advanced Search
Dubawa
5126
Ranar Isar da Sako: 2014/11/03
Takaitacciyar Tambaya
Akwai tuhumar da ake wa Annabi cewa ya koyo kur’ani daga wani mutum ba’ajame, mene ne labarin wannan kissa?
SWALI
Me ya sanya kafirai suke cewa muhammad ya koyo kur’ani daga wani mutum ba’iraniye mai suna ruzbe?
Amsa a Dunkule
Kur’ani littafi ne da yake matsayin littafin cikamakin annabawa (s.a.w) wanda yake kumshe da mu’ujizozi masu tarin yawa, ayoyin da suka fara sauka daga cikin kur’ani yawancinsu sun gigita zukatan mutane, daga fasahar su da balagarsu wanda ya kasance tare da ma’anoni cikin zirin lafuzza kyawawa takaitattu kuma shi ma kur’ani ya bayyanar da su.[1] Mushrikai a kokarinsu na hana tasirin wannan kira na Allah cikin zukatan al’umma sun yi bakin kokarinsu cikin katange mutane daga jin wannan kira, cikin tsammanisu zasu iya hana yaduwar wannan haske na kur’ani cikin zukatan al’umma.
Wasu lokutan sukan ce, me yasa Allah bai turo mala’ika da wannan kur’ani, wanda Allah ya ba su amasa da da cewa {idan ma mun aiko mu su mala’ika tabbas zamu sanya shi da suran mutum za kuma ma tufatar da shi da abin da suke sanyawa}[2]
Wani lokacin kuma zasu ta kawo uzururruka ta yadda ta kai ga suna neman cewa a saukar musu da takardun kur’ani daga sama su taba su da hannunsu, sai dai cewa wannan ba bakon abu ba ne, sabaoda haka ma Allah cikin kur’ani  yake ce musu koda ma mun saukar ta takardun kun gansu kun karanta su  duk da haka kafirai zasu ce wannan ba wani abu ba ne face tsafi da sihiri.
Wani karon domin ragewa kur’ani daraja, sai su ce kawai shi tatsuniyoyin tarihi ne, suka ce kur’ani littafin tatsuniya ne kawai wanda da yake nakalto kissoshin mutanen da suka gabata saboda haka nema suke cewa: {lokacin da wadanda suka kafirce suke shirya maka makirci domin su tabbatar da kai ko su kashe ka ko kuma su kore ka, suna shirya makirci Allah yana warware makircinsu Allah shi ne mafificin masu makirci} [3].
A cikin wannan lokaci dukkanin shubuohinsu suka rushe ba su kai ga cimma wata natija ba, a lokacin da suka tsinkayi mutane sun ga balaga da fasahar kur’ani, sai suka kirkiro wani sharrin suka ce wannan kur’ani ba littafin Allah ba ne kadai kirkirar malaman muhammadu (s.a.w) ne. sai kur’ani ya yi musu martani da: {mu mun san cewa lallai su suna cewa kadai dai wani mutum ne ke koyar da shi (kur’ani bisa hakika) harshen wanda suke karkata zuwa gare shi ba’ajame ne  wannan kuma wannan kur’ani harshe ne balarabe} [4].
Gaskiyar magana shi ne cewa mushrikan larabawa da suke cewa ba zasu iya samun wanda zasu danganta kur’ani gare shi daga cikinsu su larabawa sai suka fake da shirya makida suka tashi suka yi yunkuri wajen binciko wani mutum wanda yake ba a san shi ba sai su danganta kur’ani gare shi ta yadda bayan wasu yan kwanaki cikin sauki su gafalar da mutane daga kur’ani.
Tambaya kan cewa menene hadafin wannan shubuhar? Cikin tsammani zamu iya amfanuwa da wannan aya.
 1.  menene manufarsu cikin wannan tuhuma da kage na cewa mai karantar da annabi (s.a.w) lafuzzan kur’ani wani mutum wanda ma kwata-kwata bai san harshen larabaci ba! Wannan karshen tonuwa asirinsu ce, sannan wannan ba wata karfaffiyar shubuha ba ce, sannan a gefe guda ta kaka wannan ba’ajame da ya jahilci yaren larabci za a ce ya kawo wannan jumloli masu cike da balaga da fasaha wanda ma’abota salin yaran baki dayansu sun gaza gabansu kai hatta ta kai ga ba su da karfin gwiwa da ikon iya kalubalantar sura daya daga kur’ani?
 2. manufarsu shi ne cewa Annabi (s.a.w) ya karbo abin da ke kumshe cikin kur’ani daga wani ba’ajame, wannan ma zamu ce zuba abin da kur’ani ya kumsa cikin zirin wadannan lafuzza da jumloli masu gajiyarwa wadanda dukkanin masu fasahar larabawa na baki dayan duniya suka durkusa masa suka gaza gabansa, ta hanyar wane mutum ya faru? Shin hankali zai yadda cewa wani mutum ne ba’ajame da ya jahilci larabci ko kuma ya faru ne ta hannun wani mutum da ikonsa ya shallake ikon dukkanin mutane?
Cikin kowanne hali wannan shubuha, wani batu ne sabo da ya kasance domin nesanta mutane daga kur’ani; Allah Ta'ala ta hanyar amfani da harshen larabci da bayyanarwa kur’ani sai ya ba su amsa da cewa: malaman da kuke danganta kirkirar kur’anu zuwa gare su mutane ne wanda ba ma larabawa ba ne, duk da cewa zasu iya cimma kololuwar adabin larabci, sai dai cewa a wannan zamani  ma’abota fasahar larabawa da balagar harshen sun kasance masu tarin yawa amma duk da haka sun gaza iya saka aya guda da ya rak misalin ayar kur’ani, ta kaka kuma wanda ba ma balarabe ne a ce zai iya zuwa wanda wannan kalami?!
Wanne mutum ne suke nufi da malamin Annabi (s.a.w)?
Kamar yadda aka ce: wanda kafirai suke nufi da malamin Annabi (s.a.w) wani bawan Ibni hadarami ne da ake kiransa da sunan Makisu, a wata magana an ce  akwai bayi biyu na ibn hadarami wadanda ake kira da Yasar da Jabar, ko kuma abin da suke nufi da shi shi ne wani bawa da ake kira da sunan Bal’am da ya kasance a makka, daga karshe dai wasu sun ce : Salmanul farisi [5] ne cikin wadanda ake tsammani akwai wani mutum da ake kira Ruzbe wanda ba ambaci ianahin sunansa ba in banda cikin sashin rubuce-rubucen Suyudi[6] da a cikinsu ya bayyana cewa wanda ake nufi da Ruzbu shi ne Salmanul farisi, wanda ake nufi da Ruzbe shi ne dai Salmanul farisi.
  
 
 
 

[1] Wujuhul I’ijazul kur’ani
[2] An’am:9
[3] Anfal:31
[4] Nahlu:103
[5] Suyudi jalal dini cikin littafin itkanul ulumul kur’ani juz 2 sh 322 bugun bairut darul kutubul arabi, shekara 1421
[6] Duraihi fakrud dini, majma’ul baharaini ju z 2 sh 70 bugun Tehran shekara ta 1375 kamari
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

 • ina aka samo asalin madogarar gabatuwar jagorancin malami
  8281 Tsare-tsare 2012/07/24
  Mas'alar jagorancin malami a matsayin shugaban al'umma a musulunci wani hakki ne da aka sanya shi ga wanda ya kai matakin ijtihadi. Wasu suna ganin lamari ne sabo a cikin fikirar musulunci, sai dai jagorancin malami a matsayin wani umarni na mai shari'a mai tsarki a lokacin ...
 • shin Imamul hujja a tsibirin bamuda yake zaune?
  14911 تاريخ بزرگان 2012/07/25
  Dalilin da ya sa wasu mutane suka yi ammanar cewa “Tsibirin Bamuda shi ne mazaunar Imamu Mahdi (a.s), gani suke Tsibirin Bamuda shi ne “Jazijrayul Khadra’a”. Bisa kaddara cewa Jaziratuk Khadra’a ita ce mazaunar Imamu Mahdi (a.s) shi ya sa suka ce Tsibirin Bamuda ya kunshi wadannan ...
 • Menene hukunchi namijin da ba ya iya biyawa matarsa hakkokinta?
  12493 2019/06/16
  dawwamar rayuwar aure da karfafarta ya dogara da soyayya da kauna da fuskantar juna da girmama juna. Domin iyali su samu tsayuwa da dawwama Addini Muslunci ya sanya hakkoki ga kowanne dayansu ya kuma ayyana musu wajibai a kansu, duk sa”ilin da aka ce akwai hakkoki to ...
 • menene dalili a kan tabbatar shugabancin malami.
  17279 Hakoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/26
  Akwai hanyoyi mabanbanta domin tabbatar da “shugabancin malami” sai dai a nan za mu isu da ambaton dalilai guda biyu na hankali da na ruwaya domin tabbatar da ita. Dalili na hankali: Hankali ya tabbatar da wajabcin samun mutumin da ke ...
 • Shin namiji na da wani fifiko a kan mace ta bangaren halitta?
  7667 Falsafar Musulunci 2017/05/21
  Da namiji da mace sun ginu ne a kan abu guda kuma sun samo asali daga tushe guda da kuma rai guda. Sai dai alakarsu da juna shine kan kai su zuwa ga kamala saboda haka ba wani hanya ma da za a iya kwatantasu a matsayin ...
 • mece ce alakar jagorancin malami da jam'iyyu?
  6470 Tsare-tsare 2012/07/24
  Kungiyoyin siyasa, da ma'anar wasu jam'iyyu masu iri-iri akwai su a cikin kowace al'umma tun zamanin da. A yanzu ana ganin jam'iyyun siyasa a matsayin wani abu na tarayyar mutane da 'yancin zabe ne. bisa wannan asasin ne ya zama dole mu kalli wannan lamari a matsayin ...
 • Menene Hukuncin musulmin da ya kashe kafirin da ba bazimme ba?
  6062 حدود، قصاص و دیات 2017/05/22
  Hukuncin musulumci kan kisa idan na gangan ne kisasi za a yi (Kisasi shi ne kashe wanda ya yi kisan kai) idan kuma ba na gangan ba ne diyya za abiya. Amma kafin a yiwa wanda ya yi kisan kai Kisasi akwai sharaDai da ya zama idan ...
 • mi ake nufi da makamta a ranar lahira?
  14494 Tafsiri 2012/11/21
  Abun nufi da makamta a cikin wannan ayar[i] da sauran ayoyi makamantanta[ii] ba shi ne rashin gani irin na duniya ba {wato mutun ya zamo bai gani da idanuwan da yake dasu} , sai dai abun nufi shi ne mutun da ...
 • Shin Dukkan Hadisan Da Suka Zo Game Da Mas’alar Auren Mutu’a Karbabbu Ne?
  15766 Dirayar Hadisi 2012/07/24
  Aure Mai Tsayayyen Lokaci Sunna ne daga Cikin Sunnonin Musulunci, Wanda Halaccinsa ya zo A Cikin Alkur’ani Mai Girma, Kuma Wannan Sunnar ta Gudana A Lokacin Manzon Allah Mafi Girma (s.a.w) da Lokacin Halifa na Daya, da Wani Sashi na Lokacin Halifa na Biyu, Har Lokacin da ...
 • mene ne dalilin haramcin marenan raguna?
  8146 Hikimar Hakkoki da Hukuncin Shari'a 2012/07/25
  Allah madaukaki mai hikima ne, kuma mai hikima ba ya yin wani aiki da wasa da babu hikima, saboda haka ne duk shi’a suka yi imani da cewa dukkan hukunce-hukunce suna kasancewa bisa maslaha ne, kuam a wasu wuraren an yi nuni da dalilin haramci a wasu ...

Mafi Dubawa