Please Wait
11086
- Shiriki
Feminism lafazin faransanci ne, kuma kalmace ta asalin yaran latin kamar haka ne ta zo da wani banbanci kadan a wasu yarukan kamar turanci da jamusanci, ana amfani da ita da wata ma'ana sananniya feminine, ma'ana ai mace (jinsin mace), femenism kamar wata kalma ce da ked a ma’anar da zai yiwu a yi amfani da ita a ma'ana biyu: ma'anar farko, tana da ma'ana mai gamewa kuma sananniya: wannnan na nufin tunani da cigaba wanda ha kan yana nufin kare hakkokin mata ban da na maza a fagen siyasa, zamantakewar al'umma da tattalin arziki, kuma asakamakon wannan tunanin ne da kuma ci gaban da aka samu har lamarin ya kai ga samar da cibiyoyi da santa-santa da ofisoshin da suke kare nishadin mata ta hanyoyi daban-daban tare da yin amfani da sunaye iri-ire: (taron mata), (tsare-tsaren mata) da (ci gaban mata) da sauran su. Ma’ana ta biyu da ake yin amfani da wannan kalmar da ita, ita ce bayyana siffofin mace da abubuwan da suke fito da ita a wajen mazaje, wannan ma'anar ba abin da muke Magana a kai ba kuma ba ta gaban mu ba. Feminism wani tambari ne na kare hakkokin mace tare da dai-daita ta da hakkokin namiji, tarihin wannan ya dade, sai dai zai yiwu ace wannan ma'anar ta fara ne tun tsakiyar karni na sha tara na miladiyya. An gina kungiyoyi (mobements) da santoci daban-daban wadanda suka share fagen hanyoyi iri-iri duk ba dan komai ba sai dan a tabbatar da dai-daituwar mace da namiji. Idan mun dubi wani bangaren tarihi za mu iya kasa marhalar (mata kan) wannan tunanin ya zuwa marhala (matakai) biyu, marhala ta farko tun farkon karni na sha tara har ya zuwa 1920 (bayan yakin duniya na farko), marhala ta biyu ta fara tun daga bayan 1960.
Hakika mas'alar feminism a marhala ta farko shi ne yunkurin nemawa mata hakkokin su, farkon abin ya kasance a Amerika ne, ai mata a can sun motsa suka yunkura domin magance fifitawa tsa kanin jinsin, wannan yunkurin shi ne nemawa matan hakkokin su, wannan motsin da yunkurin ya dogara ne a kan tushen wasu abubuwan da al'umma suka yi riko da su, wasu kuma a kan tushe na addini.
Wannan yunkurin ya kunshi wasu nukudodi (wurare) masu rauni sai dai tun shekarar 1970-1980 wasu ra'ayoyi tare da karkacewa a janibin feminism ya fara ne daga tatarurrukan masu shiga gona da iri da kuma masu marawa bangaren su baya, abin dai ya ci gaba har zuwa ga masu ba shi kariya, kai har ma ya zuwa ga shigar da ayoyin addini da na mazhaba tsamo-tsaoa cikin lamarin.
Wasu tunaninnika da ra'ayoyi mabanabanta har ma da nazariyoyin sun bayyana a da'irar feminism, sai dai dukkanin su sun yi tarayya a manufa daya ita ce kare hakkokin mata tare da kawar da duk wani banbanci tsakanin su da namiji. A hakika an sami muhawara wacce ta jawo sabani da rarrabuwa a cikin da'irar wannan tunanin na feminism (matuntaka).
Zai yiwu mu nuna wasu ra'ayoyi a cikin abin da da'irar tunani mai fadi ta kunsa ga me da feminism (matuntaka) kamar: ra'ayoyin libraliya, ra'ayin markasiya, ra'ayin gurguzu "Soshiyal" ra'ayi bayan kuruciya da cigaba, da kuma ra'ayin Musulunci. Feminism duk da cewa yana da tarihi mai tsaho sai dai ya shigo bangaren Musulunci ne a karshen karni na sha tara ta hanyoyi daban-daban.
Wannan ci gaban na motsawar al'umma a cikin karnoni ya sami dammar tsara ra'ayoyin sa tare da gyara tunanin sa, wannan ne ya jawo samuwar marhala ta ilimin jami'a da ked a taken (kare matuntaka), bugu da kari wannan ya ba da shinfida da yanayin da ya dace wajen bayyanar da wannan ci gaban a sakamakon samuwar masana dangane da mas'alar al'amuran mata da duk abin da ya shafe su.
Wajibi ne mu waiwayi wata mas'ala mai girma wacce ita ce: hakika faruwar da kuma samuwar feminism a cikin turawan yamma a matsayinsa na motsi ni ci gaban al’umma baki daya wanda ya faru a cikin wani yanayina musamman, wannan ya sa lamarin ya zama yana da tushe duga daya wanda dukkani ra’ayoyi da mahangogi suka zama suna da tasu mahangar a kai, wannan lamarin na da bukatar a kwankwashe shi da gaske, hakan kuma yana bukatar karatu da kuma fursa (dama).