Please Wait
21798
Dangane da fassara ko tafsirin jimlar {wadribuhunna} ta cikin aya ta 34 suratul nisa, karkatowa ko farkarwa. Dole ne mu ambaci cewa wannan fassarar ko tafsirin bayada tushe da sanadi na fassara, sai ma dai dalilai na lafazi da suke sabani da hakan.
1} Kalmar {zaraba} a cikin harshen larabci tana da ma'ana duka ne, kuma ma'anarta ta asali shi ne duka na jiki. Sai dai in akwai dalili na lafazi ko wani dalilin daban to za ta iya daukar wata ma'anar daban bat a duka ba. Kamar wannan ayar mai tsarki na cewa {sai muka buga masu misali} [1] saboda haka a cikin wannan ayar zamu fahimci cewa Kalmar misali da tazo tana nuni ne da buga misali ba wai bugun jiki ba. Kamar kuma wannan ayar {muka buga masu tabbarin kaskanci} [2] anan zamu fahimci buga tabbari ne {sitam} da dai ire iren wadannan misalai.
2} a cikin ayar {wadribuhunna} {ku buge su} afili yake ba bu wani dalilin lafazi wanda yake nuni da cewa ba ana nufin dukan jiki bane. Amma sai dai in anyi la'akari da karina wadda akayi amfani da ita domin a cikin ayar an fare ne da cewa kuyi masu wa'azi sai mataki na biyu ku nisance su sai mataki na ukku ku doke su saboda haka sakamakon ya sabama abunda ake nufi.
Saboda inda akace ku karkato dasu ana nufin ta hanyar Magana da soyyaya ne, batun kuyi masu wa'azi wanda ya zo a cikin ayar bai da wata ma'ana domin wannan matakin na wa'azi matakin farko ne sai na biyu nisantar kwanciya in shima bai yi amfani ba, sai kuma asake komawa matakin farko na wa'azi?.
Idan kuma ku karkato dasu yana nufin ta hanyar bayar da kyauta, to wannan fassarar ma ta sabama tsarin tartibin da ya zo cikin ayar domin ance ku nisance su gurin kwanciya sannan kuma adawo ace kuyi masu kyauta wannan ya sabama hikimar ayar.
3} abun nufi da duka na jiki wanda ya zo a cikin litattafan fiqh {hukunce hukunce} dole ya zamo duka marar cutarwa wanda ba zai kai ga karaya ba ko jin rauni ko bayyanar tabo akan fata[3]. Domin abunda ake bugata a duka na jiki shi ne domin akyara zaman gida da na aure, don haka duka anan yana nufin karkatowa zuwa ga rayuwa.
4} a mahangar kur'ani mai girma zalunci, cuta da wace gona da iri abubuwane wanda akai hani dasu, sai dai ba kowane tsanani da takurawa bane yake zama zalunci ba, misali kare kai daga abokin gaba ko da kuwa zai kai ga yaki da zubar da jini[4] dukuwa dacewa tsanani ne da takurawa amma ba zalunci bane, saboda haka ba kowace aya bace a cikin kur'ani wadda ke hani ga zulunci zamuyi amfani da ita domin hani ga tsanani da takurawa ba domin ba kowace takurawa take zama zalunci ba.
5} kur'ani mai girma acigaban {ku doke su} sai ya kawo idan sun yi biyayya sakamakon dukan to kada ku yuce gona da iri ga matan ku. Don haka in muka lura da ayar zamu ga cewa kur'ani baiyi hani ga duka na jiki bane, sai dai abun nufi shi ne idan dukan ya biya bukata sai adaina domin cigaba da shi zai zama wuce gona da iri wato zalunci.
6} kamar yadda akayi nuni kur'ani yana son warkar da wani nau'I na ciyo wanda wasu matan ke dauke da shi kamar yadda masana ilimin kwakwalwa suka tabbatar mai suna {neman cutarwa} wanda idan wannan ciyo ya taso masu to dole sai an doke su domin su koma halin su na farko[5].
Wannan na daya daga cikin mu'ujizozin ilimi na kur'ani mai girma ta yadda akawo hanyar magance wannan nau'in cuta matakin farko in cutar batayi tsanani ba sai bi tahanya Magana {wa'azzi} domin magance ta, in kuma Magana bai yi amfani ba sai adauki mataki na biyu wato janyewa daga kwanciya dasu in shima wannan mataki bai biya bukata ba wato in ciwon yai tsanani shi ne sai a dauki matakin karshe wato duka. Saboda haka da ace ma'anar ku buge su bayana nufin duka na jiki bane da irin wannan nau'in cutar in tayi tsanani so sai bazata warke ba.
7} idan ya zamo irin wannan matakin wato na duka bai zamo abun karbuwa ba, ta yaya ku ka yadda da matakin janyewa daga wurin kwanciya wato mataki na biyu har kuma kuke kafa dalili da cewa gujema mace wurin kwanciya yana karama miji yadda da kai kuma ya kalaba akan tsoron da yake tattare da shi, domin haka afili yake dukan mace shima zai iya kawo sakamakon da matakin da ku ka yarda da shi {wato matakin nisantar kwanciya}
[1] Ra'ad 17
[2] Ali imran, 112.
[3] Tafsirin namune, jildi na 3 shafi na 415.
[4] Ku yaki kafirai gaba daya kamar yadda suka yake ku gaba daya, 36, tauba.
[5] Tafsirin namune, jildi na 3, shafi na 415.