Please Wait
13663
Matafiyar shi'a game da abin da ya shafi Imama taken rairayu a matsayin cewa mukami ne kuma baiwace ta Allah Allah madaukakin sarki Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ne kawai yake isar da wannan sakon saboda wajibi ne Imami ya zama ma'asumi (wanda ba ya kuskure) kuma Allah da Annabinsa ne kawai suka san wanda ba ya kuskure, su ne dai har ila yau suka san wanda ya dace da wannan matsayin domin ya hau kujerar wilaya da jagoranci, sai dai wannan matsayin ya dogara a kan amsa kiran Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi a fili, akwai dalilai masu yawa a kan tabbatar da hakan, ga wasu daga cikin dalilan:
- Tabbas Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya isar da sako saboda kafawa mutane hujja don kar nan gaba su ce me yasa baka zabe mu ba kuma ba ka zabi wasun mu ba? Tunda baki dayan sa banda Sayyadi Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ba su amsa kiran Annabi ba ta dadin rai ta kaga basu da damar bijirowa ta kowacce hanya.
- Tabbatar da fifikon Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi tare da bayyana matsayin sa a kan ragowar, har ya zama sananne a wajen kowa cewa shi ne wanda ya tsaya yake kare Annabi lokacin shan wahala da kadaici da taruwar makiya domin kau da Annabi. Waye wanda yake da jarinta da rashin tsoro har ma yake bayyanawa a fili yana goyon bayan Annabi tare da yunkurin taimaka masa tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi a gaban mutane ba wani tsoro.
- Hakika abin da Annabi ya yi yaumul inzar (ranar gargadi) bai zama ba saiu don Annabi ya shirya mas'aloli biyu ga wannan al'umma saboda kar masu neman gaskiya su kasa gane ta, kuma dan su gujewa fadawa cikin bata da sauka daga kan hanya: dayan mas'alolin nan guda biyu shi ne: asalin Imama (wato jagoranci), al'umma idan ba ta da jagora shugaba to fa zata watse ta kuma halaka. Mas'ala ta biyu ita ce samar da fagen da ya dace saboda zukatan su su yadda da Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi.
- Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi haka ne yaumal inzar dan saboda wannan rana ta kasance ta zabin Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi a mamtsayin Halifa tare da karancin shekarun sa, kuma matsayi na Imama matsayi ne wanda Allah ke bada shi, sai dai wajibi ne a sami wata hujja mai gamsarwa wacce za ta yanke duk wani uzuri da wani dalilin da za a yi riko da shi don sabawa tare da watsi da wannan umarnin.
- Hakikanin wannan aikin ya dace da kasancewar mutum yana da zabi a cikin zartar da nauyaye-nauyayen da aka dora masa, kamar yadda matafiyar shi'a ta tafi a kan haka. Wannan al'amarin ya tabbata a fili lokacin da Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kira su zuwa ga Musulunci farkon aiko shi da kuma yaumul inzar (ranar gargadi) sai ga shi kuraishawa bau Hashim suka yi watsi da daukan nauyin kira zuwa ga addinin Allah da zabin su, shi kuma Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi sai ya amince ya karba da zabin sa da son sa duk da cewa komai tun farkon sa sananne ne an rubuta shi a lauhul mahfuz, sai dai mutum fa yana da rawar da zai taka, domin yana da zabi da 'yanci a wajen shirya fagen da ya dace da shiriyar Allah, to fa kamar ayoyin masu yawa suka yi nuni a kan cewa shiriya da bata sun dogara ne a kan ayyukan mutum, kuma ayyukan su ne sharar fage kuma dai su ne suke tabbatar da shiriya ko bata.
- Abubuwan da suka gudana yaumul inzar (ranar gargadi) suna nuni a kan cewa al'ummar Musulunci, tana zabar mutum a bisa asalin 'yanci da zabinsa (saboda ba a yin dole) domin ba za a bijirowa mutum da wani launi-launi na takurawa ba, da kuma yi masa tilas da fifita wata asali, shi dai yadda lamarin yake ana duba cancanta wacce take share fagen iya daukar wannan nauyin wannan dacewar ana gano ta ne ta hanyar ma'aunan da Allah ya bayar ba tare da shigar da tasirin dangantaka ba (kusanci) da daraja (matsayin mutum) da kuma nasaba.
Matafiyar shi'a a cikin Imama (Jagoranci) tana rairayuwa kan cewa Imama matsayi ne wanda Allah ke bayarwa, kuma isar da wannan sakon na Imama ya rataya ne a hannun Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, kuma hakan saboda Imam (jagora) wajibi ne ya zama ma'asumi (wanda ba ya kuskure), Allah da Manzo ne kawai suka san wanda ya cancanci mukamin Isma (rashin kuskure) wanda kuma ya dace har ma yake da yanayin da ya jawo ake kai shi matsayin shugabanci da jagoranci mai girma, sai dai wannan matsayin ya dogara ne a kan amsar kiran Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi tare da sallamawa a fili, yana da sabubba da dalilai ga wasu daga cikin dalilan:
- Hakika Manzon Allah (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya aikata haka ne don kafa hujja a kan mutane, dan kan nan gaba suce dan me baka zabemuba kuma baka zabi wasun mu ba? Kuma duk baki dayan wadanda suke wajen banda Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ba su amsa kiran Annabi saboda haka basu da wata damar bijirowa kowacce iri.
Hakika bai dace ba ga Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ba kuma haka Annabi ya keyi ba don dabi'ar sa ba ce ya bayyana a fili cewa su basu dace da hawa kujerar halifanci ba, sai dai ba makawa zai bayyana hakan ne ta irin yadda aka saba ta hanyar gudanar da wata kudiyya sananniya ta yadda zai bayyana mas'ala mai kunshe da koro wasu fararun abubuwa sai ya kafa hujja kan ingancin ta domin a iya ganewa har ya zamana ta fi fitowa fili fiye da abin da ake iya gani da abin da ake tabawa, nugu da kari tare da gujewa kullaci kai har ma da tsoron kofe (kulle-kulle) wanda ke zukan wasu.
A wannan akwai wasu wurare wadanda ke nuna kissar halifanci ga su,[1] tare da cewa Manzon Allah (SAW0 tun farko ya an wasu ba su da ce da wannan jagorancin ba kuma ba za su iya daukar wannan nauyin ba, kuma ba za su iya fita daga cikin wannan nauyin biyayyar da aka dora musu ba (su bi Imam Ali A.S) kamar yadda ya zo a kissar gazwatul Khandak[2] kowanne sahabi ya kasa bijirowa Ammar bn Abdi Wuddin, Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ne kawai ya iya tunkarar sa a yayin da yake kuri yake tsoratar da Musulmi, bugu da kari haka ma lokacin yakin Khaibara lokacin da Annabi ya aika mutane su je su yaki Kaibara sai dai dukkanin su ba su yi dace ba sai gashi sun gudo ba tare da sun cimma komai ba,[3] kamar haka ne dai Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya aiki wani daga sahabban sa (Abubakar) ya isar da sakon suratu Bara'a sai Annabi ya nemi ya dawo har ma ya cire shi tare da umarnin Allah ya kuma dankawa Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi wanan babban aikin.[4]
- Tabbas aikin da Annabi ya yi a yaumul inzar (ranar gargadi) ya tabbatar da fifikon Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi a kan sauran sahabban, kuma kowa ya san wanda ya tsaya kyam tare da Annabi (SAW0 a lokacin kadaitaka da jarrabawa (wahalhalun da aka sha) ya fuskanci takura mai tsanani daga bangaren makiya da masu sabawa, waye ya ke da wannan sadaukantakar da rashin tsoro har ma ya ke bayyana goyon bayan sa ga Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi a gaban kowa da kowa tare da kare shi ba tsoro ballantana kai kawo. Irin wannan ne abin da ya faru a Khaibara lokacin da Annab (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi) ya ec: "lallai gobe zai bawa wani mara tsoro tuta mai kai hari da gaske ba mai guduwa ba"[5] tare da cewa Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya san irin wannan aikin ba wanda zai iya sai Imam Alis amincin Allah ya kara tabbata a gare shi.
Kamar hake ne abin da ya faru a yakin Khandak yayin da Annabi ya yi musu shimfida tun a farko, bayan nan kuma ya yiwa Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi izinin ya je su kara da Ammar bn Abdi Wuddin dan saboda fifikon Imam Ali ya bayyana a kan ragowar mutane. Saboda cikar wannan fifikon Annabi yake cewa: "Hakika Musulunci ya fito zuwa ga shirka gaba dayan ta".[6] Ko kuma kamar yadda Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yake yi idan zai yi tafiya ya bar madina, yana sanya Imam Ali shi ne halifansa kuma hakan dan ya karfafa fifikon Sayyadi Ali tare da bayyana cancantar sa da dacewar shugabanci, wata rana Annabi ya yi nuni kan haka, wata ran kuma ya bayyana a fili baro-baro. Ba dan Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi haka ba da mafi yawan Musulmi ba za su yadda da fifikon Imam Ali ba a kan sauran sahabban ba, ba kuma za su sallama ba, ballantana su mika wuya ga Imama Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi, musamman idan muka kula da samuwar masu bujirowa da munafukai da kokarin da suke yi a fili da ayyukan da suka yi dan tarwatsa abin da Annabi ya tsara, dan su sami biyan bukatar su da manufofin su marasa kyau.
- Aikin da Annabi tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya yi ranar inzar (ranar gargadi) shinfida ce ta ayyuka biyu a zamantakewar al'umma, kuma suna da gwabi (tasiri) a nan gaba bayan Manzon Allah (SAW0 don saboda kar masu neman gaskiya su fada cikin tarkon (hanyar mara kyau) bata da lalacewa: Mas'alar farko tana cikin asalin Imama da jagoraincin al'ummar Musulmi, dalilin haka saboda idan al'umma ta zama ba jagora (Imami) to al'amarin ai gushe gaba daya, mas'ala ta biyu tana da alaka da shimfidar da ae yi don mutane su yadda da matsayin Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi a cikin al'ummar Musulmi.
- Zai yiwu mu ce yaumul inzar tana nufin mutanen da za su zo nan gaba, dan a matsayin Halifa ta zama sanadin da Annabi ya zabi Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi a matsayin Halifansa kuma ya zama ya sani har ma 'yan baya. Za ka sami jawabi idan mun kaddara tambayar cewa don me Annabi ya zabi Imam Ali tare da kankantar sa? Tare da cewa matsayin Imama matsayi ne wanda Allah ke bayarwa sai dai ba makawa sai an sami wani sababi mai gamsarwa wanda zai yanke duk wata kafa ga masu iya kafa hujja da uzuri ga wadanda suka ki yi masa mubaya'a da masu sabawa, da zaben ya tabbata ba tare da yin shawara ba da tambaya to wannan zia jawo mamaki a wajen dai-daikun mutane a lokacin Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi, yaya za a gabatar da yaro a kan manya? To me kake zato da 'yan baya masu zuwa wadanda ba su riski Annabi ba tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi kuma ba su san sira ta Annabi da tsarin sa ba, ba su da tsinkaye a kan ta'adodi na Annabi (dabi'u) da darajojin sahabban sa na kyawun halayya da gyaran zuciya ba. Saboda haka ba makawa abin ya tabbata ta hanyar tabbatar musu da fifikon Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi tuntuni kuma har ya zuwa yanzu. Idan ba ta irin wannan hanyar ba zai yiwu wasu su dinga kawo hujjoji da dalilai a kan cewa Annabi ya zabi Imam Ali ne saboda wani dalili, kuma zasu iya cewa ba wani dalilin da ke nuni a kan cewa suna ragowar sahabban ba za su iya wannan aikin ba, ko kuma ba wanda yake da irin wannan daraja.
- Hakika abin da Annabi ya yi yaumul inzar ya dace da kasancewar mutum an bashi zabi (ko ya yi mai kyau ko akasinsa) a wajen yin abin da ake dora masa. Kamar yadda matafiyar shi'a tace: shugabannin kuraishawa sun ki amsa kiran Annabi da zabin su.[7] Alhalin nan take Imam Ali amincin Allah ya kara tabbata a gare shi ya yi gaggawar amsa kiran Annabi da zabinsa.[8] Tare da cewawannan abin a rubuce yake a lauhul mahfuz, sai dai mutum yana tare da zabinsa a kowanne lokaci, wannan shike yiwa mutum shimfida wajen samun dacewa da shiriya ko bata kamar yadda ayoyi masu yawa suka nuna cewa shiriya da bata suna tabbatuwa gwargwadon aikin mutum, saboda haka mutum ne ya yiwa kansa shimfida tun a zuciyar sa saboda abu biyu.
- Abin da ya faru yaumul inzar yana bayyana cewa al'ummar Musulmi tana iya zabar mutane, cikin 'yanci ba tare da takurawa ba, ba wani launi daga cikin launin mulkin fin karfi ko danniya ko kuma juyin mulki, hakika a dacewar mutum ita ce ka'idar dora mara nauyin jagoranci, wannan cancanta da dacewar su ne mizani kuma ma'aunin shari'a wajen ayyana shugaba wanda hakan ya yi hannun riga da san kai. Abin da ya fito fili na 'yanci shi ne bada gudunmawar kowa da kowa a cikin matsalolin al'umma tare da yin shawara a wannan fagen, yin shawara yana da karbar wahayi kuma ma'asumi ne, yana da basira mai girma ta tunani mai haske amma duk da haka ya kira Musulmai don ya yi shawara da su kuma su tattauna. Ba makawa sai an yi bayani a nan wajen cewa Annabi (SAW0 bai yi shawara da su ba a cikin asalin hukunce-hukuincen addini, ba shima Annabi hukuncin wahayi yake biu, sai dai yin shawara da musanyan ra'ayi suna kasancewa ne a cikin yanayin gudanar da hukunce-hukunce da kuma dabbaka su, kamar yadda aka yi nuni zuwa ga hakan a cikin littafin Allah mai tsarki.[9]
Hakika Allah ya bada umarnin yin shawara a suratu Ali Imrana saboda shawarwari da aka yi da sahabbai a yakin Uhudu ba ta haifar da natija mai kyau ba, kuma abin ya tabbata a kwakwale cewa abin da ya faru shi ne ya jawo Annabi (SAW0 bai kara yinj shawara ba.[10] Haka nan ma yana daga cikin wuraren da Annabi ya shawarci wasu daga sahabban sa kamar Hubab dan Munzir a yakin Badar.[11]
Neman shawarar mutane yana da manufa da yawa:
- Kusanto da zukatan Musulmai da ra'ayoyinsu, samar da hadin kai da kauna a tsa kanin su.
- Girmama dai-daikun mutane da basu muhimmanci da yi musu shimfidar bubbugar da baiwa da Allah ya yi musu tare da bada gudun mawa, domin shawara tana bayyana baiwar mutane da nuna irin rawar da za su taka.
- A dauki Annabi (SAW0 a matsayin abin koyi a fagen shawara tare da musanyan ra'ayoyi a cikin al'umar Musulmi, kamar yadda ya zo a cikin Kur'ani mai girma:
((لقد كان لكم فى رسول الله أسوة حسنة لمن كان يرجوا الله واليوم الآخر)).
"Tabbas Annabi Shi ne abin koyi ga duk wanda ke son rahamar Allah da kubuta ranar Lahira".[12]
- Kar a danganta samun nasara ko rashin nasara ga wani mutum daya da shigar da al'umar cikin cin nasara da tabewa (rashin nasara).
[1] Balaziniy, Ansabul Ashraf, j1, sh 58, Imama wasiyyar sa sh9: Mas'udiy, Murujuzzahabiy j4, sh 304.
[2] Subhaniy, Ta'afar, Furugun ubdiyat, sh 545, Biharul anwar j2, sh 227.
[3] Tarikhudabariy, j2, sh 300: Ibn Hajar As-kalaniy, Isaba j2, sh 508.
[4] Biharul anwar, j21, sh 266, da abin da ke biya: tafsirul mizan j9, sh 162.
[5] FurFurusuna Ubadiyat, sh 647: Siyra Halabiyya j3, sh 41.
[6] FurFurusuna Ubadiyat, sh 647: Siyra Halabiyya j3, sh 41.
[7] Tarikhuddabariy, j2, sh 63: Siyra Hulabiyya, j2, sh 286; Biharul anwar, j38, Kanzul Ummal, j15, sh 15.
[8] Tarikhuddabariy, j2, sh 63: Siyra Hulabiyya, j2, sh 286; Biharul anwar, j38, Kanzul Ummal, j15, sh 15.
[9] Ali Imrana, 159; Shura, 38; Tafsirul Mizan, j4, sh 70; Majma'ul bayan, karshen ayar, 159 a suratu Ali Imrana.
[10]Addurrul Mansur j2, sh 90-89; Tafsirul mizan, j4, sh 70; Majma'ul bayan karshen aya, 159 Suratu Ali Imrana.
[11] Sahihi Muslim j5, sh 170; Bidaya wannihaya, j3, sh 263.
[12] Ahzab, 21.