advanced Search
Dubawa
16485
Ranar Isar da Sako: 2018/10/01
Takaitacciyar Tambaya
Mene ne mafi muhimmancin abu a tarihin rayuwar annabi Ibrahim (a.s) bisa dogaro da ayoyi da ruwayoyi?
SWALI
Mene ne mafi muhimmancin abu a tarihin rayuwar annabi Ibrahim (a.s) bisa dogaro da ayoyi da ruwayoyi?
Amsa a Dunkule
Za a iya karkasa rayuwar Annbi Annabi Ibrahim (a.s) zuwa mtakai uku; kamar haka:
1. Matakin kafin annabta
2. Matakin annabta da fafatawa da bautar gumaka da tunkararsu
3. Matakin hijira daga Babila da kai-kawon fafutuka a Masar da Falasdinu da kuma Makka
1. Haifuwar Annabi Ibrahim (a.s)
An haifi Annabi Ibrahim (a.s) a kasar Babila a zamanin azzalumin sarki Lamarudu. An ce an taba gaya wa Lamarudun cewa a garinsa a wannan shekarar Za a haifi wani yaro da shi ne zai hallaka shi kana ya kawo karshen mulkinsa. A nan ne fa ya ba da umrnin kashe duk wani yaro da aka haifa a wannan shekarar, ya kuma ba da umurnin hana maza su sadu da mata da bincikar mata ko suna da ciki. Idan aka samu mai ciki sai a daureta har sai ta haihu. Idan namij ne a kashe, idan mace ce a kyale. Ana cikin haka mahaifiyar Annabi Ibrahim (a.s) ta samu juna biyu. Da ta yi kusan haifarsa sai ta gudu ta bar gari zuwa wani kogo ta haife shi. Sai ta nade shi a tsumma ta bar shi a agurin, sai ta sa wani dutse ta rufe bakin kogon, tana ta ziyartarsa a kai-akai har ya girma.
2. Annabtarsa (a.s)
Ba mu da masaniyar Annabi Ibrahim (a.s) ya na da shekara nawa aka aiko shi. Sai dai zai yiwu cewa ya samu wannan matsayin na annabta ne a lokacin da ya tattauna da baffansa Azara game da rashin tauhidinsa da batacciyar a kidarsa ta bautar gumaka.
Al’ummar Babila bayan bautar gumaka, su na kuma bautar kakakkun alloli da dama na halittun sama, kamar su rana da wata da taurari. A nan ne Annabi Ibrahim (a.s) ya shiga tattaunanwa da su a hankalce, a ilmance da ba su kwararan dalilai ta hanyar ba da hujjoji masu gamsarwa domin ya farkar da zukatansu daga barci ya bude idanunsu ya kawar musu da jahilci su hangi gaskiya.
Ya kasance (a.s) mai yawan tunani a game da sammai da kasa, da kuma tsarin zalunci na lokacin da nufin samarwa al’umma mafita. Ta haka ne zuciyarsa ta tumbatsa da hasken yakini har ya hangi zuzzurfar mulkin sammai da kasa “Haka nan muke nuna wa Ibrahim zuzzurfar mulkin sammai da kasa don ya kasance daga cikin masu sakankancewa”1
Matsayinsa na kyamatar gumaka da shirka ya yi ta kara karfafa kullum har ya kai mataki na Ilimi da ya sa ya tunkare su da kansa da nufin ruguza wadannan gumakan da aka jibge a gidan bautar gumaka da ke Babila.
3. Hijirarsa (a.s)
Bayan da Annabi Ibrahim (a.s) ya kamala abin da ya dace ya yi a wannan al’ummar, ta fuskar gyara zukata har sanda suka karkata zuwa gare shi suka yi imani da shi, sai ya ga ya dace ya bar kasar Babila shi da mabiyansa. Bisa manufar yada da’awarsa (a.s) ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen Sham, Falasdinu da Masar. To a lokacin ne ya samu damar kiran jama’a da dama zuwa bin Tauhidi da bautawa Makadaici Mai kowa.
 
Amsa Dalla-dalla
Kafin kutsawa bayanin rayuwar Annabi Ibrahim (a.s), muna ganin tilas mu yi nuni zuwa ga wasu abubuwa kamar haka:
A: Dailin girmama Annabi Ibrahim (a.s) da babban matsayinsa, shi ya sa dukanin ma’abuta saukakkun addinan nan uku suke danganta kansu zuwa gare shi da cewa suma mabiyan wannan Annabin ne mai girma. Sun kuwa hada da, Yahudawa da Nasara da duka ke tabbatar da dangantuwa ya zuwa gare shi.
Hakika Kur’ani Mai Girma ya yi isharar dangantakar inda ya yi martini gare su a fadinSa Madaukaki: “Ibrahim bai kasance Bayahude ko Banasare ba, sai dai shi ya kasance a kan addini ne mai kadaita Allah, bai kasance daga mushrikai ba”[1]
B: Sanannen abu shi ne manyan mutane kan fuskanci ibtila’i iri-iri da jarabawa daban-daban kamar shiga hadari masamman a wasu lokuta da yanayi misali; haifar Annabi Musa. Sannan yanayin haifuwarsu kan zo cikin wani yanayi da ba a saba gani ba. A irin wannan Musa (a.s)[2] da Annabi Isa (a.s)[3] da Fiyayyan Annabawa (s.a.w)[4] hakama Annabi Ibrahim (a.s), kowa tarinsa Shaida ce a kan abin da muka fada.
1. Haihuwar Annabi Ibrahim (a.s) da yarintarsa
Haifuwar Annabi Ibrahim ta zo ne a zamanin mulkin Lamarudu bin Kan’ana dan-kama-karya a yankin Babila yana da’awar allantaka wa kansa. Bautar gunki ba ta tatakaita a tsakanin jama’ar Babila su kadai ba, akwai wasu al’ummu da dama da bautar gumaka ya yadu cikiknsu da dama sun mika wuya ga bautar gumaka da wasu ababe da jama’ar Babila ke bautawa da suka mika musu wuya.[5]
 Hakika an haifi Annabi Ibrahim (a.s) a kasar Babila da aka santa da abubuwan ban al’jabi[6] a zamanin azzalumi Lamarudu. Ance an taba gaya wa Lamarudun cewa a garinsa a wannan shekarar za a haifi wani yaro wanda shi ne zai hallaka shi[7], da zai kawo karshen mulkinsa. A nan ne fa ya ba da umarnin kashe duk wani yaro da aka haifa a wannan shekarar, kuma ya ba da umurnin hana maza su sadu da mata da kuma bincikar mata ko suna da ciki, idan aka samu mai ciki sai a daureta har ta haihu, idan maniji ne a kaSha, idan mace ce a kyale. Ana cikin haka maifiyar Annabi Ibrahim (a.s) ta samu juna biyu. Da ta yi kusan haifarsa sai ta gudu ta bar gari taje wani kogo ta haife shi, sai ta nade shi a tsumma ta bar shi a agurin bayan da tasa wani dutse a bakin kogon. An ce tana ziyartarsa a kai-akai. Bayan fitarsa daga mabuya sai ya kalli taurari a lokancin wata yazo karshe sai ya ga tauraro ya bulla kafin wata sannan sai ya ga wata sannan ya ga rana sai ya fadi abin da ya fada. Da ya ga jama’arsa na bautar gumaka sai ya saba musu ya na mai aibata gumakansu har sai da al’amarinsa ya bayyana kana mukabala ta gudana tsakaninsa da su[8].
2. Yadda annabi Ibrahim (a.s) ya kalubalanci bautar gumaka.
Ba mu da masaniyar a shekarar da a aiko Annabi Ibrahim (a.s). Sai dai ta yiwu cewa ya samu wannan matsayin na annabta ne a lokacin da ya tattauna da baffansa Azara kan batun rashin tauhidinsa da batacciyar a kidarsa ta bautar gumaka. To wannan shi ne abin da ayoyi masu albarka suka yi nuni akai a Suratu Maryam; “Kuma ka tuna a cikin littafin Annabi Ibrahim, hakika ya kasance Annabi ne siddiki* a yayin da ya ce wa babansa Azara don me kake bauta wa abin da ba ya gani kuma ba ya ji kuma ba zai amfanar da kai komai ba* Ya babana hakika wani ilimi ya zo mini na abin da bai zo maka ba to sai ka bi ni in shiryar da kai tafarki madaidaici”[9]
Da ma al’ummar Babila bayan bautar gumaka ta na bautar wasu alloli da dama na halittun sama kamar su rana da wata da taurari. A nan ne Annabi Ibrahim (a.s) ya shiga tattaunanwa da su a hankalce a ilmance da ba su kwararran dalilai ta hanyar ba da hujjuji masu gamsarwa domin ya farkar da zukatansu daga barci ya bude idansu ya kawar musu da jahilci suka hangi gaskiya. Ya kawar musu da duhun kai ya haskaka tunaninsu na ainihi domin su cancanci karbar shiriya gadan-gadan su kuma tsirata kana su amshi shiya, su koma kamar yadda suke tun fil’azal bisa tafarkin kadaita Allah da dayanta shi[10].
Ya kasance (a.s) kamar yadda ayar ta siffanta shi, ya rayu a hali na lura zurfafa tunani a cikin halittar sammai da kasa da kuma ikon da ke tafiyar da halitta da kuma ingantaccen tsari da ke gudanar da ita (halitta) da kuma hasken da ya darsu a cuciyarsa na sakankancewa. “haka nan muke nuna wa Annabi Ibrahim zuzzurfar mulkin sammai da kasa don ya kasance daga cikikn masu sakankancewa[11]”. Da kuma fadinSa: “To yayin da dare ya rufe shi, sai ya ga wani tauraro, ya ce: “ Wannan ne ubangijina”! Sa’annan a lokacin da ya fadi sai ya ce: “Ni ba na son masu faduwa *To a yayin da ya ga wata ya fito sai ya ce: “Wannan ne ubangijina to a yayin da ya fadi sai ya ce: “Hakika idan Ubangijina bai shirye ni ba zan kasance daga cikin mutane tababbu* To a yayin da ya ga rana ta fito sai ya ce: “Wannan ne ubangijina wannan shi ya fi girma” Bayan ya fadi sai ya ce: “Ya ku jama’ata hakika ni na barranta daga abin da ku ke tarayya da shi* Ni na fuskantar da fuskata ga Wanda Ya yi halittar sammai da kasa ina mai mikewa dodar ban kasance daga cikin masu shirka ba[12]
Kalubalantar Bautar Gumaka A Ilmance
Wanda ke bibiyar tarihin Annabi Ibrahim (a.s) zai ga matsayinsa na kyamatar gumaka da shirka ya na kara karfafa kullum har ya kai mataki na Ilimi da ya sa ya tunkare su da kansa da nufin ruguza su wadannan gumakan da aka jibge a gidan bautar gumaka da ke Babila. Kur’ani Mai girma ya yi nuni inda ya ce: “Mamaki Wallahi zan yi wa gumakanku kakkarfar tanadi bayan kun juya kuna masu ba da baya* Sai ya sanya su gutsatstsari sai babbansu ko sa koma ya zuwa gare shi, sai suka ce ku kona shi ku taimaki gumakanku in kun kasance masu taimakonsu[13]”.
3. Hijirar Annabi Annabi Ibrahim (a.s)
Hakika gwamnatin Lamarudu ta fahimci hadarin wannan mata shin a kan daularsa, domin tayiwu ya wayar wa jama’a kai don fita daga kangin zalunci, ya kwance musu dabaibayin mulkin mallaka da tursasawa kan wannan al’umma. Shi ya sa ya nace sai an kona Annabi Ibrahim a wuta don amfani da jahilcin jama’a ya balbala ta don firgita mutane.
Bayan wuta ta kasance Sanyi da lafiya ga Annabi Ibrahim bisa umurni na Allah (s.w.t), sai gwamnatin Lamarudu ta firgita ta dimauce. Wannan ya zubar da kimarsu, domin sun zaci Annabi Ibrahim wani mata shi ne dan bani-na-iya mai neman suna a gun jama’a. Amma akasin haka sai ga shi ya bayyana a matsayin wani jagora daga Allah kana gwarzo jarumi mai iya fafatawa da kangararru shi kadai.
Wannan shi ya sa Lamarudu da yan kurensa da ke samun karfafa ta hanyar tsotse jinin talaka, suka tunkari Annabi Ibrahim (a.s) da dukkanin karfinsu.
A ta wata fuskar Annabi Ibrahim (a.s) ya kamala abin da ya dace ya yi a wannan al’ummar, ta yadda ya gyara zukata har suka karkata zuwa gare shi suka yi imani da shi, sai ya ga ya dace ya bar kasar Babila shi da mabiyansa. Bisa manufa ta yada da’awarsa (a.s) ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashen Sham da Falasdinu da Masar. To a can ne ya samu damar kiran jama’a da dama zuwa bin Tauhidi da bauta wa Makadaici Mai Iko[14].
Mataki Na Karshe A Manzancin Annabi Ibrahim
 Annabi Ibrahim (a.s) ya sadaukar da rayuwarsa ne a jihadin fafatawa da masu bautar gumaka masu cutar jama’a da sunan gumaka. Ya kuma samu damar haskaka zukatan muminai da hasken Tauhidi, ya dasa musu sabon ruhi, ya kuma kwato wasu jama’u daga kangin azzaluman mahukunta.
Bayan haka, to yanzu lokacinsa ya yi na kira zuwa ga Allah da sadaukar da komai a bisa wannan tafarki da tsantseni, domin kai wa ga mataki na jagoranci da yalwalkirji ta hanyar yi masa jarabawa ta Allah daban-daban. Kana a wannan lokacin ne ya ke gina Ka’aba domin ta zama gimshiki na kadaita Allah. Ya kuma kira dukkanin muminai ya zuwa gagarumin taro a farfajiyar wannan daki mai girma.
Hassadar Saratu matarsa ta farko ga Hajara wadda ya maidata matarsa da ta Haifa masa Isma’ila (a.s) ya tilasta dauke ta daga Falasdinu zuwa Makka bisa umurnin Allah, inda ya bar ta ita da danta a cikin sahara a tsakankanin duwatsu busassu, hannu-rabbana ba ko da ruwan Sha babu. Kana ya sake komawa Falasdinu.
Bayyanar ruwan Zamzam da zuwan kabilar Jurhum da basu izinin zama sun haifar da raya wannan yankin. “Ya Ubangijimmu hakika na zauna ni da zuriyata a wani kwari maras dausayi a gun DakinKa Mai Alfarma Ya Ubangiji na yi hakan ne don su tsaida salla, Ka sanya zukatan mutane su karkata zuwa garesu Ka kuma azurtasu da ‘ya’yan itace ko sa gude maKa” [15].
Yana da kyau abin da wasu masu tarihi ke hakaitowa cewa yayin da Annabi Ibrahim (a.s) ya ajiye matarsa da jaririnta Isma’il a Makka ya juya zai tafi, sai ta kira shi; ya Annabi Ibrahim, shin bisa umurninka ka zaunar da mu a fako babu ruwa babu wani mutum? Sai ya amsa mata a takaitace: “Ubangijina ne Ya umurce ni da hakan” Sai ta ce: Tun da dai haka ne Allah ba zai bari mu tozarta ba[16].
Hakika Annabi Ibrahim (a.s) ya Sha zuwa Makka don ziyartar dansa Isma’il. Daga cikin wadannan tafiye-tafiyen ne ya yi aikin hajji. Sai ya zo da Isma’il wanda a sannan mata shi ne mai kakkarfar imani magaskaci a mayanka da nufin sadaukar da shi bisa bin umurnin Allah. Bayan da ya amsa umurnin Ubangijinsa sai ya fito a wannan jarrabawa mai girma da babban matsayi. Allah (s.w.t) ne Ya karbi fansarsa, Ya kare masa Isma’il, Ya tura masa rago ya fanshe shi da shi[17].
Daga karshe bayan ya samu kyakkyawar nasara mai girma sai ya samu wani matsayi a mukamai wa danda mutum da wuya kan kai garesu, har takai Kur’ani Mai Girma na cewa: “Kuma a yayin da Ubangijin Annabi Ibrahim Ya gwada shi da wasu kalmomi ya kuma cika su sai Ya ce: “Ni zan sanyaka Imami, ya ce har daga cikin zuriyata! Ya ce alkwariNa ba ya samun azzalumai[18] da [19].
Matsayinsa (a.s) A Cikin Kur’ani
Ayoyi na Kura’ni suna tabbatar mana cewa Allah (s.w.t) Ya ba wa Annabi Ibrahim wani babban matsayi da bai ba wa wani Annabi daga cikin wadanda suka gabace shi. Za a iya jera su kamar haka:
Allah Ya ambace shi a matsayin <al’umma>: “Hakika Annabi Ibrahim ya kasnce al’umma mai mika wuya ga Allah kuma bai kasance daga cikin mushrikai ba” [20].
Matsayi na badadayi “Kuma Allah Ya riki Ibrahim badadayi” [21].
Lalle wasu ruwayoyi sun tabbatar da cewa: (Allah Ya rike shi a matsayin badadayi ne saboda bai taba hana wani ba, bai taba tambayar wani abu gun wani ba face Allah (s.w.t) [22].
“Ya na cikin zababbun Allah nagartattu”[23] “Kuma yana cikin salihan bayi”[24] “Yana cikin masu biyayya”[25] “Yana cikin magaskata”[26] Mai yawan kankan da kai mai yawan juriya”[27] “Yana cikin masu cika alkawuransu”[28].
Ya zo a ruwaya cewa Annabi Ibrahim mai yawan son baki ne[29] Ana masa lakabi da “uban baki”[30].
Ya kasance daga cikin masu dogaro ga Allah, ba ya neman wata bukata sai daga gare shi, ba ya nema gun waninSa[31].
Jarumi ne mai fito-na-fito domin shi daya ya tunkari sansanin masu bautar gumaka. Ba wani tsoro ya kalubalance su ya kakkarya gumakansu ya jibge. Ya tunkari Lamarudu da yan korensa ba tare da nuna tsoro ba[32].
Annabi Ibrahim (a.s) fasihi ne matuka gun iya zance, cikin ‘yan kalmominsa gajeru masu cike da hikima ya ruguza zantukan batattu. Ya dakushe hanzarinsu ta yadda ba za su iya fafatawa da shi ba. Ya kan tunkari lamura ta hanyar hakuri da juriya da ke fitowa daga yelwar kirjinsa. Za mu tabbatar da hakan ne idan muka kalli jayayyarsa da Lamarudu da babansa Azara dama sauran mahukunta yayin tattaunawarsa da su[33].
Hakika Kur’ani Mai girma ya dauki sallamawar Annabi Ibrahim zuwa ga Allah abin alfahri ga musulmi, kuma shi ne ma ya kira su da suna Musulmi[34]..
Ya tsara gimshikan hajji bisa umurnin Allah, shi ya sa a ibadun hajji ko’ina akwai sunansa. Kowe musulmi tilas ya ambaci wannan babban mutum a aikace-aikacensa na farillan hajji yana mai jin girmansa a zuciyarsa. Yin aikin hajji ba tare da ambatan Annabi Ibrahim (a.s) ba ya zama shiririta[35].
 Ya yanka tsuntsaye hudu ya kuma raya su da izinin Ubagijinsa[36]. An karbo daga Sahal daga Abu Abdullahi (a.s) a fsdin Allah (s.w.t) “To ka kama tsuntsaye nau’i hudu ka kididdige su ka sanya su tsibi-tsibi a ko wane dutse” Ya ce: Sai ya kama alhudahuda da gauraka da dawisu da kuma hankaka. Sai ya yanka su ya cire kawunansu ya ajiye a gefe guda, sai ya dandaka namansu da gashinsu da kasusuwansu suka yi laushi lukui, sai ya kasa su ka shi goma ya sanya su a kan duwatsu goma, sai ya ajiye ruwa da kwaya a kusa da shi, ya sanya bakunansu a tsakankanin yatsunsa, sai ya ce musu: Ku tafo da sauri da izinin Allah! (s.w.t). Sai gutsatsari suka rika tasowa nan da can tsoka da kashi da gashi suna tattaruwa har sai da halittar kowane ta kammala sai kowane jiki ya taso ya hade da kan nasa. Sai Annabi Ibrahim (a.s) ya saki bakunansu sai suka mike suka sha ruwa suka caki kwaya. Sai suka ce: Ya Annabin Allah Ya raya ka kamar yadda ka raya mu. Sai Annabi Ibrahim (a.s) Ya ce; Ai Allah shi kadai ke rayawa Ya kashe[37], [38].
 Wani matsayi da Annabi Ibrahim (a.s) ya rabauta da shi, shi ne fadinSa (s.w.t): “haka nan muke nuna wa Annabi Ibrahim zuzzurfar mulkin sammai da kasa don ya kasance daga cikikn masu sakankancewa”[39].
 

[1] Aali Imrana: 67.
[2] Dahe 38-39 “Domin mun aiko zuwa mahaifiyarka muka kimsa mata abin da ake kimsawa a cikin Sha’aninka. Shi ne ki jefa shi cikin akwatu, kuma ki jefa shi tare da akwatun nan cikin kogin Nil, magaucina magaucinka zai dauke shi Na jefa soyayya daga gareNi a gareka. Kuma don a rene ka a bisa kulawata.
[3] Maryam 20-21 “Ta ce ‘ya’ya zai zamana ina da da wani mutum bai tabe ni da aure ba kuma ban kasance mazinaciya ba* Ya ce: Al’amarin ai haka yike Ubangijinki Ya ce: Shi mai sauki ne a gare shi dom Mu san ya shi mamaki ga mutane da kuma rahama daga gareMu kuma ya kasance lamari ne abin hukuntawa”.
[4] Duha 6-8 “Shin bai sameka maraya ba Ya tattaraka ga (Abudalib)* Bai sameka kana mai nema ga Ubangij ba Ya shiryaka izuwa gare shi? Ya same ka mabukaci ya wadataka”.
[5] Annajafi Khumaini, Muhammad Jawa’ad Tafsiru A’sa’an j9 sh 7, dabaa’in IntiShara’at Islamiya a Tehran, daba’i na farko 1398 K.
[6] Daga Sa’id bin Zubayer ya ce: Na ji Zainul Abidina Aliyu dan Huseina (a.s) yana mai ce wa: Imamu Mahdimmu ya hada sunoninsa irin na annabawa (a.s). Akwai sunnar Annabi Adamu da sunnar Annabi Nuhu da sunnar Annabi Ibrahim da sunnar Annabi Musa da sunnar Annabi Isa da sunnar Annabi Ayuba da kuma sunnar Annabi Muhammadu (s.a.w), Ta Annabi Adamu da Nuhu su ne tsawon rayuwa, ta Annabi Ibrahim da Musa sune haifuwarsa a boye da gujewa muta ne. (Al’allama Majlisi j 15 sh 217, MU’assasatul Wafa’a Berut Lebanun 1404 H.
[7] An samu sabani dangane da yadda aka gano hakan wasu sun cewa bokaye suka fada masa, wasu suka ce an samo ne daga cikin littafan annabawa (a.s) da suka gabata, a wani kaulin kuwa cewa a ka yi Lamarudunn ne ya yi mafarki ya ga wani tauraro ya fito sai ya disashe hasken rana, sai aka fassara masa da cewa wani yaro Za a haifa da zai rushe mulkinsa.
[8] Addabrisi, Majma’ul bayan fi tafsiril Kura’an j4, sh 503, daba’in IntiShara’at Nasir Husein Tehran, 1372 SH.
[9] Maryam 41-43.
[10] Dubi tafsirin A’sab j 8, sh 8
[11] Al’an’am 75.
[12] Al’an’am 76-79.
[13] Al’anbiya’u 57-68.
[14] Makarim shirazi, Nasir, Al’amsal fi tafsiri kitabillahi almunazzal, j7, sh548.
[15] Ibrahim: 37.
[16] Alkulaini, Alkafi j4, sh201, Darul kutubul Islamiya Tehran 1765 H.
[17] Domin karin bayani sai ka dubi suratu Saffa’at 100 -107.
[18] Albakara 124.
[19] Dubi Al’amsal fi tafsiri kitabillahi Almunazzal j 7s, sh: 548-550.
[20] Annahal: 120.
[21] Annisa’a: 125.
[22] Ashshek Sadouk, Uyunul Akhbar Rida (a.s),j 2, sh76, IntiShara’at Jeha’an, 1378 H.
[23] Sa’ad 47.
[24] Annahal: 122.
[25] Annahal: 120.
[26] Maryam: 41.
[27] Attauba: 114.
[28] Annajam: 37.
[29] Dubi Azzari’at. 24-27.
[30] Abulfutuh Arraziy, Husein bin Ali, Raudul Jana’an wa Ruhul Jana’an fi tafsiril kura’an. j 18, sh 191. Markazu daraja’at Islamiya ASta’an rdawi Mashhad1408 H.
[31] Ashshu’ara: 78-82.
[32] Anbiya’a: 57-63.
[33] Anbiya’a: 63-67.
[34] Alhaj: 78.
[35] Alhaj: 27.
[36] Albakara: 260.
[37] Assadouk Alkhisal j 1, sh 265, dabaa’in Jami’atul Mudarrisen, Kum, 1403 H.
[38] Dubi Al’amsal fi tafsiri kitabillahi Almunazzal j 7, 550-552.
[39] Al’an’am 75; An ruwaito cewa Abubasir ya tambayi Ja’afrussadik (a.s): shin Annabi Muhammadu ya ga malakutun Allah kamar yadda Annabi Ibrahim (a.s) ya gani? Sai ya ce: E, ya gani mana. Nima na gagi haka, Imamai da za su zo a bayana. Abuja’afar Albakir (a.s) ya ce a tafsirin fadinSa (s.w.t) Ya ce: “Kamar haka Muka nuna wa Annabi Ibrahim…) Ya ce: “An masa kaShafi sammai bakwi ya kalli komai da kassai bakwai ya kalli komai da abin da ke cikinsu, shima Annabi Muhammadu (s.a.w) an masa haka kamar yadda aka yi wa Annabi Ibrahim (a.s), haka nima an nuna mani, kana Za a nuna wa sauran Imamai a bayana. Dubi Alkhara’ij wal Jawarih,j 2, sh 867, Mu’assatul Imamul Mahadi (AJ), Kum, 1409 H.K.
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

MPANGILIO WA KIMAUDHUI

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa