Please Wait
16676
- Shiriki
Sallar firgici, ko sallar Daren Binnewa, salla ce da ake yin ta ga mamaci a farkon lokacin da aka binne shi, don haka ne ma ake kiran ta da salar firgici, domin yayin da mutum yake barin wannan duniayr bai saba da waccan duniyar sabuwa ba, kuma ba zai samu debe kewa da ita, bai san yanayin halayen kabari ba, don haka sai ya samu razani da firgici, wannan sallar tana kawar masa da wannan razanin da firgicin ne da falalar Allah da rahamarsa, a bisa gaskiya ita salla ce don kawar da firgici ba sallar firgici ba.
Amma yadda ake yin sallar kawar da firgici to malamai sun yi bayanai daban-daban kamar haka:
1. A raka’ar farko sai karatan fatiha da ayatul-Kursiyyu, ana karantawa daga «الله لا إله إلا هو..» إلى «وهو العلي العظيم» wato: daga »Ubangiji babu wani abin bauta sai shi« har zuwa »Madaukaki Mai girma« [1], wannan ya isa[2]. »ba tare da surar Tauhidi ba«. Sai kuma a raka’a ta biyu ya karanta surar fatiha sannan sai surar Kadari 10 »Inna anzalna hu«.
Bayan sallar ta kare sai mai salla ya ce: «اللهم صلِّ على محمد و آل محمد و أبعث ثوابها إلى قبر فلان» wato; »ya Ubangiji ka yi aminci ga Muhammad da aalayen Muhammad, ka aika ladanta kabarin wane« ya kawo sunan mamacin.
2. Ko ya karanta ayatul-Kursiyyu a raka’a ta farko bayan fatiha har zuwa fadinSa Madaukaki «و هم فيها خالدون» wato; »wa hum fiha Khalidun«.
Sannan akwai wasu yanayin da aka kawo kan wannan lamarin, a cikin hadisin annabi (s.a.w) ya zo cewa: “Babu wata awa da ta ke mafi tsanani ga mamaci fiye da daren farko, to ku tausaya wa mamatanku da sadaka, idan ba ku samu ba to sai dayanku ya yi salla raka’a biyu – yadda ake yin ta kamar yadda ya zo a ruwayar da aka kawo shi ne - Ya karanta fatiha sau daya, da kulhuwallahu sau biyu. A raka’a ta biyu kuma sai ya karanta surar Alhakumut takasur sau goma, bayan sallama sai ya ce: اللّهمّ صلّ على محمّد و آل محمّد، و ابعث ثوابها الى قبر فلان بن فلان، Ubangiji ka yi aminci ga Muhammad da aalayen Muhammad, ka aika da ladanta zuwa ga kabarin wane dan wane, sai Allah ya aika masa na take da mala’iku dubu kabarinsa, kowane mala’ika yana da tufafin ado dubu, a kuma yalwata masa kabarinsa daga kunci har ranar da za a busa kaho, kuma mai sallar a ba shi lada adadin abin da rana ta haskaka shi, kuma a daukaka masa daraja arba’in[3].
[1] Bakara: 255.
[2] Nukak Majma’aul Masal’I, <Gulfaigani>, j 1, sh 190, s 261.
[3] Hashiyatul Mafatih, salatul amwat, sh 354. Tahrirul Wasila, j 1, sh 97.