Please Wait
Dubawa
8646
8646
Ranar Isar da Sako:
2016/07/12
Takaitacciyar Tambaya
menene cikakken tarihin rayuwar sahabi hujr dan Adi (rd) wanda kwanakin da suka wuce wahabiya suka aikata ta”addancin tone kabarinsa a kasar siriya?
SWALI

Amsa a Dunkule
Hujr bin Adi Al-kindi; ya na cikin sahabban manzon rahama {s.a.w} sannan bayan wafati ya kasance cikin kebantattun sahabban imam Ali (as) mai cika alkawali, hakika hujr bin adi ya halarci yakokin da imam Ali {as} ya jagoranta bayan wafatin manzon rahama ya kuma taimakawa imam da dukkanin karfinsa. bayan shahadar imam Ali {as} hakika hujr dan adi ya taka muhimmiyar rawa tsakankanin `yan shi”ar kufa ta yanda ya zamanto kayar makogaro ga yaran mu”awiya a wanda ya nada shuwagabanni a wannan yanki sakamakon ita kufa an mika ta hannun yaron mu”awiya zayad dan babansa, bayan matsanancin sabini tsakanin hujr bin adi da zayad dan babansa sai zayad ya sanya aka kama shi ya aika da shi wajen mu”awiya, yayin da aka kai shi sai mu”awiya ya nemi hujr da abokanensa da su barrranta daga imam Ali {as} amma hujr da mutanensa sai suka yi watsi da wannan bukata ta mua”wiya wanda daga karshe ya sanya aka kasha su ta hanyar sare kawukansu.
Amsa Filla-Filla:
Hujr bin adi kindi;[1] galibin malamai masana tarihi sun kidaya shi cikin sahabban manzon Allah {s.a.w}[2] in banda yan tsiraru daga cikin malaman hadisin ahlus sunna da suka sanya shi cikin kason tabi”ai, wanda wannan sabani ya afku sakamakon wasu abubuwa kamar haka: ta kaka sahabi zai kashe sahabi wadanda dukkaninsu adalai ne a akidar ahlus sunna, sannan kuma ya za ai da adalcin mu”awiya gashi kuma ya kashe babban sahabi hujr bin adi kuma kebantaccen sahabin imam Ali {as} mai cika alkawali wanda ya halarci yakokin jamal da siffin da naharawan ya kuma kasance cikin kwamandoji.[3]
An baiwa imam Ali {as} labarin cewa hujr bin adi alkindi da amru bin hamakil kuza”I suna tsinewa mu”awiya a fili kuma suna zagin mutanen sham, sai imam Ali {as} ya aika musu da sako cewa su kauracewa aika hakan, yayin da su ka ji wannan labara sai suka je wajen imam Ali {as} su na masu tambayarsa: ya sarkin muminai ashe mu”awiya ba kan bata ya ke ba mu kuma muna kan shiriya? Sai imam ya ce: ban son ace kun zama mutane masu yawan la”ance la”ance da zage zage. Kamata ya yi ku dinga cewa ya ubangiji ka kiyaye jinanen mu da nasu ka kuma sulhunta tsakanin mu ka shiryar da su daga batan da suke kai ta yadda duk wanda bai son gaskiya ba ya santa, wanda ke kan bata ya dawo shiriya.[4]
Yadda Aka Kama Hujr Dan Adi Da Yadda Ya Yi Shahada:
Daya daga cikin muhimmin abu cikin rayuwar hujr dan adi wanda tarihi ya fi mai da hankali kansa shi ne rawar da ya taka a cikin shi”an kufa lokacin shahadar imam Ali {as} hakika hujr dan Adi ya kasance babbar matsala ga yaran mu”awiya wanda ya nada su a kufa, hujr ya hana ya tsaya kyam ta yanda ya takawa madandanu da surutan Ziyad birki. Zayad ya tafi basara ya nada amru dan haris a kufa sai dai cewa labara ya isa kunnen zayad cewa hujr dan Adi da mutanensa sun yi taro suna barranta da la”antar mu”awiya a fili a bayyane sun kuma jejjefi amru dan haris sai take zayad dan babansa ya tafi kufa ya tara jama”a ya na musu bayani a dai dai lokacin da shi kuma hujr dan Adi na zaune ya kasa kunne ya na saurare har lokcin da ya ji zayad na yi masa barazana ya na cewa idan na samu damar mallakar kufa sai na sanya hujr bin Adi ya zama wa”azi ga ragowar mutane, sai zayad ya sanya aka kawo masa hujr dan Adi shi ko hujr na zaune bai ce masa komai ba, bayan an ja-in-ja da kuma fafatawa sai hujr ya yanke shawarar sulhu da kuma karbar aminci daga zayad don gudun kada su kashe shi, sai suka kama shi suka kai shi wajen mu”awiya, to a nan ne da yawan mutane wadanda cikinsu akwai munzir dan zubairu da umar dan sa”adu dan abi wakas suka ba da shaidar cewar hujr ya tara mutane suna zagin mu”awiya da la”antarsa ya na kuma kiransu da yakar mu”awiya da nuna musu cewa al”amura ba za su taba daidaito ba har sai dan dangin gidan Aliyu dan abi dalib {as} ya hau mulki, sannan kuma suka ce wai shi hujr ya koro gwamnan mu”awiya daga kufa sannan shi ya na ganin an zalunci imam Ali {as} ya na kuma yiwa imam din addu”a da nema masa rahamar ubangiji yana kuma barranta da dukkanin makiyansa da wadanda su ka yake shi.
Daga karshe dai mu”awiya ya nemi hujr dan adi da mutanensa su barranta kawukansu daga wilayar imam Ali {as} sai dai cewa ba su amsa wannan bukata ta mu”awiya ba, sai su ka yi ta yin salloli har zuwa wayewar gari. Bayan da gari yaw aye sai mutanen mu”awiya suka tafi da hujr makasa sai hujr ya yi alwala ya tsaya ya yi sallah bayan ya idar da sallah sai ya ce: idan lamarin ya kasance sabanin abin da ku ke tsammani cewa ina tsoron mutuwa ne to da zan yi salloli da yawa. Ina neman tsarinka daga wannan jarrabawa mutanen kufa na mummunar shaida kan mu, mutanen sham na kashe mu to a dai dai wannan lokaci sai Hadabatu dan fayyaz ya zare takobi ya nufi hujr dan adi sai hujr ya kama kyarma. Sai fayyaz ya cewa hujr kai da kake tsammanin baka tsoron mutuwa to idan haka ne ka barranta daga masoyinka ali ni kuma sai in kyale ka. Sai hujr ya ce masa: ta kaka ba zan ji tsoro ba alhalin ina tsaye tsakanin takobi da likkafani da kabari. Na rantse da Allah duk da cewa ina tsoron mutuwa sai dai cewa har abada ba zan furta Kalmar da za ta fusata ubangiji ba sai suka kashe shi.[5]
Dole ne mu lura da wani abu mai matukar muhimmanci; shi ne cikin masana tarihi an samu ittifaki kan kasantuwar mu”awiya ya ba da umarni kashe hujr ibn Adi a shekara ta 51 bayan hiiba.[6]
Hujr ibn adi ya yi wasiyya kamar haka: kada ko wanke jinin da aka kashe ni daga jikina, ka da ku kwance sasarin da aka daureni, ku binne ni tare da rigar jikina, a haka zamu hadu da mu”awiya ranar kiyama.[7]
Dalilin kashe hujr ibn adi ya jawo wa mu”awiya martani da zarge zarge masu tsanani, da yawan masadir din da suka kawo tattaunawar a”isha da mu”awiya sun kawo cewa ita a”isha ta zargi mu”awiya kan kisan hujr ibn adi.[8] haka cikin tattaunawar mu”awiya da imam Hassan {as} ya tozarta mu”awiya kan wannan kisa na hujr ibn adi.[9]

[1] Dabakatul kubra li ibni sa’ad j6 shafi 241.
[2] Dabakatul kubra li ibni sa’ad j6 shafi 242.
[3] Usudul gaba juz 1 sh 261.
[4] Akhbarul diwal sh 165.
[5] Diwanil mabda wal khabar fi tarikh arab wal barbar. Tarikh ibn kaldun juz sh 15
[6] 2Tarih khalfati ibn kayyad sh 131. Almusannaf juz 2 sh 54
[7] Almusannaf fi ahadis wal asar juz 2 sh 457
[8] Al”isti”ab juz 1 sh 330
[9] Nuzhatul nazir fi jam”I baina ashbah wanna”za”ir sh 82. Al”ihtijaj juz 2 sh 297
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga