advanced Search
Dubawa
13594
Ranar Isar da Sako: 2010/11/30
Takaitacciyar Tambaya
Na karanta a cikin nahjul balaga cewa Imam Ali (akwai sanda ya taba ce wa wani bakawarije “kai wawulo” ma’ana maras hakora! Shin ya kyautu wannan tozartawa ta fito daga amirul muminin?.
SWALI
Na karanta a cikin nahjul balaga cewa Imam Ali (akwai sanda ya taba ce wa wani bakawarije “kai wawulo” ma’ana maras hakora! Shin ya kyautu wannan tozartawa ta fito daga amirul muminin?.
Amsa a Dunkule

Ka iya samun wani mutum yana kokarin cin mutuncin wani da yake adawa da shi ko ta hanyar bata masa rai da tsawa da tada hankali. To shi Musulunci yana ba da damar ramuwa, watau “ramuwar gayya”. Sai dai a garin ramuwar bai dace a ci mutunci ba. Sai dai Amirul muminina a ko da yaushe (a.s) yana fuskantar masu ada’wa da batanci da masu hammaya da shi kamar Kawarijawa da wasunsu ta hanyar kafa musu hujja ko kuma yin shiru da kyaliya a lokuta da dama, baya rama wulakanci ta hanyar yin wulakanci face bisa lalura idan yin hakan ya zama tilas ya yi. Danga ne da tambayar kuwa, tilas mu dubi Kalmar “wawulo” ko “rashin hakora” ba dole ba ne ya zamana cewa Amirul muminin (a.s) ya furta hakan da nufin wulakanci. Domin a wancan zamanin sau da dama a kan yi wa jama’a lakabi ne da wasu alamomi na jikinsu na zahiri ba tare da nufin wulakanci ba, babban misali a nan shi ne Kalmar “Ashtar” (mai fafakekken ido mai yagaggar gira) ga “Malik”.

Amsa Dalla-dalla

Da farko dai ga nassin da ku ke maga a wannan tambayar daga Nahjul balaga (huduba ta 184) kana zamu amsa tambayarku. Zancen da ya zo a Nahjul balaga yadda yake: “A wata Maganarsa da ya fada wa Buruj bin Musahar Adda’i wanda bakawarije ne bayan ya daga murya ya ce masa: [babu wani hukunci sai na Allah]. Sai Imam ya ce masa “Rufe mun baki! Allah wadaranka mai wawulo. Wallahi gaskiya ta bayyana sai ka noke ka make muryarka, sai da karya ta leko sai tauraronka ya bullo kamar kahon dan akuya”.

Idan muka dubi tarihi zai bayyana mana cewa karkataccen tunani irin na Kawarijawa shi ya haifar da takensun nan na “Babu wani hukunci sai na Allah”. Da shi ne suka haifar da kokwanto a tafiyar Amirul muminin (a.s) da kawo cikas gun cin nasara a yakin Siffaini. Kana sun dauki yarda da sulhu- wadda rauninsu da wautarsa suka haifar- hujja ce ta kafurtar da Amirul muminin Ali (a.s) kuma a karshe suka yi amannar rashin hallaccin kowace hukuma, kana a karshe suka yarda da zaman kara zube.

Hakika Amirul muminin Ali (a.s) ya Sha kafa musu hujja sau da dama da nufin ruguza dalilansu.[i] Bai taba barin dama ta musa nasiha ba matukar zata yi tasiri a gare su, kamar yadda ya zo cikin Da’a’imul Islam daga Amirul muminin (a.s) ya yi huduba a Kufa sai wani mutum daga cikin Kawarijawa ya mike ya ce masa: “Babu wani hukunci sai na Allah” Sai Imam Ali ya yi shiru, sai wani ya sake fada, wani ma ya sake mikewa. Da suka yawaita fadan sai ya ce: “Kalmar gaskiya ake nufin barna da ita”. Ya ce kuna da hakki uku a kan mu, ba za mu hana ku zuwa masallatan Allah ku yi salla ba, ba zamu hana ku ganima ba matukar tana hannummu, ba za mu fara yakar ku ba har sai kun yake mu”[ii].

A kwai misalai da dama kamar yadda ya zo a cikin Tahzebul ahkam: “ Imam Ali ya na sallar asuba Ibn Kauw’a na bayansa sai ya jawo aya “Kuma hakika an yi wahyi a gare ka da wadanda suka gabaceka in har ka yi shirka, aikinka zai rushe ka kasance cikin tababbu” Sai Imam Ali (a.s) ya saurara don girmama wa ga Kur’ani har ya kammala ayar, zai ci gaba da karatu sai Ibin Kawa’a ya nanata karutun ayar Imam (a.s) ya sake shiru, sai shi ma Ali (a.s) ya jawo wata aya: “Kuma ka yi hakuri alkawarin Allah gaskiya ne, kada wadan nan da ba su sakankance da (Allah) ba su razana ka”.[iii]

Amma duk da wadannan dalilai da kau da kai, akwai marasa sani da babu wani jihadi da suka taba yi, kana ba wasu fitattu ba ne a bainal jama’a, amma gani suke zubar da martabar Amirul muminin (a.s) dama ce ta samun fice a cikin al’ummar Musulmi ta amfani da wannan damar. Wannan yana nuna cewa ba za’a iya samu maslaha da wadannan ta hanyar tattaunawa ta fatar baki da ba da hujja ga wadannan mutanen ba. Ashe ke nan babu wata dubara ga miyagun mutane masu zunubi da mutakabbirai sai mayar musu martani da salo irin nasu da lafuza irin nasu ta hanyarsu. Kana afuwa da yafiya idan suka yawaita ba zasu tsinana komai ba sai ba da kafa ga Shakiyyai ‘yan tarzoma, a karshe yakan haifar da fitina tsakanin jahilai.

Imam Ali (a.s) yana siffanta irin wadannan ga Kumaili bin Ziyad yana cewa: “---su gayyan sodi ne ‘yan mijin iya baba, a duk inda iska ta kada sai su karkata, ba su neman su haskaka da hasken ilimi kuma ba su jingina da wani rukuni kwakkwara”[iv]. To shi ma “Buruj bin Musahar” ya na cikin wannan kason wanda da binciken ya ke yi saboda neman gaskiya zai iya kawar da tasa matsalar idan ya kai ta gaban Imam (a.s) ko daya daga cikin mabiyansa da mataimakansa har ya gamsu ta hanyar ba da hujja ta ilimi da za ta kai ga kyakkyawar natija. Sai dai cikin sauki zai amsa kiran ya bi rudu ba wani kace-nace kuma ya yi amfani da hakurin Imam Ali (a.s) da hakurinsa da nufin cutar da Imam da tozarta shi. Amma a gefe guda mun san a Musulunci ramakon gayya ya halasta amma bisa Sharuda, kamar yadda Allah (SWT) Yake cewa: “Wata mai alfarma daidai yake da wata mai alfarma, alfarmarsa abin yi wa sakayya ce, saboda haka duk wanda ya yi shisshigi a kanku da yaki ku yi shishshigi a kansa da irin shisshigin da su ka yi a kanku, kuma ku ji tsoron Allah hakika Allah Yana tare da masu tsoronSa”.[v]

A irin wannan yanayi idan wasu mutane suka dauki gabar cin zarafin Amirul muminin da abin da jama’a suke ganin sa a matsayin cimmutunci ne da tuhumarsa da kafurci da kokarin bata shi a tsakanin jama’a, buku da kari abin da zai haifar da bata tunanin da bata Addini, to a irin wannan hali, a bisa dabi’a ya dace Amirul muminin ya mai da musu da martini da irin nasu slon. Sai dai kamar yadda tarihi yake nuna mana a lokuta da dama ya kan musu martini ne da ya dace ko kuma ya yi shiru ya kyale. Idan kuma zai yi martini ya kan yi amfani da kalmomi masu harshen damo kamar “dan masaki” da “wawulo” da ma’anarsa ta gabata.

A wani guri zamu ga inda Amirul muminin (a.s) ya kira wani ya umurce shi da fita yaki a Kufa wanda shi mutum ne mai son kai sai ya ki bin umurnin Imam Ali (a.s) na fita zuwa yaki sai ya kira shi da suna “dan masaki” don aibatashi[vi]. A nan kalmar “masaki” ta kan iya daukar ma’anar saka wanda a zamanin sana’ar ba ta da tagomashi. Sai dai da muka dubi wasu ruwayoyi sai suka nuna mana abin da ake nufi da masaki shi ne (mai saka ko mai kitsa karya)[vii], ba yana nufin aibata wannan karamar sana’ar ba ne.

Kalmar “wawulo” da ke nufin “maras hakora” ta iya nufin wata sifa ce ta wani mutum ba tana nufin aibata shi ba, kamar yadda Kalmar Ashtar take nufin “mai fafakekken ido mai tsagaggar gira”. Amma ba ana nufin aibata Malik ba ne wanda kwamanda ne babba a rudunar Amirul muminin (a.s). A wata fuskar “wawulo” na iya daukar ma’nar rashin basira da fusaha ta magana, wadda siffa ce da kawarijawa suka yi fice da ita. Ashe ke nan duk mutumin da aka haramta masa fusahar magana ke nan kamar maras hakora ne da maganarsa ba ta fita a fahimce ta saboda rashin hakora.

A bisa abin da ya gabata duk wani zance da ayyuka na waliyyan Allah ba za mu fassara su da ma’anarsu ta zahiri ba.

 


  1. Misalin abin da muka fada ya zo a Nahjul balga sh 40 da sh 82, dabaa’in Darulhijra, Kum, “A wani. zancensa da (a.s) ya yi a cikin Kawarijawa a lokacin da ya ji maganarsu cewa: Babu hukunci sai na Allah sai ya ce: (a.s) Kalmar gaskiya ake fufin karya da ita. Haka ne babu hukunci sai na Allah, amma abin da wadannan ke cewa babu jagora sai Allah, alhali dole a samu shugaba a cikin jama’a nagari ko fajiri da zai amfani mumini da imami da ‘yancinsa ya dadadawa kafuri ya yada sakon Allah ya tara ganima ya yaki makiyi ya kawo zaman lafiya ya kare mai rauni daga mai karfi domin mumini ya sarara idan fajiri ne a huta da shi”
  1. Attamimi Almagribi Nu’uman bin Muhammad, a Da’a’imul Islam j1,sh393, Darul Ma’arif, dabaa’in Masar 1385 H.
  1. Ashshek Dusi Muhammadu bin Hassan, a Tahzebul’ahkam j3 sh35 Darulkutub Islamiya Tehran, 1365 H
  1. Nahajulbalaga hudubz ta 147, sh 496, dabaa’in Darulhijra, Kum,
  1. Bakara:194.
  1. Almajlisi Muhammad Bakir, a Biharul’anwar, j32, sh86, dabaa’in Mu’assasatul wafa’a Berut 1404 H.
  1. Alkulaini Muhammad bin Yakub, a Kafi j2, sh 340,j10, dabaa’in Darulkutub Islamiya Tehran, 1365 H.

 

 

TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa