allah haka al’amarin yake, duniya ba ta zama ba tare da hujjar Allah ba, wanda zai tsaya wa Allah da hujjar sa ko dai wanda yake a fili a sarari sananne, ko wanda yake a boye a cikin tsoro,, don kada hujjojin Allah da dalilansa su rushe.[2]
Ya zo cikin wata ruwaya mai bayani filla filla. daga haruna dan kharijah, ya ce: haruna dan sa’ad al’ijliy ya ce mini: ga shi isma’ilan da kuke mika wuya gare shi ya rasu, shi kuma Ja’afar ya tsufa, a gobe ko jibi zai rasu, sai ku zauna babu shugaba!! sai ban san irin amsar da zan fada masa ba, sai na labarta wa Abu Abdullahi (a.s) irin abin da ya fada sai ya ce: Allah ya kiyaye! Allah ya kiyaye! na rantse da Allah, Allah ba zai yarda wannan shugabancin ya yanke ba har sai dare da rana sun yanke.[3]
Shekhus saduk ya ruwaito a cikin littafin kamalud din, ruwayar da take nuna cewa duniya ba za ta wanzu ba ba tare da hujjar Allah ba, har zuwa ranar tashin alkiyama.[4] kuma shi shekhus saduk ya yi sharhi sosai a kan wannan al’amarin, wanda za a iya dubawa don karin haske.
[1] Ash shekhus saduk, kamlud din, juzu’i na 1 babi na 22 shafi na 212 darul kutubul islamiyya kum, 1395 hijira kamariyya.
[2] Annu’umaniy, muhammd bin ibrahim, alghaibah, shafi na 136 maktabat assaduk Tehran 1397 hijira kamariyya.
[3] kamlud din juzu’i na 2 shafi na 657
[4] A duba kamalud din juzu’i na 1 babi na 22 shafi na 212