advanced Search
Dubawa
15393
Ranar Isar da Sako: 2010/12/26
Takaitacciyar Tambaya
shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
SWALI
Tun lokaci mai tsawo kwakwalwa ta take ta nazari dangane da tsibirin Bamuda cewa yana kunshe da wani sirri. Wasu mutane kan ce wai a gurin ne Imamu Mahdi yake zaune. Sai dai wannan zancen bai gamsar da ni ba. Domin babu wata hujja da ta nuna Imamu Mahdi (a.s) ya na gurin. Ina kuma mamakin nutsewa da bacewar jiragen ruwa manya da kanana da jiragen sama da mahayansu ke yi a duk sanda suka bi ta mashigar. Ina bukatar amsar wannan mahimmiyar tambaya.
Amsa a Dunkule

Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan abubuwan ne wai don Imamul Mahdi (a.s) yana gurin. Tilas mu san cewa Jaziratul Khadra’a a matsayinsu na mazauna kana marayar Imamu Mahdi (a.s) a zamanin gaiba babba an samo ne daga wata hikaya majiyar da masana suka yi inkarin ta, watau ba su amince da ita ba, dalilin raunin isnadinta da tushenta. Don haka batun Jaziratul Khadra’a sam ba gaskiya ba ne! To idan wasu tsiraru sun amince da haka, babu wani dalili da zai tabbatar da Jaziratul Khadra’a ita ce Tsibirin Bamuda mai ban’al’ajabi. Kuma shi Imamul Hujja Imami ne mai tausayi kana zabin Allah ne (s.w.t) don shiryar da dan-Adam da tseratar da su ba halaka su da nitsar da su ba! Tabbas idan ya bayyana zai kakkabe zalunci a bayan kasa, kana ya cika ta da daidaito da adalci, amma hakan ba ya nufin yawaitar kashe-kashe ko kisan kiyashi ba. Domin karin bayani ku dubi wadannan Shafuka. (na yanar gizo):

  1. Shin Imamul Hujja na rayuwa ne a Jaziratul Haddara’a?

http://www.askdin.com/showthread.php?t=4474

  1. Mazaunar Imamul Hujja.

http://www.intizar.bdchtinid23nb.ft2.html

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa