advanced Search
Dubawa
9072
Ranar Isar da Sako: 2011/01/10
Takaitacciyar Tambaya
Dan Da Ma’aurata Biyu Musulmi Suka Haifa, Shin Shi A Gabar Farko Shi Musulmi Ne Ko Kuma mutum Ne Kawai?
SWALI
Salamun Alaikum, Don Allah Ina Son A Amsa Mun Wannan Tambaya: Dan Da Ma’aurata Biyu Musulmi Suka Haifa, Shin Shi A Gabar Farko Shi Musulmi Ne Ko Kuma mutum Ne Kawai, Wato Shin A Take Ya Zamo Musulmi Ne Ko Mutum Ne Kawai?
Amsa a Dunkule

Mutumtakar Mutum A Tare Da Samuwar Sa Take, Ta Yanda A Dukkan Yanayi Ba Zai Yiwu A iya Raba Ta da Shi Ba, Sabanin Shi Musuluncinsa shi Ba a Danfare Da Samuwarsa yake Ba, Sai Dai Zuwa yake Yi, Wato zamu iya Suranta Samuwar Mutum Wanda Ba Musulmi Ba, Kamar Dai Sauran Mutanen da ba Musulmai Ba, A Daya Bangaren Kuma Dan Da Mutum Ya Haife Shi Shi ma Mutum Ne, To Amma Musuluncinsa, A Lokacin Da Yake Yaro Marar Wayo, Bai Karbi Musulunci A bisa Fahimta Ba, Shi Ba Musulmi Ba ne, To, Amma idan Dukkan Mahaifansa Musulmi Ne, Ko Dayan Mahaifansa, Ko Kakansa Musulmi Ne, Za a Yi Masa Hukuncin Shi Musulmi Ne[1].

Ko Da Yake A Bisa Ga Nassoshi Na Ruwayoyi[2] Duk Wani Da Ana Haifarsa Ne A kan Addinin Tauhidi, Wanda Allah Ya Halicce Shi A kai, Saboda Haka Idan Ya Samu Zarafi A bisa Tarbiyyar da ya Samu, Tabbas Zai Riki Musulunci Ne A Matsayin Addini, Amma Ba Wani Abu Daban ba, Sai Dai Zai Yiwu Iyayensa, Ko Al’ummarsa Su Nisantar da shi daga Barin Wancan Halitta Na Tauhidi da aka Masa Ta Hanyar Koyarwa da Gurbataccen Ilimi.

 


[1] Taudhihul masa’il cikin hashiya na Imam Khomein juzu’i na 1 shafi na 78 mas’ala ta 108: Idan dayan iyaye ko kaka namiji na yaron da bai balaga ba, kafiri ne, to, shi ma dan najasa ne, idan kuma dayansu musulmi ne to shi ma dan zai bisu a zamowa musulmi.

[2] Shekhus-saduk, man la yahadhuruhul fakih juzu’I na 2 shafi na 49 hadisi na 1, 668 intisharat jami’atul mudarrissin, kum, 1314hijira kamariyya: ko wani abun haihuwa ana haifarsa ne a kan addinin tauhidi sai dai iyayensa ne suke sashi ya zamo yahudu ko kirista ko bamajuse”

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa