Please Wait
10987
- Shiriki
Fatawa: Ita ce fitar da hukuncin wani lamari a addini ta hanyar koma wa madogarar shari’a da amfanuwa da garesu, ta hanyar da aka san ana fitar da hukuncin.
Hukunci: Shi ne abin da ake zartarwa ta hannun jagoran hukumar musulunci. Jagora zai iya amfana daga dokokin shari’a da tsarin musulunci da lura da zurfafa tunani tare da la’akari da sharudda game da wata mas’ala ta musamman domin ayyana matsayin al’umma ko wasu kungiyoyi, ko wasu jama’a daban.
A mahangar shari’a biyayya ga hukuncin ubangiji da fatawar malami wanda ya cika sharudda, kamar biyayya ga jagora mai jibintar lamarin musulmi wani abu ne na tilas. Sai dai akwai cewa fatawar malami ga malami ko mai koyi da shi wata aba ce da ta zama tilas su bi ta, yayin da game da hukunci ya zama dole ne ga kowa ya yi biyayya ga malami jagoran hukuma.
Yayin da mujtahidi yake komawa zuwa ga madogarar shari’a (littattafan shari’a) domin tsamo hukuncin shari’a na ubangiji kan wata mas’ala ta hanyar amfani da hanyoyin da suke na musamman domin wannan aikin na fitar da hukuncin shari’a, bayan ya fitar da hukuncin sai ya sanya shi hannun masu koyi da shi, to wannan muna kiran shi da sunan “Fatawa”. Don haka ne zamu iya cewa: Fatawa ita ce fitar da hukuncin shari’a a wannan addini ta hanyar koma wa madogara wannan addinin ta hanyar amfani da wasu hanyoyin yin hakan na musamman[1].
A lokacin jagoran musulmi ya fitar da doka kan wata mas’ala kan al’umma, ko wasu kungiyoyi, ko wasu jama’a, yana mai la’akari da dokokin shari’a da tsarin musulunci, da duba mai zurfi da kula da sharudda yanayin wannan mas’ala, to sai mu kira wannan da hukunci. Don haka zamu ga a hukunci ana la’akari da dokoki da al’adun da tunanin duniyar musulmi bisa yanayi da sharudda na musamma, kuma matukar wannan yanayin bai canja ba to wannan yana nan yadda yake gun jagora ko mataimakinsa.
A mahangar shari’a biyayya ga hukuncin ubangiji da fatawar malami wanda ya cika sharudda, kamar biyayya ga jagora mai jibintar lamarin musulmi wani abu ne na tilas. Sai dai akwai cewa fatawar malami ga malami ko mai koyi da shi wata aba ce da ta zama tilas su bi ta, yayin da game da hukunci ya zama dole ne ga kowa ya yi biyayya ga malami jagoran hukuma.
Don Karin Bayani:
1- Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat ba Diyanat, Cibiyar al’adu ta Khaniyye Khirad, Kum, Bugu na biyu, 1380.
[1] Imam Khomain (k.s) yana cewa da wannan hanyar “Ijtihadin Jawahiri” ko “Fikihun Al’ada” (Mahdi Hadawi Tehrani, Fikhu Hukumati ba Hukumate Fikh, game da Risalar wucewar shekara ta biyar da juyayin imam Khomain (k.s), shafi: 10 – 11, watan Khurdad 1373).