Please Wait
Dubawa
12734
12734
Ranar Isar da Sako:
2018/07/07
Takaitacciyar Tambaya
Salmanul farisi da Ammar dan Yasir a lokacin halifancin Umar sun karbi makamin gomnoni, idan har Umar ya kasance wanda ya yi ridda kuma shi azzalumi ne a mahangarsu, to me yasa suka karbi wannan matsayin a lokacin da yake mulki?
SWALI
Salmanul farisi ya kasance gomnan Mada’in a lokacin halifancin Umar kuma Ammar dan Yasir ya kasance gomnan kufa, wadannan mutane guda biyu sun kasance daga cikin Shi’ar Imam Ali (a.s), don haka idan har ya kasance a mahangarsu cewa Umar murtaddi ne kuma azzalumi ne, don me zasu karbi mukami a lokacinsa tun da ba zai taba yiyuwa su zama matemaka ga azzalumai ba, kuma a bisa wannan Allah Ta”ala yana cewa:
"وَلا تَرْکَنُوا إِلَى الَّذِینَ ظَلَمُوا فَتَمَسَّکُمُ النَّارُ". (هود، 113).
“kada ku karkata zuwa wadanda suka azzaluma sai hakan ya sa wuta ta shafe ku, (surar Hudu aya ta 113)?.
Amsa a Dunkule
A bisa la’akari da bayanai masu zuwa zamu bayanin kuma mu bada amsa kan ma’anar mabiya:-
- Duk da cewa Shi”a na da tsokaci kan halifofi, amma ba su dauke su a matsayin wadanda suka yi ridda ba, kuma tare cewa ya zo a wasu ruwayoyi na ahlussanna, cewa lalle sahabbai Manzon Allah (s.a.w) sun yi ridda, sai dai wannan riddar ba ta dauke da ma’anar irin ridda da aka sani a shari’a.
- “Rukuni” wato jingina, kalma ce da daka ciro ta daga sigar “rakun” wato ginshiki wanda yake nifin wasu turaku da suke sa bango ko garun gida ko wani abu ya tsayu kyam, don haka wannan yana nunin cewa Kalmar an dauke da ma’anar dogaro da jingina da wani abu, kuma ya zama lalle a gane cewa jingina ba ta nufi zallar jingina da wani abu, balle ma hakika tana nifin jinginar da ke hade da karkatar ra’ayi zuwa ga wani abu.
Kuma abin da ake nufi da wadandu suka yi zalunci shi ne, dukkanin wadanda suke da hannu wajen kawo barna da zaluntar bayin Allah Ta”ala, kuma wadannan da suka mai da bayin Allah Ta”ala tankar bayi a gare su.
- Shi”a sun yi imani da cewa a ko wane hali bai halatta mutun ya yi tarayya da azzalumai wajen zaluncinsu da danniyarsa ba, kuma bai halatta a karbi gudun mawa daga gare su ba, haka ma bai halatta a karkata zuwa gare su ba, amma ya hallata ayi aiki da su ta bangare wani aiki na gari ko abu mai kyau bisa sharadi na daban, za a iya yin aiki a karkashin hukumar dagutanci ba tare da an yi tarayya a cikin zaluncinta ba, ta yadda mutum zai kasance yana yin ayyuka na gari yana temakawa mutane, kuma da sannu za a fayyace jawabi kan wannan lamarin a karkashin jawabi filla-filla.
- Yana da kyau ka sani cewa yanayin rayuwa da zamantakewa a kwanakin musulunci na farko, ya kacance wani yanayi ne na daban, musuluncin abin kauna ya kasance farkon kafawa, kuma ya kasance yana kewaye da hadarin makiya na cikin gida da na waje. Bisa wadannan yanayoyin tare da kokarin kare musulunci da temakawa wajen ci gaban sa da fadadarsa, ba wani abu da zai hana Imam Ali (a.s) wanda yake shi ma’asumi ne ya zama ya yi aiki hannun da hannu da halifofi, kuma Salman da Ammar ma sun karbi wannan aikin na shugabancin Mada’un da Kufa ne bisa umarnin Imam Ali (a.s).
Amsa Dalla-dalla
Donim samun cikakken sakamako da gamsashshiyar amsa ya zama lalle mu sa wasa masa’aloli a faifan bincike kamar haka:-
Shin ‘yan Shi”a sun yi yarda da cewa sahabbai sun yi ridda?
Menenne ma’anar karkata ga zalunci a ayar da ta gabata?
Shin yin aiki a karkashin hukumar zalunci be halatta ba ta kowane hali?
Kuma shin yin aiki ko karbar mukami a karkashi wata hukama na nufin karfaffawa da goyen bayan wannan shugaban?

- Shin ‘yan Shi”a sun yi yarda da cewa sahabbai sun yi ridda?
Tare da cewa Shi”a na da tsokaci da yawa dangane da halifofi sai dai ba sa ganinsu a matsayin murtaddai kuma duk da cewa a wasu daga cikin ruwayoyin Ahlussunna an jigana wa sahabban Manzon Allah (s.a.w) yin ridda sai dai wannan ba ridda ce irin ta asali ba (wacce ke nufin fita daga musulunci). [1]
Ma’aunin da Shi”a take amfani da she a wajen daukar matsaya kan halilfofi, shi ne irin matsayin da Imamai (a.s) suka dauka a ma’amalar su da su musamman ma Imam Ali (a.s), ba magangunaun mutane game gari ba, don me kuwa, alhali Shi”a na hakika su ne wadanda suke bin Imamai (a.s) sau da kafa. [2]
Kuma abin da ya fi komai muhimmanci wajen Imam Ali (a.s) da sauran Imamai (a.s) wanda suke la’akari da shi sosai kuma suka sadaukar da rayuwar su a kan sa, shi ne kiyaye asasin musulunci, saboda haka ne Imam Ali (a.s) bai taba kyamatar mika hannun gudun mawa wajen yin aiki tare da halifofi ba domin wanzuwar asalin musulunci, kuma a lokacin da suka nemi shawarar sa ya kasance mafificin mai ba da shawara a gare su, kuma a lokuta da yawa ya sha aika ‘ya’yansa fagen fama a karkashin jagorancin halifofi. Saboda me sayyadi Imam (a.s) bai nemi wani abu ga kansa ba? saboda shi duk abi da yake bukata ya kasance saboda musulunce ne kawai, kuma tun da Abubakar da Umar sun kasnace kan kujerar jagorancin al’ummar musulmai kuma yin fito na fito da su a wannan lokacin mai hadari da musulunci ya kasance yana yaduwa kuma yana kewaye da hadarin manyan daulolin zamanin musamman ma dauloli mafi girman dauloli Iran kasar farisa da Rumawa, bisa kaifin basirar da Imam Ali (a.s) yake da ita, ta hanyar daukar wannan matsayin sai ya zama ya yanke wa dukkanin makiya musulunci kauna daga cutar da musuluncin.[3]

- Ma’anar karkata da jinginuwa a aya mai girma da ta gabata:- “kar ku karkata zuwa ga azzalumai domin hakan zai sa wuta ta shafe ku kuma a wannan lokacin ba kubda wani majibinciin lamari kuma ba ku da matemaki in ba Allah Ta”ala ba” [4] shin me wannan ayar take nufi?
- Kalmar “rukun’ ta samo asali ne daga jingina da ma’anar ginshiki hakama tunba ko katankar da gini ko wani abu tsaya a samansa ko ya dogara da shi, don haka ma’anar ta tana nifin jingina da dogara da wani abu. [5]
- Wadanda suka yi zalunci ma ma’anar ta ta game dakakin wadanda suka yi zalunci da fasadi wajen cutar da bayin Allah Ta”ala suka mayar da su bayinsu kuma suka yi amfani da rayuwarsu da karfinsu don anfanin kashin kansu. [6]
Amma yana da kyau a kula da wannan nukutar cewa karkata a nan ba ta nufin jingina kadai ba, ballamtana ma abin da take nufi shi ne jinginar da ke tare da karkatar ra’ayi, kuma wannan ne ma ya sa harafin “ila” ba ta zo da harafin “ala” ba. kuma fassarar da masana lugga suka yi wa wannnan ayar, [7] tafsiri na da ma’ana mafi gamewa, kuma yin hakan a kan kansa ita ce hanyar da masana lugga ke bi wajen fassara aya.
Bisa wannan karkata zuwa ga azzalumai - wanda ya za a cikin wannan ayar - wani nau’i ne na karkata da ke tattare ta karkatar da kuma son hakan har zuciya, daidai ne wannan jinginar ta kasance a cikin lamarin addini ne ko kamar idan suka zama suna yin wasa da addin ko suna yi masa zagon kasa, idan ya zama abin da zai afmafane su ne sai su fade shi, idan kuma ya zama lamarin da zasu cuto da fadar sa ne sai su boye shi su ki yada shi, ko kuma ya kasance a cikin rayuwar addini ne, kamar su rika bawa zzalumai damar su rika mulkar mutane bisa yadda ran su yake so a wajen gudanar da lamarin al’umma suna yin amfani da addini don su samu biyayyar dukkanin mutane. Ko kuma ya zama suna son shugaba azzalumi kuma son da su ke masa sai ya zama dalilin cakudar wannan da lamarin addini, kuma daga karshe sai hakan ya zama dalilin da zai jawo munanan abubuwa a cikin rayuwar mutane.
Da ga wannan bagaren ne, ya zama cewa: yin hani kan jingina zuwa ga azzalumai a wajen yin mu’amala da su da kuma siye da siyarwa, haka ma samun nutsuwa da su da kuma amintawa da su a cikin wasu abubuwa, dukkanin wadannan abubuwan ba sa daga abubuwan da aya mai girma ta yi magana a kansu, hakkia mu ga shi kansa Manzon Allah (s.a.w) a daren ya yi nufin yin haijara zuwa madina a lokacin da ya doshin inda kogon hira’i yake ya hayi abin hawan da zai je madina a kan sa a wajen wani amintaccen mushriki wanda aka san shi da amana, kuma Manzo (s.a.w) ma ya aminta da shi kuma sun kulla yarjejejniya kan cewa bayan kwana uku zai kawo masa abin hawa har kofar kogon hira, kuma su ma musulmai sun yi irin wannan mu’amalar da mushrika a gaban idon Manzon Allah (s.a.w). [8]
Bisa wannan asasin Shi”a sun yi imani da cewa a matakin farko bai halatta mutun ya yi tarayya a cikin zalunci azzalumai ba kuma bai halarta ya nemi temakonsu ba a mataki na biyu idan jingina da su ya zama dalilin da zai kai ga raunana da rashin karfin al’umma musalama da rashin samun ‘yancin, kai da rashin dogaro da kai, har su wayi gari sun zama wata al’umma mara galihu wacce ba ta iya tabuka komai, don haka ya zama wajibi a sha kan irin wannan yanayin wanda ba wani sakamako da zai jawo wa al’ummar musulmai face sai rushewa da rashin katabus da kuma rauni. [9]
I mana, wasu ruwayoyi sun zo a cikin litattafan Ahlussunna da suke lazimta mika wuya ga sarakunan da suke mulki a zamaninsu a matsayinsa na majibinta al’amari, ko waye shi kuwa, misali: ya zo a hadisin da - wai aka ce - an cirato daga Annabi (s.a.w) yake cewa: wajibi ne ku yi sarki biyayya ko da kuwa ya kwace muku dukiya koda kuwa sun doke ku! Haka ma a wasu ruwayoyi an nakalto wajabcin yin biyayya ga majibincin lamari da ma’ana mai fadin gaske. [10]

- Shin halarcin karbar mukami ko ka a ce yin aiki a karkashin hukumar azzalumi bisa saki ba kaidi ne?
Da yake an yi mayanin ma’anar wannan ayar a sarari kan cewa abin da ake nufi da karkata zuwa ga azzalumai shi ne dogaro da shi tare da son hakan a zuci.
Amma karbar matsayi a cikin hukomomin azzalumai ba a kallonsa da wannan mahangar a ko da yaushe kuma hakan ba zai zama haramun ba, kuma karbar wannan aikin zai iya zama yana da manufofi masu yawa:

- Domin kara wa hukumar azzalumi karfi.
- Domin yada barna.
- Don neman duniya da maka.............
Idan shigar wani mutum ko karbar aikinsa a cikin wata hukuma ya zama da daya daga cikin wadannan masufofin ne ta lalle aikin sa ya munana kuma abin da ya yi haramun ne.
Duk da cewa yin aiki a karkashin wata huma wani nau’I ne na temaka mata da karfafata ta yadda mafi karfin abin da za a iya sauwarawa shi ne mutum ya kara karfafa tsayuwar ta ta hanyar karbar aikin da ya yi, amma bisa kallon wasu abubuwa ya zama dole a samu wasu daidaikun mutane masu manufa ta gari a cikin hukumomin azzalumai, tabbas kimar su da matsayinsu ya tsaya ne kan sabanin manufar da suke da ita da gungun jama’a ta farko bisa karbar aiki. Bisa wannan asasin aka samar da hukunce-hukunce na musamman ga irin wadannan mutanen da suka saba da na gungun farko, kuma wannan na da alaka da mihimmancin halartar mutum irin wadannan wuraren ayyukan kuma lamarin na da wani matsayi irin na sa ta yanda karbar aikin zai iya zama halal ko mustahabbu ko ma ya zama wajibi.
Ya zo a littafin wasa’ilsh Shi”a a wani babi mai taken: “babin halarcin karbar aiki a hannun sarki azzalumi domin temakawa muminai da kawar musu da cutuwa da yin aiki da gaskiya idan an sami damar haka. [11]
A wannan babin an kawo ruwayoyi da dama da suke yin nuni kan halascin karbar aiki a hannun sarki azzalumi; bisa misali zamu ambaci wasu daga cikinsu:-

- An karbo daga Ali dan Yakdinu (wazirin Haruna Rashid Halifan Abbasawa): an nakalto cewa ya ce: Imam Musa Alkazim ya gaya min: Allah Ta”ala yana da wasu mutane da suke gefen sarakuna wadanda suke kare masoya Allah Ta”ala (muninai) daga munanan abubuwa. [12]
- Haka ma yana cewa: wadannan su ne ‘yantattun Allah Ta”ala daga wuta. [13]
- Imam Sadik yana cewa: ramuwar hidimtawa Sarki ita ce kyautatawa ‘yan uwa. [14]
Ya zo a cikin kurbin isnadi da sanadi zuwa Ali dan Yakanin yana cewa da Imam Kazim zuciya ta na kuna matuka kan hidimar da na ke yiwa sarki, da zaka yi mini izini da na zan guje wa mukami na, sai Imam (a.s) ya ba shi amsa da cewa ba zan ba ka izini ka bar aikinka ba, ka sa tsaron Allah Ta”ala cikin lamarinka. [15]
A wasu ruwayoyi masu yawa da muke karanta wa daga Imamai (a.s) baya ga Ali dan yakdin sun bawa suwa daga cikin makusantansu irin wannan halasci. [16]
A ko wane hali karbar irin wannan matsayi da rashin karbarsa yana danfare a karkashin dokokin abu mai mihimmanci da kuma abu mafi mihimmanci. Kuma ya zama lallai a auna tsakanin amfaninsa da rashin sa a mahangar addini da ta al’ada.
Don haka karbar mastayi a hukumar sarki azzalumi zai iya zama da kyakkyawar manufa kuma yana da tasiri mai yawan gaske.
Ga wasu daga cikin manufofin kyawawa wadanda suka hada da:-
A wasu lokuta, mutum kan sami kan sa a wani yanayi, bisa dalilan rinjayar (da abin da ya fi zama maslaha) sai ya zabi abin da ya saba da son zuciyar sa kuma ya jefa kansa cikin hadarurruka masu yawa ya kama aiki a cikin hukumar azzalumai wanda da sannu zamu yi nuni zuwa wasu daga irin wadannan yanayoyin.

- Kyautatawa ‘yan’uwa na addini
Bandar dan Asim yana cewa Imam Musa dan Ja’afa (a.s) ya kasance yana cewa da Ali dan Yakdin wanda ya kasance wazirin Harunar Rashid: “ ya kai Ali ka yi mana lamunin abu daya ni kuma zan lamince maka siffofi guda uku, ka yi alkawarin cewa duk wani masoyin mu da ka gani zama girmama shi, ni kuma zan lamince maka abubuwan nan uku, kaifin takobi, azabar kurkuku da kaskancin talauci, har abada wadannan abubuwan uku ba za su taba cinma ka ba” tun daga wannan lokacin duk sa’adda Ali dan Yakdin ya ga masoya alayen Annabi (s.a.w) sai ya yi kasa-kasa da fuskarsa. [17]
- Yiwa nutane hudima:
A wasu ruwayoyi da aka karbo daga Imam Ridha ya zo cewa: Yusif (a.s) ya tara alkama a shekaru bakwai na farko, ya sakaya su a cikin runbunan ajiya, kuma a shekaru bakwai din da suka biyo na fari, ya fara raba alkmaa a lissafe da bin diddigi wajen lissafi ya fito da ita yana rabawa mutane domiin su gudanar da rayuwar su ta yau da gobe tare da kiyaye amana ya iya tseratar da mutanen Misra daga halaka, Annabi Yusif (a.s) a shekara bakwai bin fari bai taba cika cikinsa ba don kar ya manta - Allah Ta”ala ya yi masa tsari - masu fama da yunwa. [18]
- Don rage kaifin azzalunci azzalumai da kuma shiryar da azzaluman mahukunta.
A cikin tafsirin Mujma’ul bayan da na Almizan sun yi nuni kan abin da Annabi Yusif (a.s) ya aikata a lokacin (fari) kamar haka:- a lokacin da shekarun fari suka shigo, a wannan shekarun Annabi yufis (a.s) ya rika siyir da alkama da zinare da azurfa da jauhari da kayan ado (sarka da dan kunne dss) da dabbobi da bayi da gidaje da gonaki, haka ya yi mu’amala da mutane. A lokacin da fari ya zo karshe sai ya ce da sarkin misra dukkanin mutane tare da dukiyar da suke da sun wayi gari a karkashin ikona, amma Allah Ta”ala ya sheda da cewa kuma kai ma ka zama sheda kan cewa dukkanin mutane sun wayi gari cikin ‘yanci kuma zan mayar musu da dukkanin dukiyoyinsu, sannan zan mayar musu da manyan gidajensu da ma kananan gidaje da stamp da takardun su na abububwan da suka mallaka duk zan hada in mayar musu. Mulki a waje na hanya ce ta kubutar da al’umma kawai ba wani abu na daban ba, kai ma ka yi musu adalci a cikin dukkanin lamura. [19]
Wasa daga cikin fa’idojin shiga hukumar azzalumai ya hada da:-

- Watakila wanda ya karbi wannan matsayin da ga karshe zai kai ga tunbuke hannun azzalumi (kamar yadda ya faru daidai fadin wasu ruwayoyi dangane da yaruwar Annabi Yusif (a.s).
- Wani lokaci hakan kan zama tushe na dalilin samun juyin juya hali da kuma yinkurin kawo canji daga baya don me kuwa alhali zai samar da shimfiidar da ta kai ga samar da sabuwar hukuma (ta yiyu muminu Ali Fir”auna ya zama daya daga cikin wadannan).
- Wani lokaci kuma su kan zama mutanen da za’a rika jingina da su su zama mafaka ga wadanda ake zalunta da raunanan kuma su rika rage kaifin zaluncin na sama a kan talakawa.
Wadannan lamura ne da ko wane daya daga cikinsu shi kadai ya isa ya zama dalili kan karbar wadannan makuman. [20]
Wani abu la’akari a nan shi ne irin wadannan tambayoyin na da magabaciya dadaddiya, ta yanda wasu mutane jahilai da wasu kuma masu kalubalanta sun yi wa Imam Ridha (a.s) irin wannan kakubalen.
Kamar yadda muka karanta a ruwayoyi da yawa an nakalto hakan a tarihin Imam Ridha (a.s) kamar haka:-
Wasu masu kalo bale daga cikin mutane sun yi wa Imam nakadi da cewa ta yaya a ka yi tare duk wannan gudun duniyar da kake da shi da rashin damuwa da duniya kuma ka karbin matsayin mai jiran gadon Mu’amun? A wajen bada amsa Imam (a.s) ya ce: shin Annabi (s.a.w) ne ya fi fifici ko kuma magajin (wasiyyin) Annabi? Sai suka bada amsa da cewa Annabi mana. Sai ya tambaye su shin musulmi ne ya fi fifiko ko mushriki? Sai suka ba da amsa da cewa musulmi ne ya fi, sai ya ce azizu misra ya kasance mushriki Yusif (a.s) kuma Annabi ne, shi kuma Mamun musulmi ne ni kuma wasiyyim Annabi (s.a.w) ne, kuma Yusif (a.s) ne ya nemi azizu misra ya ba shi mukamin kwamishinan gona da ajiya sannan ya ce ni mai kiyaye wa ne amintace, alhali ni tilasta min karbar wannan matsayin aka yi. [21]

- Shin yin aiki a ko karbar mukami a karkashi wata hukama na nufin karfaffa da goyen bayan wannan shugaban?
Bisa ga bayanin da ya gabata ya bayyana a sarari cewa ba haka lamarin yake ba a ce a ko da yaushe yin aiki ko a ce karbar matsayi a wata gwamnati yin hakan na nufin karfafa wa ne ga ita hukumar da mai shugabanta ta ba.
Bisa la’akari da sharadan na musammana din da musulunci ya sami kansa a ciki, a kwanakin farkon na samuwar musum, ya kasance yana kewaye da makaiya na ciki dana waje kuma domin kokarin samar wa musulunci gindin zama da kansa zamu iya fsukantar dalilin da ya sa Salman da Ammar suka karbi matsayi a cikin gwamnati da ma abin da ya fi haka na hada hannu na kukasa-kusa da Imam Ali ya yi da hallifofi. Da wani yaren, irin wannan yanayin na musamman tare da burin kiyaye samuwar musulunci da temakawa wajen kafuwar sa da yaduwansa, ba abin da zai hana Ali (a.s) a matsayin sa na mai ba da shawara ma’asumi ya hada guiwa da halifofi. [22] kuma Salman da Ammar a karkashin umarnin Ali (a.s)[23] su zama sun karbi mukamin gomnonin Mada’in da Kufa.

[1] Don samun karin bayani a komawa amsosshin da aka bayan a sate (sait) (yanar gizo) 1589 (sait 1970) da 2799 (sait 3502) da 2805 (sait 3562) da kuma 2807 (sait 3501).
[2] Domin samun karin bayani a koma wa tambaya mai mai lamba 1015 (sait 1167).
[3] An cirato daga jigo mai numba 1348 (sait 2982).
[4] Surau hudu aya ta 113.
[5] Makarim shirazi, nasir tafsirul amsal j 9 shafi na 260, Darul kutubul islamiyya, Tahran, shekara ta 1374 hijiri shamsi, bugu na daya.
[6] Tafsirul amsal j 9 shafin ana 263 (an takaice bayanin).
[7] Mufaradat din ragib Kalmar rukuni.
[8] Daba’daba’I Muhammad Husain a cikin almizan, musawi hamdani sayyid Muhammad bakir tarjamar almizan j 11 shafi na 68-75, daftari intisharat islami jami’ahtul madrasataini, hauzar ilimi Kom, Shekara 1374 HSH.bugu na biyar.
[9] Tafsirul amsal j 9 shafin ana 261.
[10] Tafsirul amsal j 9 shafin ana 264.
[11] Wasa’ilu Shi”a na Hurrul Amuli, j 17 shafi na 192, mu’saaar Ahlulbait (a.s) Kom, shekara ta 1409 H.K.
[12] Wasa’ilu Shi”a j 17 shafi na 22326.
[13] Wasa’ilu Shi”a j 17 shafi na 22327.
[14] Jafar Bahzade, shafi na 387, nashiru islamiyya, Tehran, 1380, shekara ta 1380. Bugu na daya.
[15] Majlisi Biharul anwar, adabul mu’ashra, tarjamar mujalladi na sha shida Biharul anwar j 2 shafi na 234, kamrahi, Muhammad Bakir, nashir islamiyyam Tehran, shekara ta 1364,H.SH. bugu na daya.
[16] Tafsirul amsal j 10 shafi na 7 da na 8.
[17] Al-adabul diniyya lil khaza’inul mu’ayyaniyya, tarjamar abidi. Shafi na 365.
[18] Muhsin kira’ati tafsir nur j 6 shafi na 105, markazu farhangi darsaha az kar’an, Tehran, shekara ta 1383H.SH. bugu na sha daya.
[19] Adreshin da ya gaba ta j 6 shafi na 105, da na 106 (da bayani a takaice).
[20] Tafsirul amsal j 10 shafi na 7 da na 8.
[21] Wasa’ilish Shi”a j 12 shafi na 146.
[22]
Saboda haka ne ma shugaban munina Ali (a.s) yake cewa: da sannu zan sarayar da nawa hakkin mutukar lamarum musulmai ya tafi daidai don ka da lamarin su ya tarwatse kuma ba wanda aka aka zalunta in ban i ba” Nahjul balaga, tarjamar dashti, Muhammad khudhuba ta 74, shafi na 122 da na 123. Ibni abul hadid j 6 shafi na 166, subhi salih, shafi na 102.

[23] La’akari da sallawar wadannan manyan mutanen biyu suke da ita dangane da Imam Ali (a.s) da kuma I’itikadinsu da ma’asumancinsa, abu ne mai wahalar gaske ace sun karbi wannan matsayin nmai girma wanda ya kai matsayin gomna jiha baki daya ba tare da sun nemi izininsa ba.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga