advanced Search
Dubawa
6331
Ranar Isar da Sako: 2012/12/08
Takaitacciyar Tambaya
Daga cikin matanin hadisin sakalaini guda biyu da aka rawaito wannan ne daidai?
SWALI
‘Yan Shi\'a suna cewa Manzo (s.a.w) a karshen rauwarsa ya yi bayanin cewa: bayan wafati “ni zan bar muku abubuwa biyu na daya shi ne Kur\'ani na biyu shi ne ‘yan’gida na”. Su kuma ahlussuna suna cewa: Kur\'ani ne da sunna, wannan ne daidai kuma daga ina aka samo ko wane daga cikin wadannan hadisan? Kuma don me dakta shari’ati a cikin littafinsa na shi’anci safawiyyawa yake cewa Kur\'ani da sunna?
Amsa a Dunkule
Matanin da ahlussunna suka cirato daga sahihul Muslim da Turmuzi da musnadi Ahmad wanda ke cikin wannan littafan ya zo ne kamar haka “littafin Allah da ‘yan gida na” kuma wannan shi ne matanin da ya shahara a wajen ahlussuna.
Amma akwai wani matanin da ba wannan ba da ya zo a cikin litattafai sahihai na ahlussunna wanda Hakaim ma ya nakalto shi a a cikin littafinsa, kuma abu huraira ne kadai ya nakalto ruwayar Hakim, wacce Shi'a ba su taba yarda da ita ba amma akwai wata ruwayar ma da ke cikin litattafan ahlussuna da sahabbai kamar su abu saidul khudri da zaidu dan arkam da zaidu dan sabit suka nakalto wanda wannan ruwayar ta su ta fi inganci da aminci fiye da wadda hakim ya kawo a cikin littafinsa.
 
Amsa Dalla-dalla
Hadisin sakalaini na daga cikin ruwayoyin da kimanin mutane talatain daga cikin sahabbai ne suka nakalto shi kuma sama da mutun dari biyu daga malaman ahlussuna ne suka yi tsakaci da cewa kimanin litattafai dari biyar ne suka rawaito shi[1]. Kuma zamu iya komawa zuwa jigo mai namba 6921 sahihul bahari da hadisus sakalaini domin mu sami Karin bayani kan maciratar wannan hadisi. Amma donmin mu kawo samfurin hadisin a cikin litattafan Shi'a za mu iya komawa zuwa littafin nan madaukaki kafi. Ya zo a a cikin litattafin cewa Manzo (s.a.w) ya na cewa: «إِنِّي تَارِكٌ فِيكُمْ أَمْرَيْنِ إِنْ أَخَذْتُمْ بِهِمَا لَنْ تَضِلُّوا كِتَابَ اللَّهِ عَزَّ وَ جَلَّ وَ أَهْلَ بَيْتِي عِتْرَتِی»‏؛
“Ni mai bar muku lamura biyu ne idan kuka yi riko da su ba za ku taba bacewa ba har abada, littafain Allah da ahlin gaida na turakata”[2].
Matanin da ahlussunna suna nakalto wanda shi ne ya zo a cikin littafin Sahihil Muslim[3] da Turmuzi[4] da Musnadi Ahmad[5] ya zo ne kamar haka “littafin Allah da ‘yangida na” wanda kuma shi ne shahararren a tsaka-tsakin ahlussunna.
Amma akwai wani matanin da be zo ba a cikin litattafai sahihai ba, kuma Malam Hakim Nishaburi ya kawo shi cikin littafinsa, ya tsara littafin nasa da yanayin da ya ke tara hadisai da buhari da musulim ba su fitar da su a cikin litattafansu ba, Hakima ya nakalto hadisin yana mai cewa: «....عن أبی صالح عن أبی هريرة قال: قال رسول الله (ص): إنی قد تركت فيكم شيئين لن تضلوا بعدهما: كتاب الله و سنتی و لن يتفرقا حتى يردا علی الحوض».
An karbo daga abi salih daga abu huraira ya ce: Manzo (s.a.w) ya ce: “Ni mai bar muku abubuwa biyu ne ba za ku taba bacewa ba matukar kun yi riko d su littafin Allah da sunnata kuma ba zu taba rabuwa ba har sai sun riske ni a tafki”.[6]
Kamar yadda aka gani a sarari wannan ruwayar an karbo ta ne daga Abuhuraira[7] kuma matanin wannan ruwayar ya yi tsananin kama da wacce ta zo a sahihu muslim da musnad Ahmad in ban da Kalmar “sunnata” wacce a wadannan litattafa da sauran litattafai Kalmar “’yangidana” ce ta zo.
 
Dalilan Fifikon Matanin Kalmar ‘Yangidana A Kan Matanin “Sannanta”
Domin tabbatar da cewa matanin ahlin gidani ya fi na sunnanta inganci zamu yi nuni zuwa dalilai kamar haka:-
  1. Ruwayar ‘yan gida na ta zo a cikin litattafan ahlussunna na asali misali sahihu muslim, turmuzi da musnadi Ahmad, amma ruwayar da ta zo da sunnata kamar yadda muka yi bayani a baya Hakim ne ya kawo ta a mustadraki din sa.
  2. Ruwayar Hakin nishaburi abuhuraira ne kadai ya rawiato ta wacce Shi'a ba su taba yarda da inganci ta ba, amma sauran ruwayoyin da suka zo a wasu litattafan daga sahabin nan kamar su Abu sa’idul khudri,[8] zaidu dan arkam[9] da zaidu dan sabit[10] a mahanda ta adadi da inganci maruwaita ta fi wacce ruwayar ta Nishaburi inganci.
  3. Ruwayoyin da suka zo da matanin (Yan’gida na) ta kasance ruwaya ce da sunna da Shi'a suka yarda da ingancinta, ma’ana a duniyar musulunci amfi yarda da wannan ruwayar.
 
Warware Cin karo Da Juna Tsakanin Wadannan Ruwayoyi Biyu
  1. La’akari da bayanin da ka fada a sama da kuma tsananin kamanceceniyar da ke tsakanin wadannan ruwayoyi guda biyu za mu iya kai wa ga sakamako kan cewa matannin da yake mashhuri a wajen  malamai shi ne wanda ya zo da “yan gidana” kuma Kalmar “sunnata” da ta zo a waccen ruwayar ko da ya zama bisa rabkanuwa ko kuma da gangan aka sa ta aka cire “’yan gidana” saboda kasancewar wannan rawayar ita kadaice ta zo ta hannun abuhuraira abin da zai tabbatar da wannan tsammani shi ne Abuharaira tare da wadanda kuke tunanin irin na sa tun bayan warfarin Manzo (s.a.w) suka yi nesa da Ahlulbaiti kan abin da ya faru na lamarin wanda zai gaji manzon Allah (s.a.w) kuma suke kokarin nuna cewa su ne a kan gaskiya ta ko wace hanya. Donim waraware wannan cin karo da juna ruwayar abuhuraira za ta zama ba abar la’akari ba ce kuma ta fadi a inganci.
  2. Tsammani na biyu - duk da ruwayar na da rauni sosai-   shi ne cewa Manzo (s.a.w) ya fadi dukkanin guda biyun ma’ana mashhuriyar ruwayar nan da ta zo take cewa: “zan bar muku abubuwa guda biyu littafin Allah da turaka ta, ‘yan gida na” a wani wajen kuma sai muka ji abuhuraira shi ka dai yana cewa ko kuma mu ce ya rawaito: yana cewa Manzo (s.a.w) ya ce: “ wadannan abubuwan biyu su ne littafin Allah da kuma sunnata” a wannan mahamgar wadanna ruwayoyi guda biyu ba su ci karo da juna ba tun da sunnar Manzo (s.a.w) da ahlinsa ba su ci karo da juna ba ta ko ina, kuma Ahlulbaiti su ne suka fi kowa sanin sunnar Manzo (s.a.w) kuma su suka fi kowa yin aiki da ita[11]. Don haka zai zama kene an hada tsakanin ruwayoyi guda biyu bisa ga abin da suke cewa kuma sun zama suna karfafa junansu.
Sakamako: rawayar da jimlar “turaka ta ‘yan gidana” ta zo a cikin ta ba kawai ‘yan Shi'a ne suka inganta ta ba hatta ma sunna sun tafi kan cewa ta fi zama mashhuriya a wajen su. Don haka an riga an yi bayanin hakikanin yanda ingancin wadannan matanoni guda biyu su ke kuma duk marubuci mai adalci zai ya zama lalle gare shi ya yi nuni zuwa wannan bayanin da ya gabata a cikin bincikensa.
 

[1] Husaini tahrani , sayyid Muhammad  Husain, Imam Shanasi, J4 Sh 208, Nashru Allama Taba’taba’I, Mashhad bugu na uku 1426.
[2] Kulaini Muhammad  yakub al-kafi, wanda aka bibiya aka gyara, gaffari Ali akbar Akhundi, Muhammad , j 1 sh 294, darul kutubul islamiyya, Tehran, bugu na hudu, 1407.
[3] Sahihu Muslim j 7 sh 123 Darul Fikri, Bairut.
[4] Sahihu Turmuzi  j 5 sh 328, Hadisi na 3874 darul Fikr Bairut 1403.
[5] Musnadi Ahmad dan Hanbal j 3 sh 14, 17, 26, 59, j 4 shafi 371 darul sadirat, bairut sahihu buhari da hadissin sakalaini tambaya ta 6921.
[6] Nhshaburi Muhammad  dan Abdullah , Mustadrak ala assahihaini . j 1 sh 172, darul kutubu al-ilmiyya abairut, 1411.
[7]  Domin samun Karin bayani a koma wa jigo: ≪hakikanin abu huraira a mahangar sahabbai tambaya ta 973≫.
[8] Ahmad dan hammabali, munadi Ahmad hadisi 11135, maktabatu al- shamila.
[9] Adreshin da ya gabata hadisi na 18464.
[10]  Adreshin da ya gabata hadisi na 20596.
[11]  A kama wa jigo kibantuwar Ahlulbaiti da ma’abota bargo tamabaya ta 159 Ahlulbaiti a ayar tsaki tambaya ta 132.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa