Please Wait
16119
Hakika ita alaka ko daggantaka ta kasu kasu biyu, alakar ALLAH da mu da kuma alakar mu da ALLAH, to alakar mu da ALLAH na iya samun rauni, amma raunin yana faruwa ne daga bangare mu zai wuya alakar tamu da ALLAH ta yanke baki daya. Sai dai cewa ita alakar ALLAH da mu wanzajjiya ce ko tabbatacciya, “shi ALLAH ko da yaushe yana tare da ku a duk inda kuka kasance”[1] wannan shi ne ma'anar abin da yake cewa a cikin al-kur'ani “wato shi ALLAH yana tare da ku a duk inda kuke” sabo da haka idan alakar mu da ALLAH ta yi rauni ba makawa da mu yi bncike domin mu gano domin gano dalilin da ya kawo nakasu da kuskuren da ke tare da mu domin a san hanyar da tad a ce a magance su.
Kamar yadda aka ce hanyar lazimtar abu ga dan Adam, ita ce ci gaba da alaka mai yawa tare da wannan abin da yake so ya lazimta wannan shi ne wani abu da ilmi na ran dan Adam “ilmin nafs” ya tabbatar da shi kuma aka yi la'akari da shi cewa wani abu ne tabbatacce ba zai yiwu ba a yi inkarin shi ba. sabo da haka ba makawa samun yi bincike daggane da dalilin da yake nesanta mu da ALLAH, kamar girman kai da hassada da isa da wadata da sauran laifufuka wadanda dan Adam yake aikatawa wadanda suke sakamako ne na tunanin shi, abin nufi su wadannan laifufukan suna haifar da matsala a cikin ran dan Adam sannann akwai laifufuka na waji ko wadanda dan Adam yake aikata su da gabban jikin shi, wadannan laifufukan su ne suke zame mana shamaki tsakaninmu da ALLAH.
Ba mamaki yazamo abin da kuka ambata a cikin tambayar data gabata ya zamo gaskiya cewa tunaninnikamu wadanna munana su ne sababi da dalili na raunin alakar mu da ALLAH. sabo da duk wani aiki da dan Adam yake aikatawa zaka samu asalin shi daga tunani ne na dan Adam. koma da wata ma'anar tunani shi ne tushe da asali na kowa na aiki. sabo da haka ba makawa abu na farko da zamu yi shi ne mu fara tsarkake tunanin mu da zuciyarmu daga duk tunaninnika munana. duk da cewa yin haka yana da mutukar wahala, sai dai sakamakon hakan yana da mutukar fa'ida da muhimmanci.
Sannan tunaninnika wadanda suke zuwa ga mutum wasu tunaninnika ne na shedan sabo da haka dole ne amagancesu cikin gaggawa kafin mutum ya kai ga yin amfani da su, kamar yadda ALLAH yake cewa a cikin al-kur'ani shi mai girma “hakika shaidanu suna wahayi ko suna rudar mabiyansu”[2] sabo da haka dolane adauki matakin magance tunaninnika na shedan.
Hakika daya daga cikin abubuwan da suke nesanta dan Adam da ALLAH madaukaki wanda yake kai shi da ya shagala, su ne tunaninnika munana.[3] wani lokacin tunaninnika na shedan suna yin nasara a kandan Adam ta yarda har lokacin da yake bauta, kamar a salla misali, zaka gan shi yana salla amma hankalin shi yana waniwaje wani, shi ne abin da ake kira da rashin nutsuwa yayin salla.
Sabo da haka ba makawa sai'ammagance wadannan tunaninnika da a hanasu ci gaba da habbaka da a hanasu wazuwa a cikin tunanin dan Adam, hakika wadanna tunaninnika suna farawane da matakai daya bayan daya, misali magana sannan saurare sannan halartar gurin su sannan karanta jaridu wadanda suka shafi gurbatattun tunannika da sauransu, da haka ne da kadan-kadan sai sukafu a cikin tunanin dan Adam, yayin da za su taru su kuma yawaita sai su haifar da shauki, daga karshe sai su zamo hali na dan Adam, bayan haka zai zamo cikin sauki su shiga cikin tunani na mutum sai su wanzu a cikin shi, sai su kai mutum zuwa ga shagala a kan ambaton ALLAH. sabo da haka ne muke ganin mutane masu tunanin abin duniya ba su da tunani sai na jin dadin abin duniya.[4]
Zuwa na shi ne bayani daggane da wannan matsala sai dai dole sai mun yi wani binciken dagane da kashe na biyu, shi ne bayani dangane da yadda za a kubuta daga wannan matsaloli.
Kamar yarda muka fada a bun da ya gabata cewa ba makawa ko dolane amagance munanan tunani da a hana su damar shiga cikin tunani da zuciya. kamar yada yakamata a yi kokare wajin magance ko kore wasu tunaninnika sababbi, kamar yadda al-kur'ani ya nuna hanya domin magance wadanna matsaloli, su ne matakai kamar haka;
Kiwan kashe da kan shi ko kula da kan shi, abin nufi mutum ya yi hattara a kan mu yake yi kuma zai aikata.
Ambatan ALLAH ko da yaushe, nisantar munanan gurare marassa kyau, nisantar wasu abubuwan karantawa da abin ji da wasu daga abubuwan sawa da wasu daga cikin abubuwan ci. lokacin da dan Adam zai rayu yana mai kiyayewa a ko wane lokaci yana kuma mai kiyayewa daggane da wadanna abubuwan masu matsla, to tabbas ambatan ALLAH zai tabbata a cikin zuciyar shi da kadan-kadan sai ya zamo tunaninnika masu kyau iggantattu su maye gurbin munana. sabo da haka ne ya zo a cikin kur'ni mai tsarki cewa “hakika ambatan ALLAH shi ne abu mai magance kuma ya kawo karshen yanayi shagalta daga barin ambatan ALLAH, da kuma kusanta zuwa ga ALLAH mai girma”[5]
ALLAH madaukaki yana cewa “ya ku wanda kuka yi imani ku ambaci ALLAH Ambato mai yawa”.[6] yayin da ambatan abu yake karuwa a cikin zuciya sakamakon haka dangantaka ko alaka tana karuwa ta yadda wannan alakar tana komawa ko canzawa zuwa hali na dan Adam, ta yadda shi dan Adam din zai ga kan sa a cikin masu ambatan ALLAH da salla a ko da yaushe.
Sabo da haka ambatan ALLAH, da yin nasara a kan tunani ko a kanmashiga ta tunaninnika munana yin hakan yana kawo tsarkin zuciya da samar da yanayi domin tabbatar da tunaninnika na abin da ya shafi ALLAH da rahamar shi.
Dolane anan mu yi nuni ga wani abu wanda yake da muhimmanci shi ne mutum ya zamo yana da tunaninnika munana ko yin tunanisu wani bala'I ne ko jarrabawacce ta ALLAH mai girma ga dan Adam kila tayiyuma sharar fagene na sanin ALLAH ko samun alaka da shi, hakika aya mai girma ta yi nuni da hakaninda ALLAH mai girma yake cewa ““hakika wadanda sukaji tsoran ALLAH yayin da wasu daga cikin shedanu suke shafe su domin haifar musu da munanan tunani suna tunawa cewa wannan aiki ne ko tunani na shedan”.[7]
Ya zo a cikin wata ruwaya da aka rawaito daga Abi Abdillah amincin ALLAH yatabata agare shi ya ce “wani mutum ya taba zuwa gurin annabi Muhammad tsira da amincin ALLAH su tabbata a gare shi, sai mutuman ya ce ya ma'aikin ALLAH na halaka! Sai annabi tsira da amincin Allah ua kara tabbata a gare shi ya ce mishi wani mummunan abu ne ya same ka abin nufi “shedan ne ya zomaka ya ce maka wanene ya halicceka? Sai kace masa ALLAH ne sai ya ce maka ALLAH wane ne ya halicce shi? Sai mutuman ya ce a narantse da wanda ya aikoka ko ya turuka da gaskiya haka ne abin da ya faru. Sai annabin ALLAH tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya ce wannan wallahi shi ne tsantsar ko cikakken imani.[8]
[1] Al hadi 4
[2] Saratul an’am 121.
[3] Jawado amulli , abdullahi marhalolin akhlak a cikin al-kur’ani. Shafi na 30.
[4] Jawado amulli , abdullahi marhalolin akhlak a cikin al-kur’ani.shafi na 30.
[5] Jawado amulli , abdullahi marhalolin akhlak a cikin al-kur’ani. Shafi 34 da 35
[6] Surartul Al’ahzab, aya ta 41.
[7] Saratul a’arafi aya ta 201.
[8] Biharul anwar juzu’I na 55 shafi na: 324.