advanced Search
Dubawa
8041
Ranar Isar da Sako: 2006/05/16
Takaitacciyar Tambaya
Wane addini ne Cikamakon Addinai?
SWALI
Wane addini ne Cikamakon Addinai?
Amsa a Dunkule

Addinin karshe shi ne addnin da aka aaiko da ma'anar cewa bayan wannan addini babu wani addin da za a sake aikowa ko wani dan sako da zai zo.

Kamalar addini yana daga cikin sharuddan cikar addninai, da kuam sharadin cewa addinin karhen ba yadda za a iya jirkita shi.

Amsa Dalla-dalla

Addinin karshe shi ne addnin da aka aaiko da ma'anar cewa bayan wannan addini babu wani addin da za a sake aikowa ko wani dan sako da zai zo.

Kamalar addini yana daga cikin sharuddan cikar addninai, da kuam sharadin cewa addinin karhen ba yadda za a iya jirkita shi. Don haka zamu ga cewa addinin karshe yana nufin addinin da aka saukar a karshe da babu wani a bayansa, wato mai zuwa da wannan sakon shi ne mafificin manzanni da aka aiko wa mutane har zuwa ranar kiyama, kuma don haka ne dole ne addinin ya kasance shi ne ya fi kowanne addini kamala, da ya kunshi duk wani abu da ake tsammanin samunsa ga addini. Kuma duk wani abu da ba a samu ya saukar da shi ba wanda yake da rawar da zai taka wurin kamalar dan Adam to ya kasance abu ne wanda da hankalin dan Adam zai iya riskarsa ya gano shi. Ko kuma za a iya samunsa ta hanayar sulukin tsarkake ruhi. Don haka kamalar addini ba yana nufin ya bayar da amsar komai ba karara ta yadda idan mutum ya koma wa kere-kere bai samu amsa ba sai ya ce addini bai kammala ba! Har ma ya ga wannan a matsayin rashin kamalar addini!.

Da wannan ne zamu gane cewa abin da ake nufi shi ne cewa duk wani abu da dan Adam yake neman sa ta hanyar amsar wahayi to akwai shi a wannan addinin, kuma da saukar da irin wannan addinin babu wata hanya da ta rage domin kuma aiko wani addinin, don haka silsilar aiko manzanni ta dakata ke nan.

Kamalar addini tana daga sharuddan cikar karewar aiko wasu addinai, da kuma kasancewar wannan addinin na karshe babu wani canji da zai same shi ko gurbatawa, wannan kuwa ya samu ga addinin musulunci ta hayoyi biyu ne:

1. kasancewar Kur'ani a matsayinsa na mabubbuga kuma madogara ta asalin addini ba zai samu gurbata ba[1].

2. samun ma'auni da hanyar yin bayanin wannan littafin da muka samu a cikin tafarkin tafsirin da ya zo daga ahlul-baiti (a.s) wanda dalibansu suka yada shi kuma ya zo mana kakanni da kakanni zuwa jikoki har yau da zamu ga yadda ya bayyana sosai a cikin ijtihadi da fikihun Jawahiri[2].

Abin da ake nufi da ma'auni a nan shi ne ma'aunin da kowa yake koma wa zuwa gareshi wurin bayanin addini da mahangarsa, wanda da wannan ne aka samu kamalar tsarin tafsiri gun ahlul-baiti (a.s) wanda yake da ka'idoji tabbatattu da yake iya nunawa a tsawon tarihi daidai gwargwadon yanayin zamani da wuri.

Dubawa sosai:

1. Mahdi Hadawi tehrani, wilaya wa diyanat, cibiyar al'adu ta Khaniye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.

 


[1]Mahdi Hadawi tehrani, mabani kalami ijtihadi, shafi 61 - 73.

[2]  Mahdi Hadawi tehrani, bawarho wa fursish'ho, guftare awwal, bahasin cikamakon addini.

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa