Please Wait
8807
- Shiriki
Kur'ani ya zo da salon bayani kala-kala dangane da halittar Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda za a iya fahimtar cewa halitta Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi ta kasance bisa wasu matakai mabanbanta daya bayan daya, kamar yadda zai zo:[1]
- Halitta daga kasa: "ya ku mutane idan kun kasance kuna kokwanton tashi bayan mutuwa, to ku sani cewa mun halicce ku da turbaya…"[2]
- Cakuda turbayar da ruwa da mayar da ita tabo, "shi ne wanda ya halicce ku da tabo….".[3]
- Sannan sai tabon ya zamo mai wari: "a yayin da ubangijin ka ya ce da mala'iku lalle zan halicci mutun daga kyafaffen yunbu mai wari."[4]
- Sannan sai ya wayi gari jiki hadadde: "hakika mun halicce ku daga tabo hadadde mai kwari (wanda ya hade jikinsa sosai)".[1][5]
- Sannan ya canja ya zama busasshe sosai sandararre: "an halicci danadam daga busasshe, sandararren (tabo) kai ka ce busassar tukunyar kasa wacce ta sha gashi a wuta".[6]
Da wannan ya bayyana a gare ka a sarari cewa abin da ake nufi da halittar mutum daga tabo baki shi ne: bayanin wata marhalar daga marhalolin halittar mutum, da ma'anar cewa an tara wani gwargwado na kasa a matakin farko, kuma bai zo a ciki wata aya daga ayoyi ba cewa launin kasar ya kasance baki ba, abin dai da ya zo a cikin ayoyi shi ne, an halicci mutun da kasa amma ba a bayyana kalar kasar ba.
Sannan sai aka zuba wa wannan kasar wani gwargwado na ruwa sai ta zama tabo, kuma sanannen abu ne cewa idan aka bar tabo ya dauki tsawon lokaci a wani waje lalle launin sa da warin sa za su canja kuma za ka ga launin sa ya karkata zuwa baki-baki, kuma zai rika wari, ko da kuwa (asalinsa) farar turbaya ce, bayan haka a sannu- a sannu sai ya kyafe a inda ya zama sinadari sannan ya zama busasshe sosai tamkar dutse,
Babu wata manuuniya ko dalilin da ke nuna cewa Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi bakar fata ne, ko da ma mun kaddara cewa an halicci Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi da bakar turbaya, to ta yaya za mu iya yin hukunci da cewa wajibi ne amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance bakar fata, wannan kuwa duk da miliyoyin canje-canje da aka gudanar a jikinsa, kuma shin ana da masaniya a kan cewa a yayin da aka gudanar da wadannan canje-canjen a jikinsa launin nasa ya wanzu a baki bai canja ba?
Sakamakon[7] wannan binciken zai tabbatar maka da cewa, ba zai yiyu a iya tabbatar da cewa annanbi Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi bakar fata ne shi ta hanyar ayoyin Kur’ani ba, saboda haka idan har ana so a gano launin fatarsa sai dai ya zamo ta hanyar gudanar da bincike a karkashin fannin da ke tattare da wannan ilimin, ta yadda binciken zai tabbatar da yadda aka samo asalin launoni mabanbanta kamar baki da fari da ja dss… daga launin da annabi Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi yake dauke da shi.
[1] Tafsirul amsal juzu'I na 17 shafi 283.
[2] Surar hajji aya 50
[3] Surar al'ami aya ta 2.
[4] Surar al-hijir aya ta 25.
[5] Surar Saffati 11.
[6] Surar arrahmani 14.