Please Wait
9832
Hakika shedan na da zuriya kuma su ma la'anannu ne kamar yadda yake la'ananne, domin su ma bisa hakika sun bi tafarkin sa kuma sun yi riko da hanyarsa da salonsa wajen batarwa da kokarin kautarwa daga tafarkin gaskiya, sun dogara da wannan hanyar a wajen batar da bil'adama da fitar da su daga madaidaiciyar hanya, ta wannan janibin dukkanin su la'anannu ne, sai dai ya zo a wasu riwayoyi cewa shedan din nan da aka wakilta shi a kan halakar da Annabinmu (Muhammad) amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, ya musulunta a hannun mafi girman annabawa amincin Allah ya kara tabbata a gare shi.
Yadda shedan ya ke kamar dai yadda mutum ya ke ne yana da `ya`ya kuma yana da zuriya, kuma ayoyi masu girma da hadisai madaukaka da suka zo ta hanyar ahlul baiti (a.s) sun tabbatar da wannan hakikar, daga ciki akwai fadinsa madaukakain sarki: {ashe kwa rike shi da zuriyarsa majibinta al'amari ba ni ba, alhali su makiya ne a gare ku, tur da sauyin da azzalumai suka zaba wa kansu}.[1] Haka ma allama Majlisi ya rawaito a cikin littafin (assama wal'ardh)- (sama da kasa). A cikin babban littafin nan na sa (Biharul anwar) cewa: Allah ta'ala ya ce da iblis: "ban taba ba dan Adam wani da ba face sai na ba ka makamancinsa, kuma hakika ko wane mutum na da shedani wanda ake haifarsa tare a lokacin haihuwarsa".[2]
Hakika zuriyar shedan kamar dai shedan su ke an halicce su domin halakar da mutane da karkatar da su daga tafarki madaidaici kuma su na bin irin salon da babansu ya bi, saboda haka ne ya tabbata cewa su ma la'anannu ne kamar dai babansu, bisa hakika mafi yawansu da rinjayensu haka su ke kasancewa, in banda sashin daidaikunsu wadanda su ka yi karanci, tamkar shedan din da ya musulunta a hannun manzon rahama tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, Allama Majlisi ya rawaito cewa an tambayi annabi tsira da amincin Allah ya kara tabbata a gare shi sai ya ce: hakika Allah ya temake ni a kan wani shedani har sai da ya musulunta a hannuna.[3]
Daga karshe zamu yi nuni ya zuwa wasu lamura masu mihimmanci:
Hakika lalle ayoyin Kur’ani da suka zo da wasu kalmami makamancin Kalmar "waliyyai"[4] ko Kalmar kabila, kamar yadda yake a fadinsa madaukaki sarki: {hakika shi da kabilarsa suna ganin ku ta inda ba kwa ganin su. Hakika mun sanya shedanu waliyyai ga wadanda ba su yi imani ba}[5] wannan bai game dukkanin mutane ba lalle waliccinsa da rinjayensa da ikonsa wajen batarwa sun tsaya ne a kan wasu daga sasin mutane da kuma sashin ayyuka lalle akwai da yawa daga cikin mutane da kuma da yawa daga cikin wasu ayyuka da shedan ba shi da iko a kansu, ballantana ma ba shi da wata wilaya ta hakika. Allama daba-daba'i yana cewa: amma zuriyarsa da kabilarsa da ambatonsu ya zo a cikin Kur'ani da fadinsa {hakika shi da kabilarsa suna ganin ku ta inda ba kwa ganinsu. Hakika mun sanya shedanu waliyyai ga wadanda ba su yi imani ba}[6] da kuma fadinsa: {shin za ku rike shi shi da zuriyarsa majibinta al'amari}.[7]
Saboda haka yi wa dayan su biyayya ko dai ya zama wasu ne daga cikin mutane ke yi masa ban da wasu, ko kuma a yi masa biyayya a cikin wasu ayyuka ban da wasu, amma biyayya bisa yanayi na temakawa wannan sunan sa temako, kuma babbar manufar da Iblis ke tukewa zuwa gare ta, ita ce batarwa daga tafarki da hallakarwa.[8]
Hakika Ibblis daya ne daga cikin aljanu: {Sai mala'iku suka yi sujjada im ban da iblis ya kasance daga cikin aljanu}.[9] Gama cewa Kur'ani ya tabbatar da samuwar zuriyar shedan, a wani wajen kuma sai ya yi nuni zuwa ga mutuwar aljanu: {Wadannnan su ne wadanda alkawarin narko ya tabbata a kansu a cikin al'ummin da suka shude gabanin su na daga aljanu da mutane, hakika sun kasance hasararru}[10]
Daga nan ne za mu fahimci cewa su ma aljanu suna haihuwa, domin abu ne a bayyane cewa ci gaban samuwar zuriyar da ke fuskantar mutuwa na bukatuwa zuwa haihuwa. Sai dai abin sa ya wanzu boyayye a gare mu shi ne sanin yanayin yadda wannan haihuwar ta ke, shin ta yi kama da yadda dan Adam ke haihuwa ko kuwa? Wannan kam Kur'ani bai yi nuni zuwa gare shi ba.[11]
[1] Surar kahfi a ya ta 50
[2] Tarjamar kitabus sama'I wal alam shafi 243.
[3] Biharul anwar juzi'z na 16 shafi 334.
[4] Surar kahfi aya ta 50.
[5] Surar a'arafi aya ta 27.
[6] Surar a'arafi aya ta 27.
[7] Surar kahfi aya ta 50.
[8] Almizan fi tafsirin kur'an juzu;;I na 12 shafi na 111.
[9] Surar kahfi aya ta 50.
[10] Surau ahkafi aya ta 18.
[11] Ka duba tarjamar al-muzan juzu'I na 12, shafi na 226.