advanced Search
Dubawa
6745
Ranar Isar da Sako: 2016/12/14
Takaitacciyar Tambaya
Ayar nan ta {Ba kai ne ka yi jifa ba a lokacin da ka yi jife sai dai Allah ne ya yi jifan}. Ya tafsirin ta yake? Me ash’arawa suke cewa kuma me mu’utazilawa suke cewa kuma shin wannan ayar na da alaka da tilastawa da zabi?
SWALI
Dnagane da tafsirin aya ta 17 surar Anfali Menene mahangar Ash’arawa da Mu’utazilawa kuma wane martini aka yi musu kai? Ya lamarin ya ke?
Amsa a Dunkule
A cikin Kur'ani mai girma muna karanto wannan ayar {lalle ba ku yake su ba, sai dai Allah ne ya yake su kuma Ba kai ne (ya kai wannan Annabi) ka yi jifa ba (a lokacin da ka jefe su da kasa da duwatsu) a lokacin da ka yi jife sai dai Allah shi ne ya yi jifan kuma donin Allah zai jarrabta muminai jarrabawa kyakkywa hakika Allah mai ji ne mai gani}.[1]
  1. An nakalto wasu ruwayoyin kan dalilin saukar wannan ayar,[2] wacce ta fi shahara it ace kamar haka: (a yakin Badar jibril ya sauko ya gayawa Manzo (s.a.w) cewa Allah yana umartar sa da ya dibi kasa sannan ya jefa ta inda mushirikai suke don haka sai Manzo (s.a.w) ya umarci Ali (a.s) da ya debo kasa ya zuba masa a tafin hannunsa mai albarka daga nan sai Manzo (s.a.w) watsa kasar idan mushrikai suke ta yanda kasar ta shiga idanuwan baki dayan mushrikan da ke fagen daga sannan sai firgici da tsoro suka cika zukatansa sannan musulmai suka yi galaba a kansu su ka yi nasara a kansu[3]. Wanda wannan al’amarin shi kansa mu’ujiza ce.
  2. Ga yanda litattafan tafsiri suka fassara ayar:
Tare da zurfafa tunani kan sha’anin saukar wannan ayar zai bayyana a sarari cewa wannan ayar tana nuni kan yakin badar kuma jimlar na ta {wa ma ramaita} “ba kai ne ka yi jifan ba” tana yin nuni kan dankin kasa cikin tafi da Manzo (s.a.w) ya yiwa mushrikai kuma abin da ake nufi da kisa shi ne matattun mushrikan da aka kashe a da takubba da ke hannun musulmai a ci gaban ayar kuma sai aka ce “kuma donin Allah zai jarrabta muminai jarrabawa kyakkywa” wannan manuniya ce kan cewa zurin aya zuri ne na nuna baiwar da Allah ya yiwa musulmai. Ma’ana Allah yana so ya gorantawa musulmai temakon da ya yi musu.[4]
Abin da ya kamata a lura da shi a nan shi ne cewa: a zahiri dukkanin wadannan abubuwan da suka faru a yakin badar Manzo (s.a.w) ne da sahabbansa suka yi, amma fadai Allah cewa “ba kai ne ka yi wannan aikin ba” yana nuni zuwa abubuwa kamar haka:-
Na daya: wannan karfin na jiki da ruhi wanda ta hanyarsa musulmai suka iya cin nasara kan makiya, Allah ne ya ba su kuma da wannan karfin na Allah suka samu kusanci zuwa gare shi.
Na biyu: Faruwar mu’ujizoji (misalin in nasara kan makiyin da adadin sa da tanadin sa na yaki ya zarce na musulmai) wanda wannan ya sa musulmai sun kara samun kwarin guiwa su kuma mushrika sun yi rauni. Wannan mu’ujizar ma Allah ne ya sa ta yi tasiri. Bisa hakika za a iya yin bayanin hadafin da manufar Allah Ta’ala a cikin wannan yar da cewa wannan nasara ko wadannan ayyukan musulmai ne suka yi kuma Allah ne ya yi. Ayyukansu ne saboda da nufinsu da kuma jikinsu hakan ya wakana kuma aikin Allah ne tun da shi ne ya ba su karfi ta temako na musamman (ta yanda karfin su kadai bai isa ya samar da wannan nasarar ba).[5]
Amma dangane da abin da aka so a sani kan mahangar Shi'a a kan haka shi ne, Shi'a ba su yadda da cewa mutum na da zabi mudlaki ba kuma ba a tilsta wa mutum ba madlakan ba. (ma’ana ba a tilasta wa mutum ba, kuma ba a sakar masa ba, «امر بین الأمرین» sai dai lamari ne tsakanin lamura niyu).[6]
Amma cewa menene ra’ayin ko mahangar Ash’awarawa da Mu’utazilawa, ya zama lalle mu koma zuwa tushen maginar akidarsu sai mu warware lamarin,
  1. Akidar Ash’arawa kan wannan lamarin shi ne {ba ku ne kuka kashe msuhrikai ba ni ne na kashe su} tare da cewa a sarari da zahiri musulmai ne suka kashe su amma sai Allah ya danganta wa kansa yin kisan da ma watsa kasar {lokacin da ka watsa kasa bai kai ne ka watsa ba ni Allah ni ne na wasta” wanda bisa hakika abin da wannan akida ke cewa shi ne “kai ba ka yi komai ba ni Allah ni ne na yi komai” wanda wannan na nifin mutane ba su da zabi kan ayyukan da su ke aikatawa.[7] Da wani yaren su musulmai sun hau kan aikin da Allah ya yi sai suka zartar (tamkar fatanya da manomi) kuma ba su ne suka kirkiri ayyuakan da suka gudanarwa ba.[8]
Don haka idan muka kalli wannan ayar a mahanar Ash’arawa su suna ganin cewa dukkanin ayyukan da bayi ke yi na imani da kafirci da biyayya da sabo da ayyukan da gabbai ke yi kamar tafiya faduwa da zama da tashi da motsi da tsayawa da makamancinsu dukkanin su ayyuka ne da Allah ke yi kuma a cikin wannan shi dan‘adam abin tilastawa ne shi tamkar kayan aiki ne a wajen Allah kuma yana yin motsi bisa yadda Allah yake so yake nufi kuma duk inda yake so sai  ya yi da shi kuma ba shi da wani katabus na ya yi nufin aikata wani abu ko zabi[9].
  1. Mu’utazilawa ba su jigina da wannan ayar a wajen kafa akidars ba, amma ba su yarda da fassarar tilastawa da aka yi wa wannan ayar ba, don haka suke cewa bayi na da ‘yanci a cikin ayyukansu kuma ana jingina ayyukan da suka yi zuwa gare su ne kawai kuma Allah ba shi da wani hannu kuma ba wata rawa da yake takawa kan ayyukan da bayi suke yi.
 

[1] Surar anfal.
[2] A koma wa asbabun nuzuli na dakawati wanda Ali Ridha fawazazulu ya fassara, j 1 sh 122- 123 taheran, nashrani, 1383. Da kuma jalalud din suyudi aldurrul Mansur j 3 sha 174 175, kum library din ayatulllahi mar’ashi annajafi 1404.
[3] Dabrasi Fadhalu dan Hasan a cikin Maj’ma’al bayan fi tafsirin kur’an j 4 shafi na 814, Tehran nasir khusro bugu na uku  1372. Daba’daba’I sayyid Muhammad  Husain a tafsirul mizani j 9 sh 60 kum daftari intisharati islami bugu na biyar 1417. Makarim shirazi, nasir a tafsiril amsal j 7 sh 115. Tehran darul kutubul islamiyya bugu na daya 1374.
[4] Almizan fi tafsirul kur’an j 9 shafi 38.
[5] Tafsirul amsal j 7 shafi 115.
[6] “Mafhumu amru bainal amraini” tambaya ta 58 “raddi adille jabriyuun” tamabaya ta 528.
[7] Kasimi Muhammad  jamaluddiin, mahasinit ta’awili j 5 shafi 269 – 270 bairut darul kutubul ilmiyya, bugu na farko 1418. Subhani, Ja'afar a cikin lubbiul asar fil jabari wat tafwidhi (alamru bainal amraini) sha 38 kum muassar iamam Sadik (a.s) bugu na daya 1418.
[8] Fakhruddin razi Muhammad  dan umar a cikin mafatihul gaibi j 5 shafi na 466, daru ihya’it turasil arabi bairut bugu na nuku 1420 da kuma jigo mai suna “kasbe ish’ari” tamabaya ta 16786.
[9] Dauui sayyid abdulhusaini a cikin  kalimud dayyib dar takriri akaidi islami, shafi na 108, kitab khane islam. Bugu na hudu 1363.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa