advanced Search
Dubawa
8770
Ranar Isar da Sako: 2012/05/06
Takaitacciyar Tambaya
wadanne hanyoyi da sharuda ne zasu ba mu cikakkiyar damar amfana da dabi’a ta hanya mafi dacewa?
SWALI
wadanne hanyoyi da sharuda ne zasu ba mu cikakkiyar damar amfana da halittu ta hanya mafi dacewa?
Amsa a Dunkule

Bisa la’akari da sadanin ra’ayi da bambancin makarantu masu tsara wa mutum hanya mai fuska daya -wato karkata ga bangaren jin dadin duniya zalla da watsi da makomar mutum, Ko kuma watsi da ni’imomin Allah da dukafa ga tarbiyar ruhi shi kadai- shi ya sa addinin musulunci ya yi tsokaci a kan wannan batu ta fuska matsakaiciya kuma madaidaiciya, bai watsar da janibin rayuwar duniya ba kamar yanda bai kau da kai daga rayuwar lahira ba. A’a ya sanya dan Adam kamar tsuntsu mai tashi da fukafukai guda biyu tare, domin kaiwa ga samun kamala, da kuma kusanci da Allah. Kuma (musulunci) bai ga wani karo da juna ba a daya bangaren na ma’anawiyya (addini) matukar ya kyautata mu’amalarsa a cikinta (duniya) kai! Ita ce ma Gonar Lahira.

Sannan kuma amfana daga duniya a kankin-kansa da kuma kayan more rayuwa din dole ya kasance madaidaici, nesa da almubazzaranci da barna da kwauro da wasa da halittun Allah. A nan ne zamu ga kur’ani na Magana da fayyace cewa daga siffofin mumini ‘’Su wadanda suka yi imani in za su ciyar basa barna ba kuma sa yin kauro, amma suna tsakanin wadannan a bisa tsari(1).

Amsa Dalla-dalla

Addinai da kungiyoyi da makarantu na mahangar rayuwa, wadanda aka bijiro da su a bainar jama’a, sun sanya wasu gama-garin dokoki da kundaye, da ladubba da manufar amintar da bukatun dan Adam, da samar masa ababen more rayuwa na yau da kullum, da jan shi zuwa rabauta da tabbatuwa.

 

Amma kungiyoyin ‘yan holewa, watsi suka yi da bangaren mutumtakar dan Adam kacho-kam, kai har sai da wasu saboda wuce gona-da-iri, ba su ma yi imani da shi ba kwata-kwata. Sai suka tafi a kan ra’ayin da yake killace rayuwar dan Adam da rabautarsa a kan amfani da cin ribar karshe game jin dadin duniya.

A madadin haka sai ga wasu kungiyoyi da makarantu sun yi riga da wadancan, su kuma akidarsu shi ne; rabautar dan Adam tana kunshe cikin fifita bangaren ruhi da boyayyun abubuwan ruhi, har ta kai ma cewa su ba wai sun yi sako-sako- da bangaren jin dadin duniya ba kawai, a’a su a ganinsu rabautar dan Adam tana kunshe cikin nesantar dukkan wani nau’i na jin dadi kwata-kwata, da dukkan sauran abubuwan da ke doron kasa, tare da kiran mutane zuwa ga kaucewa da kare kai daga wannan janibin dungu-rungum.

Kuma kamar yanda aka sani kowane ra’ayi ka ga ana yadawa a bainar jama’a ba makawa ya samo asali ne daga yadda aka fassara, ko ake kallon duniyan nan, da kuma ita kanta rayuwar.

To don haka, muna iya cewa irin wannan karkata mai wuce gona da iri wajen amfani da abin duniya mara iyaka da mike kafa a wajen holewa dabam-dabam, da tabarbarewar al’amura mara iyaka daya game ko’ina a wannan duniyar tamu ta yau, musamman ma kasashen turai; wata alama ce mummuna sakamakon abin da kungiyoyin nan suka aikata na kuntata wa rayuwar dan Adam da kange shi daga amfanuwa da kayayyakin more rayuwa.

Amma a koyarwar musulunci tsayawa ta yi a tsakiyar wadannan ra’ayoyi biyu da aka ambata, sai ta samar da wata matsaya madaidaiciya wacce take tanadar wa dan Adam abin da yake bukata a bangaren rayuwarsu ta zahiri da kuma bangaren mutumtakarsa a tare.

A lokacin da musulunci ya ba da muhimmanci da bangaren mutumtakar dan Adam bai kuma yi ko in kula da janibin rayuwa da bukatar amfani da ita ba.

An ruwaito daga Imam As-Sadik (a.s) cewa ya ce: ‘’Lalle Allah mai girma da daukaka ya baiwa Muhammadu (s.a.w) shari’o’in Nuhu da Ibrahim da Musa da Isa (a.s) tauhidi da ikhlasi da tunbuke gumaka, da kuma halittar ‘fitra’ mikakken addini, sassauka. Da kuma cewa babu rahbaniyanci (gujewa komai na duniya) babu yawon holewa, ya halasta kyawawa a cikinta ya kuma haramta munana, ya kauma sauke nauye-nauyen shari’a da ke kansu’’ (1).

Hakika Manzo mai girma (saw) da Imamai masu tsarki (as) sun tsawatar da al’ummar musulmi daga ruhbaniyanci, da kauracewa al’umma a wurare da yawa. Daga cikin su, muhawarar Sarkin Muminai (a.s) a kan Asimu bin Ziyad, lokacin daya sa yar-shara, ya bar shimfidar gado. sai dan uwansa ya kawo kararsa wajen Shugaban Muminai (as) ana kiran sa Rabiu bn Ziyad cewa; ya kuntata iyalansa, ya fusata ya’yansa (da hakan). Sai Sarkin Muminai (as) ya aika a kira shi, sai ga shi an zo da shi, da Imam (as) ya gan shi sai ya daure masa fuska, sannan ya ce da shi, ‘Shin ba za ka ji kunyar iyalinka ba? Shin ba zaka tausaya wa ‘ya’yanka ba? Shin a ganinka Allah zai halatta maka rayuwa mai kyau alhali bai so ka more ta? Kai kaskantacce a kan haka a wajen Allah(2).

Amma ya kamata a lura cewa bangaren da ake zargi na duniya shi ne damfaruwa da ita da bararrajewa cikin jin dadinta, ba tare da wani sharadi ko iyaka ba, ta yanda mutum na iya manta wajibobin da Allah ya dora masa tun asali; da kuma babban aikinsa ta fuskacin mahaliccinsa, da halittu baki daya, da ruduwa da ita, manta lahira, gami da alfahari da barna da sauran abubawa munana wadanda suke biyo bayanta.

Ba zaka samu wani zargi ba kan duniya, idan mun dauke ta kamar gada ce wacce dan Adam zai ketare zuwa rayuwar lahira da samun kusanci da Allah.

Hakika ruwayoyi sun yi nuni ga haka. Bari mu ambaci ruwayoyi biyu kacal.

  1. Imam Sarkin Muminai (as) ya ce; a lokacin da ya ji wani mutum yana sukan duniya; ‘’Ya kai wannan mai sukan duniya, wanda ya rudu da ruduwanta, wanda aka yaudare shi da barnace-barnacenta, shin ka rudu da duniya, sannan ka rinka sukanta? Kai ne me tuhumarta da laifi? ko kuma ita ce mai tuhumarka? Yaushe ta rudar da kai? shin ba ka tuna rasuwar iyayenka? Ko b aka tunanin makwantar iyayen naka a cikin kasa?..Lallei duniya gidan gaskiya ce ga wanda ya gaskatata, gidan zaman lafiya ce ga wanda ya fahinceta, gidan wadata ce ga wanda ya yi guzuri daga gare ta, gidan wa’azi ce ga wanda ya wa’aztu da ita, masalacin masoya Allah, wurin sallar mala’ikun Allah, masaukar wahayin Allah, wurin kasuwancin waliyyan Allah, sun nemi rahama a cikinta, sun samu ribar aljanna a cikinta, to, wa ye zai soke ta?’’. (3)
  2. An karbo daga Abdullahi Bn Abi Ya’afur, ya ce; Wani mutum ya fada wa Abi Abdullahi (as) cewa: ‘’Wallahi mu muna neman duniyar kuma muna murna da abamu ita! Sai ya ce; ‘’Kuna so ku yi me da ita?’’ Sai ya ce; ’’ In kare mutuncina da na iyalina, in sadar da zumunci da ita, in yi sadaka da ita, in yi hajji da umara’’. Sai ya ce (as); ‘’To ai wannan ba neman duniya ke nan ba, ai wannan shi ne neman lahira’’. (4)

 

Yanzu ta bayyana da cewa, matsayin musulunci a wannan batu shi ne tsaka-tsaki, ya zama tsakanin sakaci da wuce-gona-da-iri. Sannan kuma shi wannan cin gajiyar a kan kansa da kuma su halittu dole ayi taka-tsan-tsan, don gujewa barnatarwa ko almubazaranci, kwauro, da kuma wasa da halittun Allah. Shi ya sa zamu ji kur’ani mai girma yana fayyace mana siffofin muminai; wadanan da in zasu ciyar ba su yin barna, ba su kuma yin kwauro, amma suna tsakanin wadanan a bisa tsari.5

Haka nan ma hadisi mai girma akwai nuni bisa nauyin da ya hau kan al’umma game da muhalli (mazauni) da abubuwan cikinsu.

Sarkin muminai (ali)a.s) ya ce; ‘’Kuji tsoron Allah ya ku bayin Allah game da bayinsa da garuruwansa, kufa ababen tambaya ne har a kan wurare da dabbobi.6

Ga mai neman karin bayani ya duba wadannan wuraren;

Alrafah walnaiim aldunyawiyy wal uktirawiy adireshin bambaya: 7576 (mauki; 7574)

  1. Al Kulaini; Muhammad bn Ya’akub, alkafi zjuz’8 shafi 17, hadisi 1, Darul Kutubul Islamiyyah, Tehran 1365 shamsi.
  2. Masdarin da ya gabata, juz’1 shafi 410.
  3. Nahj-al-balagah, shafi-492, hikma ta-131, Durul-Hijirah, Kum.
  4. Duba; al Kafi, Juz 5, Shafi 72 Hadisi; 10
  5. Surar Furkan aya; 67
  6. Allamah Majlisi, Bihaar-al-Anwar, juz; 32 shafi7 mu’assasat-alwafa; Beirut Lebanon 1404 Hijri.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa