Please Wait
10744
Daga cikin Jimillar Akidun Shi’a Imamiyya Isna Ashariyya, shi ne cewa su Imamai Ma’sumai (a.s) ya wajaba su zamo Tsarkakku ne daga Dukkan wasu Sharri, da Sabo.
Abun da aka Ambata kuma a cikin wannan Tambayar babu wata Warwara mai Rusarwa a ciki, babu abin da ya kore wannan Akidar a ciki, saboda ko da mun kau da Kai daga barin Bincika Rauni ko Karfin ita Ruwayar, da farko dai zamu ga ba abin da ake nufi da tsatso masu daukaka da kuma mahaifa tsarkaka wai samuwar su dole ne a cikin dukkan jerin salsala na dangantaka har ma da dangi wadanda ba na asali ba.
Abu na Biyu kuma abin da ake nufi da Tsarki a nan shi ne Tsarki daga Sharrori na Zina, da Kazantar Jahiliyya, da Daudar ta, Annabi mafi Girma (s. a. w) yana Ishara da irin wannan Ma’anar a cikin Hadisin da ya ce: ”Ni Addu’ar Annabi Ibrahim Ne (a.s) ” da kuma fadar sa (s. a. w) ’an Ciro Ni Ne Daga Tsarkakan Tsatso Zuwa Ga Mahaifa Tsarkaka, Kazantar Jahiliyya Ba Ta Shafe Ni Ba”.
Duk da kuwa Ita wannan Ruwayar ma ba ta da wata Kima a Bangaren Isnadi, domin iyakar abin da aka iya samu a cikin Littattafan da ke wurimu shi ne Nakaltowar da Arbili ya yi a cikin Littafin Kashful Gummah, ya ce: ’ja’afarus Sadik (a.s) Ya Ce: ”Abubakar Ya Haife Ni Sau Biyu” yana daga cikin abin da ya Kamata a Lura da shi cewa Wasidar dake Tsakanin Arbili da Imam Sadik (a.s) shi ne Hafiz Abdul Aziz Bin Akhdar Aljanabiziy kawai, wanda wannan bai wadatar ba sam sam, saboda haka ita Ruwayar ba ta da Kima a Ilmance.
Amsa Wannan Tambayar Taku, na Bukatar ayi Darasin Mas’aloli kamar haka:
- Me ake Nufi da Tsatso Masu Daukaka, da Mahaifa Tsarkaka,? Wadanda aka Ambata a cikin Tambayar?
- Shin Ruwayar da aka Ambata tazo ne daga Shi’a? kuma mene ne Isnadin Ruwayar?
- Idan ma ba’a Kalli Isnadin Ruwayar ba, mece ce Ma’anar ita Ruwayar?
- Game da Amsa Tambayar Farko, Wajibi ne mu Lura da cewa daga cikin Akidun da Tabbatacciya ce a cikin Akidun Shi’a cewa su Ma’asumai (a.s) Wajibine ya zamo Jerin Salsalar Dangantakarsu a Bisa Jerin Tsawonsa ya zamo daga Tsatso ne Madaukaka da Mahaifa Tsarkaka.
Hakan kuma ya Wajaba ne Saboda Kasancewar su a Mukami ne na Shiryar da Mutane, idan ya zamo Dangantakarsu ba ta kasance mai Kyau ba-Wa ‘Iyazu Bil Lahi-zai Jawo Munanawa a wurin Mutane da Kyamarsu da ga Mutane. [1]
Ayar Tsarkakewa ta na Ishara zuwa ga wannan Ma’ana din, haka ma akwai Ruwaya da aka Ruwaito daga Ibn Abbas a cikin fadin Allah (s. w. t. ) cewa: ”DA JUJJUYAWAR KA A CIKIN MASU SUJJADA”[2] Abin da ake nufi da Wannan Ayar shi ne Jujjuyawar da Annabi (s. a. w) ya ke yi a cikin Tsatso masu Tsarki, daga wani Mahaifin zuwa wani Mahaifin, har Allah ya Tayar da shi ga Annabci, Haskensa ya Bayyana a cikin Mahaifan sa, [3]
Haka kuma an ciro Ruwaya daga Annabi (s. a. w) da yake cewa: “An Ciro Ni Ne Daga Tsarkakan Tsatso Zuwa Ga Mahaifa Tsarkaka, Kazantar Jahiliyya Ba Ta Shafe Ni Ba”. [4]
Kuma ya Wajaba a san cewa Al’amarin Saduwar da ba ta Shari’a ba, ta Watsu Sosai a Zamanin Jahiliyya, har ta kai ga Ziyad Dan Baban sa, a saboda Rashin sanin Babansa na Gaskiya ana Danganta shi ne ga Baban sa (Majhuli) Wanda ba’a san shi ba, ko a Danganta shi da Uwarsa Sumayya. Saboda haka da a ce an Haifi Da a cikin irin wannan Yanayin, wanda Zina da Fasikanci ya Yadu a ciki, to su masu wannan Gidan sai ya zamo suna da wani Matsayi Babba a cikin Al’ummar. domin ci gaba da Bincike zamu kawo Shaida a kan abin da muka Fada.
Abu ne a Fili cewa Uwayen Imam Sajjad (a.s) da Imamul Hujjah (a. t. f. ) sun kasance ne daga ‘Ya’yan Manyan Kasar Iran, da Kasar Rum, wadanda su wadannan Mata Guda Biyu din, ko da yake su Mata ne masu Tsarki, to, Amma Kakan Shahara bano wato Hazru Buwaiz[5], shi ne Mutumin da ya kekketa Wasikar Annabi (s. a. w) a Lokacin da ya aiko masa yana kiransa zuwa ga Musulunci, har Annabi Muhammadu (s. a. w) ya Tsine masa, kuma Laifuffukan sa Tarihi ya Tabbatar da su.
To Amma a bisa ga Wannan Aya mai Daraja[6], Sunnar Allah tana Jazawa a Haifi Mumini daga Zuri’a na Kafiri haka ma akasin hakan, kamar Misalin Dan Annabi Nuhu (a.s) da wasu daga cikin ‘Ya’yan A’imma (a.s).
-Saboda haka Amsar mu ta Wannan Tambaya ta Biyu Shi ne cewa: Ita Wannan Ruwaya Marhum Marigayi Arbili shi ya Ruwaito ta a cikin Kashful Gummah [7] tana nufin Mahaifiyar Imam Sadik (a.s) ita ce ‘Yar Alkasim Dan Muhammad Dan Abubakar. haka kuma Daya daga cikin Kakaninsa as Mata, ita ma ta fito ne daga Zuri’ar Abubakar, abin da yake da muhimmanci kuma ya dace mu fada a nan, shi ne shi Marigayi Arbili da Gaske ne ana Kidaya shi daga cikin Manyan Malaman Shi’a Imamiyya, to amma ya ciro Ruwayar ne daga Littafin Sifatus Safwa na Ibnul Juziy, wanda shi kuma ana Kirga shi ne a cikin Malaman Ahlus Sunnah, kuma da yawa Malamam mu sun ce shi Mutum ne mai Rauni. a saboda haka wannan Ruwaya ba ta da wani Isnadi mai Karfi, wanda za a iya Dogara da shi.
Ko da kuma mun kau da Kai daga Isnadin shi Hadisin, to a cikin Ma’anar da Hadisin ya Kunsa Babu wani Cin karo da irin kalmomin da suka zo a cikin wannan ziyara din, game da abin da ya kebanci Dangartakar Ma’asumai (a.s). domin kuwa kamar yadda muka bayyana ne cewa abin da ake nufi da Tsatso masu daukaka da Mahaifa tsarkaka shi ne cewar ubanni da uwaye na Annabawa da Wasiyyai (a.s) ya Wajaba ya zamo sun Tsarkaka daga barin Kazanta na Zina da Fasikanci da Fajirci.
Kuma idan muka yi Darasin Silsila na Imamai as zamu ga wannan Hakikar a Fili. to, Amma wai ya zamo Dukkanin Ubannin su da Uwayen su, ya Wajaba su kasance Dukkan su Ma’asumai ne, to, wannan ba da’awace ta Shi’a ba Balle ya Wajaba Mana mu kare ta, domin ga Misali da yawa daga cikin Annabawan Bani Isra’ila sun kasance daga Tsatso ne na Daya daga cikin Yan’uwan Annabi Yusuf (a.s) wanda a bisa wani Mikdari na Musamman za a samu sun yi Tarayya da ‘Yan uwan Yusuf din wajen Zaluntar Annabi Yusuf din (a.s)
Wannan kuma duka idan ma an yi hukunci ne da ingancin ita Ruwayar, Alhali a Fili yake cewa ita Ruwayar ba ta da wata Kima a Bangaren Isnadi, domin mafi yawan kawai abin da aka samu din a cikin Littattafan da ke wurin mu shi ne Nakaltowar da Arbili ya yi a cikin Littafin Kashful Gummah kamar haka: ’ja’afarus Sadik (a.s) Ya Ce: ”Abubakar Ya Haife Ni Sau Biyu” yana daga cikin abin da ya kamata a lura da shi cewa Wasidar da ke tsakanin Arbili da Imam Sadik (a.s) shi ne Hafiz Abdul Aziz Bin Akhdar Aljanabiziy kawai, saboda haka Ruwaya ce ta Sunnah kawai, kuma tana da Nakasu a wajen Isnadi, wanda wannan bai Wadatar ba samsam, da za a Dogara da ita, saboda haka ita Ruwayar ba ta da Kima a Ilmance.
[1] suratul ahzab 33 inda allah ya ce: Ku Tabbata A Cikin Dakunan Ku Kada Kuyi Fita Irin Ta Jahiliyyar Farko Kuma Ku Tsaida Salla Kuma Ku Bada Zakka Ku Bi Allah Da Manzonsa Iyaka Kawai Allah Yana Nufin Ya Tafiyar Da Kazanta Ne Ga Barin Ku Ku Ahlul Baiti Kuma Ya Tsarkake Ku Iyakacin Tsarkakewa”
[2] suratush shu’ara’i, 219
[3] abul hasan ali ibnul hasan al mawardiydar wal maktabat hilal beirut hijira kamariyya 1409 almalisiy muhammad bakir biharul anwar juzu’i na 37 shafi na 63 mu’assasatul wafa beirut 1404 kamariyya.
[4] al askalani ibnu hajar. al’isaba fi tamyizis sahaba juzu’i na uku shafi na 537
- darul kutubul ilmiyya beirut 1415 hijira kamariyya.
[5] wannan maganar tana gudana ne kawai idan akayi hukunci da ingancin cewa sayyida shahar bano ita ce yar kisra, domin akwai mutane masu yawa masu bincike da suke shakkar wannan al’amari
[6] suratur rum aya ta 19 allah ya ce: ’yana Fitar Da Rayayye Daga Matacce Kuma Yana Fitar Da Matacce Daga Rayayye Kuma Yana Raya Kasa Bayan Mutuwar Ta Kuma Da Haka Zaku Fito”
[7] arbili ali dan isa kashful gummah, juzu’i na 2 shafi na 160, maktabatu bani hashim, tabriz, hijira kamariyya
- at tabrisiy fadhlu dan hasan, mujma’ul bayan fi tafsiril kur’an. juzu’i na 5 shafi na 102.