Please Wait
Dubawa
10764
10764
Ranar Isar da Sako:
2008/09/18
Takaitacciyar Tambaya
Wanene Salmanul Farisi kuma saboda me wasu suka hakaito shi a matsayin marubucin Kur\'ani kuma suka ce shi ne wanda ya zo da shi?
SWALI
Wanene Salmanul Farisi kuma saboda me wasu suka hakaito shi a matsayin marubucin Kur\'ani kuma kuma suka ce shi ne wanda ya zo da shi?
Amsa a Dunkule
Salman mutumin Iran ne bafarishe wanda ke da dabi’a ta neman gaskiya ya tafiye - tafiye wajen neman addinin gaskiya kuma ya gwada addinai daban daban har zuwa lokacin da daga karshe ya karbi addinin musulunci, ya yi imani da shi, amma a cikin litattafan ilimin Kur'ani ba a ambaci sunan Salman a matsayin marubucin wahayi ba sam sam.
Amma dagane da cewa an ba shi ko an saukar masa da Kur'ani zamu iya cewa, ba wanda ya yi da’awar cewa Salman ne ya zo da Alkur'ani mai girma ba Annabi (s.a.w) ne ba‼ a hakika abin da aka yi da’awa she ne (wai) Annabi (s.a.w) na koyar ayoyi Kur'ani daga wajen Salman, bayan haka sai ya karanta wa mutane da sunan wahayi a ka yi masa wanda a kan haka ne aka saukar da aya ta 103 a cikin surar Nahali tana mai musanta faruwar hakan.

Amsa Dalla-dalla
Wanene Salmanul Farisi?
Abu Abdullahi ce Alkunyarsa, kuma ya rasu a mada’in a lokacin halifancin Usman, ya rasu a lakacin da ya kasance shi ne gomnan a cen. An rawaito cewa Salman ya bada labari cewa: Ni dan manomi ne, (babansa ya kasance shugaban alkarya) kuma ni mutumin kauyen “je” a Isfahan ne, baba na yana matukar so na ta yadda ya kasance yana tsare ni a cikin gida ba ya bari in fita tamkar wata ‘ya mace budurwa kuma na taka rawar gani kan lamarin addinin majusanci har sai da na wayi gari na zama baban malaman majusanci wanda ke hura wutar bauta.
Baba na ya kasance yana da wata gona, wata rana ya kasance ya shagaltu da wani gini da ya je yi sai ya aika ni in je kewayen gonar a maimaikonsa, a kan hanya sai na ga cocin kiristoci, sai na je kusa da su na saurari yadda suke bauta sai ibdarsu ta burge ni, na ga ibadarsu ta fi ta mu inganci, sai na tambaye su kan asalin wannan addinin a ina halkwatar sa take, sai suka ce min a Sham, ta ke, (bayan da baba na ya hana ni fita ya sa min mari a kafafuwana don kar na koma wajensu......) don haka sai na sulale na guje masa, na tafi Sham, (Syria), sai na zama na kusa da fada, na zama mai yi masa hidima ina koyar abubuwa daga gare shi, har wata rana lokacin wafatinsa ya yi, sai na ce da shi da me zaka yi min wasici?
Sai ya ce dukkanin mutane sun halaka, sun bar addininsu zan yi maka wasici da wani mutum a Mosil, ka tafi wajensa, daga yin wafatin sa sai na tafi wajen wancen mutumin da ya yi min wasiya da shi, ba a dade sosai ba har sai da shi ma ya rasu, kuma kafin wafatinsa na ce da shi: da wa zaka yi min wasici? Sai ya ce ban san wani da ya yi saura kan tafarkin gaskiya ba, in banda wani mutum a garin Nasibaini.
Don haka sai na tafi Nasibaini wajen wannan mutumin, shi ma wannan mutumin na Nasibaini sai wafati ya riske shi, sai ya tura ni wajen wani mutumi a Umuriyya a cikin kasar rumawa, sai na je wajen wannan mutumin na zauna a wajen sa, na yi kasuwanci har sai da na malaki tumakai da shanu, lokacin da wafati ya zo masa na tambaye shi cewa da wa zaka yi kin wasici? Sai ya ce gabaki dayan mutane sun bar addininsu ba wanda ya yi saura kan gaskiya daga cikinsu kuma kwanakin bayyanar annabin da zai zo da addinin Ibrahim sun kusa, kuma zai bayyana a kasar larabwa, kuma zai yi hijira zuwa garin da ke tsakani masu zafi biyu, (manyan duwatsu biyu) wanda yake da yawan dabino. Sai na tambaye shi menene alamomin wannan annabin? Sai ya ce idan ka ba shi kyauta zai ci amma idan ka ba shi sadaka ba zai ci ba yana da tambarin annabta tsakanin kafadunsa guda biyu.
Don haka sai na biyo tawagar fataken Bani kalb wadanda ke kan hanyar su ta dawowa gida, suna isa “wadil kura” sai suka zalunce ni suka siyarwa wani bayahude ni, sai na wayi gari ina kula masa da shuke-shuken sa iya yi masa aikin gona, kuma ina yi masa aiki, wata rana ina tare da shi katsaham sai dan baffansa ya zo wajensa ya saye ni daga hannunsa ya tafi da ni Madina. Na rantse da Allah Ta'ala ina ganin garin na gane (cewa shi ne garin da aka ce Annabi (s.a.w) zai yi hijira zuwa gare shi), kuma sai Allah Ta'ala ya aiko Muhammad (s.a.w) a Makka a lokacin ban taba samun wani labari na sa ba. wata rana ina kan bishiyar dabino, sai dan baffan shigaba na ya zo ya ce: “Allah wadaren kabilar banu kila (Allah Ta'ala ya kashe ko ya tsini wa kabilar banu kila), wallahi suna cen sun taro a kuba suna gewaye da wajen wani mutumi da ya zo musu yau daga Makka yana raya cewa Manzon Allah (s.a.w) ne shi”. Ina jin haka sai na fara kyarma na kusa fadowa kan uban gidana (daga kan dabino), na sauko kasa (ina tambayar dan amminsa sai mai gida na ya mare ni ya ce bai shafe ka ba je ka ci gaba da aikinka), sai na ci gaba da binceke ta ko wace hanya.
Ubangida na bai ba ni wata amsa ba bai ce da ni komai ba kawai cewa ya yi je ka ci aba da aikinka wannan lamarin ba shi da wani amfani gare ka, ka bar shi kawai. Lokacin da dare ya yi dama ina da dan wani dabino da na ajiye sai na dauka na tafi wajen Manzo (s.a.w), na ce: na ji labarin cewa kai mutumin kirki ne, kuma kana da sahabbai ‘yan hijira mabukata talakawa, ga wannan dan dabinon sadaka ce kuma ina ganin kai ka fi kowa dacewa da ita fiye da waninka. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya karba ya bawa sahabbai ya ce ku ci, amma shi bai kai hannusa ba. sai na ce a raina wannan daya daga cikin alamominsa ce, sai na dawo gida. Da gari ya waye sai na dauki sauran dabinon nan na tafi wajensa, sai na ce na ga ba ka cin sadaka, sai na mika masa na ce wannan kyauta ce daga gare ni. Sai Manzo (s.a.w) ya ce: “ku ci” shi ma sai ya ci tare da su. Sai wata rana na tafi kusa da Manzo (s.a.w) a makabartar baki’a a yayin da yake cikin tawagar rakiyar gawar daya daga cikin sahabbansa da ya rasu, sai na kukkutsa tsakiyar jama’a ina zagaye zagaye, kamar ina neman wani abu Manzo (s.a.w) yana zaune a tsakiyar jama’arsa sai na tafi kusa da shi na yi masa sallama sannan na zauna a baynasa ina hangawa ko zan ga hango tambarin annabtarsa, da Manzon Allah (s.a.w) ya lura da ni sai ya fuskanci abin da nake nema sai ya dan gotar da mayafinsa sai na yi ido hudu da tambarin annabta.
Sai na rungume shi ina sunbantar sa ina zubar da hawaye, sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: da ni ka komo, sai na dawo wajen Manzo (s.a.w) na zauna a gabansa na karanto masa kissa ta baki daya har zuwa karshe, sai Manzon Allah (s.a.w) ya yi matukar mamaki sanna ya yi farin ciki ganin cewa sahabbansa sun saurari wannan kissar. Sai na kai ga yakini cewa wannan shi ne wannan annabin a take sai na fadi kasa ina sumbantar kafafuwansa ina kuka. Sannan ya ce da ni, “ya Salman ka koma wajen ubangidan ka” kuma zan siye ka a wajen uban gidanka kan shukar bishiyar dabino dari uku da zan shuka masa da kuma zan ba shi ukiya arba’in [1] ta zinare. Sai Manzon Allah (s.a.w) ya ce: ku temaka wa dan uwanku. Daga nan sai Manzon Allah (s.a.w) ya shuka su baki dayansu da hannunsa, kuma na rantse da Allah Ta'ala dukkaninsu sun kama, ba daya daga cikinsu da ta bushe, kuma a lokacin da aka je wani yaki an kawo wa Manzo (s.a.w) dukiya sai ya ba ni ita ya ce: ji ka biya kudin yantuwarka, sai na je na biyu na sami yanci. Saboda matsalolin da nake ciki da rashin ’yantuwa ban sami damar zuwa yakin Badar da Uhudu ba, amma na halarci yakin Handak. Wasu suna ganin cewa Salman ya rayu shekara dari biyu da wani abu. [2]
Salman da rubuta wahayi
A litattafan ilimin Kur'ani da sauransu ba a kawo sunan Salman a matsayin marubuci daga cikin marubutan wahayi ba.
Salman da kawo Kur'ani
Daya daga cikin shubuhar da ake ta yadawa a lokcin Annabi Muhammad (s.a.w) ita ce cewa ba daga wajen Allah Ta'ala ya zo da Kur'ani ba, lalle ya koye shi ne daga (bal’amu ko kuma Salmanul Farisi). A kan wannan ne kuma domin a bata wannan shubuhar da ake da’awa aka saukar da aya ta 103, daga cikin surar Nahali wacce zamu yi magana a kanta yanzu.
Allah Ta'ala yana cewa: {hakika mun san cewa (mushrikan makka) suna cewa ba kowa ke sanar da shi wannan kur'anin ba face wani mum (daga cikin malaman yahudawa da nasarawa da farisawa), sai dai yaren wanda suke jingina wannan lamari zuwa gare shi ba larabci ba ne, shi kuma wannan Kur'anin an saukar da shi da yaren larabci gangariya[3]}. [4]
Sha’anin saukar da Kur'ani
Dangane da sha’anin saukar wannan ayar an nakalto daga dan Abbas yana cewa: Bil’ama wanda bisa hakika ya kasance makeri kuma barume, bamasihe ne shi wanda ya zauna a Makka, wai shi ne yake koyar da Annabi (s.a.w). kuma an rawaito daga Dhahhaku yana cewa wanda da suke nufi da wannan mutumin shi ne Salmanul Farisi, kuraishawa suna cewa: “Annabi (s.a.w) ya kasance yana koyar kissoshi daga Salman”. [5]
Warware maganar jingin wa Salman kirkiro Kur'ani

- A yayin amsa wannan shubuhar Kur'ani yana cewa: yaren wanda kuke cewa a wajensa Annabi (s.a.w) yake koyar Kur'ani ba larabci mai nagart ba ne, a nan ba a ce (ba balarabe ba ne), wanda a nan Kalmar (Ajam) ana jingina ta ga wanda ba Balarabe ba ne shi amma Kalmar (a’ajami) ana jingina ta ga a’ajam wato wanda bai iya larabci mai nagarta ba, daidai ne balarabe ne shi ko ba balarabe ba ne. ma’ana yaren wanda suke da’awar cewa shi ne ke koya wa Annabi (s.a.w) Kur'ani ba yare ne ingantacce ba kuma baya magana da larabci, to ta yaya Annabi (s.a.w) zai yiyu a ce kur’anin da ke cike da mafi daukakar magana kuma mafi kwarewar da nagartar zance na fusaha a ce a wajensa ya koya?! {kuma wannan yaren laranci ne mai nagarta): wannan Kur'ani da yaren larabci aka saukar da shi kuma babu kokwanto a cikin haka, duk lokacin da larabawa suka kasa zuwa da makamancin Kur'ani - tare da cewa Kur'ani da yaren su aka saukar da shi - to ta yaya kuwa wanda bai iya managarcin yare ba, a ce shi ne zai kirkiro Kur'ani ya koya wa Annabi (s.a.w)?! [6]
- Samanul Farisi ya musulunta ne a Madina kuma lokacin da ya kai wa Annabi (s.a.w) ziyara mafi yawan Kur'ani ya riga ya sauka, tun da mafi yawan Alkur'ani a maka ya sauka, kuma a wannan bangare na Kur'ani ne aka fadi mafi yawan gamammiyar masaniyar da ce cikin Kur'ani, kuma akwai su ma a cikin kissoshin da suka zo a cikin ayoyin madina, banlantana ma abin da ya zo a cikin ayoyin makka ya fi wanda ya zo a cikin ayoyin madina, kuma Salman ai daya ne daga mabiyan Manzon Allah (s.a.w), to wane ilimi zai iya kara masa. [7]
- Dun da su da kan su suna cewa, Salman ya kasance masanin Attaura da Injila, kuma wannan Attaurar da Injilar har a yau dinnan a hannun mutane suke, idan muka auna su da Alkur'ani, zai bayyana a sarari cewa tarihin Kur'ani ba shi ne tarihin da ke cikin wadannan litattafan ba, a cikin Attaura da Injila an jigina wa annabawa abin kunya da kurakurai masu yawa, wadanda dabi’ar kowane mutum game gari kan kyamaci hakan, kai abu ne mai muni ne danganta wannan hatta ga malamin coci kai hatta ma ga mutumin kirki game gari, sai gashi saboda tsaurin ido ana jingina wannan ga daya daga cikin mafi girman masu hankalin a duniya”. [8]
Sakamakon bincike
Salman ba marubucin wahayi ba ne kuma dangane da kirkiro Kur'ani ko kuma kawo shi ba a jigina wani abu makamancin haka zuwa gare shi ba, kadai abin da ya faru shi ne wasu sun yi da’awar cewa ayoyin Kur'ani ba wahayi ba ne, kuma lalle Annabi (s.a.w) ya samo shi ne daga wajen Salman, wanda kuma mun riga mun amsa wannan jawabi a cikin abin da ya gabata.

[1] Daidai da dirhami arba’in kenan wanda duk dirhami rabin da daya bisa biyar din miskale ya kama, kuma duk dirhami goma zai kama miskali bakwai daidai. Kuma miskalin shari’a daidai yake da uku bisa hidun miskalin sairafi ne. don haka duk ukiya daya ta kama miskali sairafi 22 ke nan. Kuma ukiya arba’in din ta ukiaya arba’in din da aka yi yarjejeniya kan Salman a kanta duka ta zama daidai da adadin miskali sairafi duga 880, wanda ya yi daidai da dinare 1100. An ciro daga littafin zindagi, Muhammad (s.a.w), feyenbare islam, j 1, shafii na 145.
[2] Mukaddasi mudahharu dan dahir, afrinesh wa tarikh, tarjamar Muhammad Ridha shafi’I, kudkani, Tehran agahi, bugu na daya shekara ta 1374, j 2 shafi na 802 da na 803. Da kuma Ibni hisham (wanda ya yi wafati shekara ta 218), rayuwar Annabi Muhammad (s.a.w), annabin musulunci, tarjamar sayyid hashim rasuli, Tehran intisharat kitabce, bugu nan a biyar, shekara ta 1375, j 1 shafi 139 zuwa na 147.
[3] Surar Nahali aya ta 103.
[4] Ali mishkini, tarjamar Kur'ani (mishlini) alhadi wum, bugu na biyu shekara ta 1381.
[5] Matarjama, tarjamar mujma’ul bayan, fi tafsiiril kar’an j 14 shafi na 52, intishaarti farahani - Tehran, bugu na daya, 1360.
[6] Tarjamar maj’maul bayan, wanda ya gaba ta j 4 shafi na 53.
[7] Musawi hamdani, sayyid Muhammad bakir, tarjamar tafsirul mizan, daftari intisharat islami jami’e madarrisine hauze ilmiyya kum, kum, bugu na biyar, 1374. J 1 shafi na 100.
[8] Tarjamar tafsiril mizan, Hamadan, j 1 shafi na 101.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga