Please Wait
9489
Ana amfani da Kalmar 'yanci da ma'anoni daban-daban kamar zabi, barin 'yancin sha'awa da makamantansu, sai dai abin da yake ma'aunin bincikenmu a nan shi ne abin da ake gani a matsayin 'yancin dan Adam, ko kuma 'yancin al'umma a siyasance.
Wasu mutane sun yi shisshigi matuka yayin da suke ganin duk wani iyaka da za a yi wa mutum game da 'yancinsa to takurawa ga dan Adam da kai shi ga tabewa. Su suna yarda da iyakance 'yancin dan Adam ne kawai yayin da wani 'yancin ya hana wani 'yancin. Irin masu wannan ra'ayin sun hada da wasu masana dokoki da hakkokin al'ummu, da kuma wasu kwararrun masana kan siyasar duniya ne.
Wasu mutanen kuma sun takaita matuka yayin da suke ganin cewa mutane suna kama da dabbobi ne masu farata da fikar fada wadanda ci gabban zamaninsu ya kai su zuwa ga lalacewa. Suna ganin dalilin da ya kai ga rayuwar zamani ta dan Adam a al'ummun yau, gyaran dan Adam yaan cikin ajiye 'yancinsa a gefe guda ne da karbar ikon kasa a kansa kai tsaye.
Mahangar masanan yammacin duniya game da 'yancin dan Adam duk da kuwa suan da sabani mai yawa bisa madogara da asasinsu, sai dai dukkansu suna ganin cewa kafa doka wani abu ne da yake hakkin dan Adam.
Sai dai a mahangar siyasar musulunci duka biyu ba daidai ba ne. musulucni yana ganin cewa mutum yana da halitta ce mai karkata zuwa ga ubangiji da kuma wata halitta mai karkata zuwa ga rayuwar duniya wanda shi ne bangaren bukatunsa na halittar jiki. Don haka sanya doka ga mutum dole ne ya kasnce daga shiriyar ubangiji da wahayin Allah, domin ubangiji ne ya san hakikanin (hanyar) gyara da lalacewar mutum.
'Yanci yana da ma'anoni mabambanta kamar zabi, da kuma sakin mutum kan bin sha'warsa, sai dai mu muna binciken 'yanci ne a mahangar siyasar duniya a yau da zaman rayuwar al'umma. Tambayar asali da ake kawowa a nan shi ne zuwa wane haddi ne gwamnati da doka suke iya haddada 'yancin dan Adam.
Wasu mutaen sun wuce gona da iri wurin bayar da amsar wannan matsala ta yadda suke ganin sanya iyaka ga 'yancin mutum zai kai shi ne ga tabewa kawai. John siturat Mil yana cewa: Duk al'ummar da ta iyakance 'yancin dan Adam, to zata kai ga mutane su koma masu karancin hankali, da karancin jur'a, kai a takaice masu karancin samun yanayin ci gaba[1].
Roso ma yana cewa: Duk wanda ya ki yarda da 'yancin da Adam, to ya yi watsi da 'yanadamtaka ne, kuma ya yi watsi da ayyukan 'yanadamtaka, kuma babu wani abu da zai iya cike gurbin wannan hasara[2].
Irin wadannan masanan suna ganin ana iya yi wa 'yanci iyaka ne kawai yayin da 'yanci ya ci karo da wani 'yancin, wato ta yadda zai kasance 'yancin mutum bai takura ko hana 'yancin wasu mutanen ba.
A cikin wadannan jama'ar akwai masu ganin sanya doka wani hakki ne na mutane, kuma ita gwamnati zata kasance mai gudanar da wannan dokar ce kawai kamar Roso. Amma wasu daga cikinsu kamar John siturat Mil yana ganin tarayya cikin zabe da sanya doka wani hakki ne na mutane na musamman kwararru da masu aiki, da 'yan siyasa wadanda zasu iya binciken lamarin al'umma, kuma su iya gane (abin da zai zama) gyara ko barna a cikin al'umma.
Amma wasu mutanen kuwa kamar Makiawali sai suka takaita yayin da suke ganin mutane kamar wasu dabbobin jeji ne wadanda ci gaban zamaninsu ya kai su ga daidaicewa da lalacewa, don haka ne don haka da za a bar su da 'yancinsu to suna nan dai kan yanayinsu na da wanda shi ne rayuwar dabbobin jeji. Wannan mahanga tasa ta samu karfafuwa daga Tomas Hobaz a Ingila.
Don haka ne a mahangar Hobaz tarayyyar al'umma wani daji ne cikin jeji da yake wani diragon[3] ne mai suna kasa, wanda ya kan kai ga dole ne a samun salladuwa a tafiyar da ita[4]. Don haka ne zamu ga Hobaz yana ganin jagorancin kamakarya daidai ne saboda yana ganin akwai wani sharadin rayuwa da mutane suke imani da shi na cewa sun zartar a zuciyarsu cewa a ba su kariya su kuma su saryar da nasu 'yancin.
A takaice muna iya ganin cewa daga abin da ya gabata masanan yammancin duniya suna da mahanga mabambanta game da ma'anar 'yancin mutum. Idan suka kalli mutum kallon mummunan fata sai su ba shi mahangar Makiawali da Haboz, amma idan suka yi kyakkyawan fata ga dan Adam sai su kalle shi da tunanin nan na John Luck, da john Jeckus Roso.
Sai dai dukkan masanan yammacin duniya duk da dukkan sabanin da suke da shi, sai dai su yi tarayya cikin cewa sanya doka wani hakki ne na mutum.
Sai dai a mahangar musulunci duk da cewa ana ganin mutum a matsayin mai nau'in halittar mai karkata zuwa ga ubangiji da take kiran sa zuwa ga kyawawan alherai[5], sai dai yana da bangaren halittar jiki, wanda yake karkata ga bukatun jiki na rayuwa. Rabautar mutum yana kasancewa cikin galabar nau'in halittarsa a kan halittar jikinsa, sai dai yana da rabo da zai ba wa ita ma bukatar jikinsa.
Ta wani bangaren kuwa ana ganin cewa sanya doka dole ne ya kasance ta hanyar shiriayr Allah madaukaki ta hanyar wahayin ubangiji, domin Allah madaukaki ne masani da yadda za a samu gyara ko bacewar mutum.
Da wannan ne zamu ga cewa mahangar siyasar musulunci ba ta kasance mai wuce gona da iri ba irin ta yammacin duniya da takan iya kaiwa ga lalacewa da fasadi da barna, kuma ba ta kallon mutum da mummunan kallo da zai kai shi ga karbar hukumar tilas babu adalci a hakkinsa wanda yakan kai ga zubewar karamarsa, sai ta mayar da shi kaskantacce wulakantacce maimakon ya kasance mai zabi da daraja mai ikon kansa.
Karin bayani:
1. Mahdi Hadawi Tehrani, Wilayat wa Diyanat, Mu'assar Al'adun Khaneye Khirad, Kum, bugu na biyu, 1380.
[1]. John Estaurat Mil, Risala game da 'yanci, Sheihul Islam, shafi 25, tarjume ba nashre kitab, 1338.
[2]. John Jekues Roso, Karardode Ijtima'I; Shakibafuur.
[3] Lebiatan.
[4]. Mahmud Sana'I, Azadiye fard wa kuadrate daulat, bahasin akidar siyasa da zaman al'ummar Haboz, Luck, Estaurat Mil, da tarjamar Tehran, Sukhan, Faranklin, 1338. Jamal Barut, almujtama'ul madani, s; 14 – 18.
[5]. Fidirar Allah da ya dora mutane a kai: Rum; 30.