Please Wait
13761
- Shiriki
Wa’azi yana nufin isar da sakon Allah (s.w.t) zuwa ga jama’a. Kasantuwar sakonin Annabawa a dunkule abu guda ne, sannan sakon Fiyayyan Annabi (s.a.w) na masamman ne, da ya zo da nufin shiryar da bil Adama don fitar da shi daga duffai zuwa ga haske. A bisa haka ne ya samu mahimmanci na masamman kassntuwarsa hanya ce ta isar da sakon Wahayin Ubangiji zuwa ga bayi. A nan za mu iya karkasa hanyoyin yin wa’azi a Musulunci zuwa matakai uku: Wa’azi na fatar baki da na rubutu da kuma na aiki. Kowane ta nata salon da rawar data kan taka. Na fatar baki ya hada da yin jawabai a wuren yin Ashura, mukabala, umurni da yin kyakkyawa da hani da yin mummuna da dai sauransu. Shi kuwa salon rubutu ya hada da tura littatafai da rubuce-rubuce. To haka shi ma salon na ilimi ya kunshi nau’i iri-iri da za mu ambata wajen ba da amsa dalla-dalla.
Wa’azi ya na nufin isar da sakon mazanci a ta han’yo’yin da suka dace ta amfani da dabaru na musamman.
Dukkan addanai da sakonnin Allah da mazhabobi na nazari -a tsawon zamunna- sun dogara ne da wa’azi a matsayin hanyar isar da sakonninsu, kana sun yi amfani da han’yo’yi da dabaru daban-daban a wannan fagen. Sannan wa’azi yana da wani matsayi na musamman a Duniyarmu ta yau don kai sako a bangaren da ya shafi Akidu da nazarce-nazarce da samun dammar yaduwa gagaruma a ta wannan fuskar a matakai daban-daban. Lalle malamai da suka kafa wadannan cibiyoyi sun yi matukar kokari don jawo hankulan jama’a suka kirawo mabiya da mataimaka da masu mara baya da sauransu.
Kasantuwar Sako na Musulunci shi ne karshen sakonni kuma mafi kamalarsu, da ke dauke da sakon madauwami zuwa ga dukkanin jama’a, zai zama ke nan, jigon wa’azi ne da sanarwa da kuma yadashi a Duniya –don bushara da gargadi- lalle ya zamana yana da matsayi na musamman mai muhimmancin gaske. Saboda Musulunci addini ne mai shiryarwa. Matukar jama’a suka gaza ganin kyawawan dabi’u da Sakon Musuluncin ke dauke da su, to ba za a samu a shiryar ba kamar yadda ake bukata. Domin shiryarwar sashe ne na kira zuwa ga Allah (ma’arifa).
A nan ya dace yin nuni zuwa ga han’yo’yin yin wa’azi a Musulunci da suka kasu gida uku a matakai daban-daban: Wa’azi na fatar baki da na rubutu da kuma na aiki,:
- Nau’o’i na wa’azin fatar baki ya kunshi salo iri-iri. Daga ciki akwai, jawabai, kiran Salla, karanta addu’o’i, karatun Kur’ani Maigirma, bukukuwa na farinciki (mauludi) da na bakinciki na bacin rai (Ashura) mukabala (tattaunawa), umrni da kyakkyawa da hani da mummuna. da sauransu
- SALO NA RUBUTU.
- TA HANYAR RARRABA Kur’ani Mai girma da ajiyeshe inda jama’a zasu karanta. Irin wannan salon yana da matukar tasirin gaske wajen shiryar da jama’a da kyatata dabi’u a bainal jama’a. To har a wannan zamanin hanyar tana da gagarumin tasiri. Lalle Kur’ani ya yi tsokaci zuwa ga wannan tabbacin yana mai muna hasken Littafi Mai girma: “Ya ku Ahlulkitabi hakika manzannimMu sun zo muku suna masu bayyana mafiyawa daga cikin abin da ku ka kasance kuna sabani a ciki na daga cikin littafi, kuma yana mai afuwa daga abubuwa masu yawa. Hakika haske daga littafi mabayyani ya zo muku daga Allah, kuma Allah Yana shiryar da wanda ya bi tafarkin yardarSa zuwa ga tafarkai na aminci, Ya kuma fitar dasu daga duffai ya zuwa haske da izininSa, kuma Ya shiryar da su ya zuwa tafarki maidaidaici[1]”
- DOGARO DA SALON YADA HADISAI. Yada hadisai da hikimomi manya manya wadanda aka samo daga Ma’aiki (s.a.w) da Imamai (a.s).
- AIKEWA DA LITTATAFI. Hakika. Annabin Girma (s.a.w) ya dogara da salon aiken wasiku tun a farko-farkon Da’awa ta Musulunci. A irin wasikun ne ya tura wasikarsa zuwa ga Najashi Sarkin Habasha. Hakika Annabin Girma (s.a.w) ya shiga aika wasiku bayan Sulhun Hudaibiya, bayan samun tabbaci na rashin cutuwa a gareshi ta hayar mushrikai. A salon a yada Da’awa a wajen Jaziratul Arab, ya aika wakilai biyu don wannan aikin suna kiran jama’a zuwa ga Tauhidi, su shiga Musulunci, ya rurrubuta wa sarakuna da shugabanni da malaman Addinin Kirista da shugabannin kabilu da shehunansu. Lalle ya ci gaba da wannan salon har ya zuwa karshen rayuwarsa[2]
- SALON WA’ZI A ILMANCE:
Musulunci ya karfafa salon na wa’azi matukar gaske da kuma ilmantarwa, ya ba su gagarumi muhimmanci babba, harma sai da ya zo a cikin fadinSa (s.w.t) ce wa: “Shin zaku umurci mutane da aikata nagarta, kuma ku mance kanku, alhali kuna karanta littafi. Shin ba zaku hankalta ba”[3]. Ya sake fadi a wani gurin: “Ya ku wadanda su ka yi imani, domme ku ke fadin abin da bakwa aikatawa?”[4] Kuma an ruwaito daga Imam Sadik (a.s). yana ce wa: “Ku zamana masu kiran mutane da ayyukanku, kada ku zama masu kira da harsunanku”[5] Hakika Annabi (s.a.w) da Imamai Tsarkaka (a.s) sun dogara da wannan salon ainun, domin yana daga cikin sifofin mai wa’zi fada-da-cikawa, ma’na ya yi ammanna da abin da ya ke kira ya zuwa gareshi. Harilayau Annabin Girma (s.a.w) da Imamai Tsakaka (a.s) sun yi amfani da hanyoyin bayyana mu’uzizozi da karamomi don yin wa’zi da tabbatar da gaskiya., don hakan yake da nasa tasirin mai girma wajen janyo jama’a zuwa Musulunci.
Buku-da-kari, akwai wasu lamura da Musulunci ya ba su muhimmaci mai girma a fagen wa’azi, kana yake ganin cewa riko da su yana da gagarumin tasiri na samar da sakamako mai kyau a fagen wa’azi da yada sako na Musulunci, da suka hada da:
- MAHIMMACI NA GURI:
Babu kokwanto guri na taka gagarumar rawa a fagen yada da’wa ta Addini da sadar da kalimar Addini zuwa ga bayin Allah. Annabin Girma (s.a.w) ya yi amfani da zuwan mahajjata Makka a lokacin aikin hajji don yin wa’azi.
Haka Imam Husaini (a.s). ya yi zango a Makka na watanni –a hanyarsa ta zuwa Karbala- da nufin mika sakonsa ga mahajjata da nufin tona asirin Ummayyawa da halifansu Yazidu la’nannan Allah.
Kuna Imam Sadik (a.s) ya tsaya a ranar Arfa a filin yana kira da babbar murya yana ce wa: “Ya ku mutane! Lalle Manzon Allah ya kasance shi ne Imami sannan sai Aliyu Dan Abudalibi sannan sai Hassan sannan sai Husaini snnan sai Aliyu Dan Husaini sannan sai Muhammadu Dan Aliyu (a.s). sannan sai wannan (ya nufin kansa).[6]
Guraren yin wa’azi su na da yawa daga ciki akwai Makka, da masallaci. Lalle masallatai suna da gagarumin tasiri wajen isar da sakon Allah a tsawon kafuwar tarihin Musulci. An ruwaito daga Annabi (s.a.w) yana ce wa: “Babu wasu jama’a da za su zauna a wata mazauna a daya daga cikin masallatan Allah (s.w.t) suna karanta Littafin Allah suna tilawarsa a tsakaninsu face natsuwa da rahama sun lullubesu kana Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da Shi. Kuma duk wadda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa ba zata iza shi gaba ba[7].
- WA’AZI A WASU LOKUTA NA MUSAMMAN:
Yana daga cikin abubuwa da mai wa’azi kwarerre ya kamata ya mora har da dama ta lokaci. Ayoyi na Kur’ani Maigirma da hadisai daga Imamai Ma’sumai (a.s). sun yi nuni ga wannan tabbacin karara.
Allah (s.w.t) Yana fadi a cikin LittafinSa Maigirma Yana mai nuni game da saukar Alkua’ani Maigirma: “Lalle ne Mun saukar da shi a daren Lailatun Kadiri”.[8] Sai Allah (s.w.t) Ya zabi fiyayyayen darare na Lailatun Kadiri cikin fiyayyen watanni watan Ramalana. Ku a san cewa umurni na bayyana sako ya zo ne bayan shekara ta uku da Aike Maigirma a fadinSa (s.w.t): “Kuma ka bayyanar da abin da aka umurceka kuma ka ka bujure wa mushrikai”[9]. Wannan ya isa ya nuna mahimmancin kayyade lokaci a gun yin wa’azi ko da’awa. Da bayyana daga mabuya zuwa sarari tsakanin kafurai da mushrikai, da bai riga ya bayyanar ba a can baya.
Alokacin da mushrikai suke kange Manzon Allah (s.a.w) da mabiyansa daga wa’azi suna hanasu isarda sakon Allah ya zuwa ga mutane sai Manzon Allah (s.a.w) ya rika amfani da watanni na alfarma da ba a yaki a cikinsu ya mike a kasuwannin Ukaza, Majinna da Maja’az yana mai kiram mutane da su bi Mikakken Addini. Domin su kafirai suna baiwa wadannan watannin tsarki na mussamman suna masu haramta yaki da zubar da jini a cikinsu, sai suka zama wata dama da babu irinta da Annabi (s.a.w) kan yi amfani da ita shi da sahabbansa ba tare da fuskatar wata tsankwama da cutarwa ko kuntatawa ba[10].
- FARAWA DA AMBATON SUNAN ALLAH (s.w.t).
Kasantuwar Allah (s.w.t) Shi ne hakikanin mai tasiri a kowane aiki kuma Shi ne kan sanya a dace a kowane aiki, zai zamana ke nan cin nasarar yana da alaka ne da ambatonSa (s.w.t). A nan za a zama gaya zama tilas a fara da fiyayyan sunaye watau sunan Allah. Yin hakan zai albarkaci aiki ta yadda zai bashi nagarta ta musamman ta cimma babbar manufa. A she ke nan babu wani mamaki kasantuwar ayoyin farko da suka sauka ga Ammabin Girma (s.a.w) sun fara ne da Bisimillah. “Ka yi karatu da sunan Ubangijinka Wanda Ya yi halitta”[11].
- KARBAR WAHAYI DAGA ALLAH.
Babu shakka komai iya maganar mutum da fusaharsa da zalakarsa zai iya fadawa kuskure ko son rai da son zuciya kan iya shiga. Amfani wahayin Ubangiji shi ne hanya daya tilo wadda da ita Allah zai dorashi bisa daidai. Tilas mai wa’azii ya yi riko da wannan igiyar (wahyi) da amfani da ita don cimma bukatarsa. Ma’ana dole mutum ya yi amfani da wahyin da Allah Ya yi wa AnnabinSa Maigirma (s.a.w). Wanna shi ne ake kira Tafarki Madaidaici.. “Kuma ka yi riko da abin da aka yi maka wahyi zuwa gareshi, lalle ne kana bisa tafarki madaidaici”[12].
Isarda sakon wahyi da Allah Ya turo wa Annabi (s.a.w) ya na nufin kai tataccen sako da babu son rai da son zuciya a ciki da sauransu.. “Kuma ba ya yin furuci bisa son rai* (Maganarsa) ba komai bace face wahyi da aka yiwo masa”[13].
- DOGARA DA DALILI DA HUJJA. Dogara da dalili da hujja da nisantar daga shiririta da ya sabawa magana da rashin sanin yakamata.
Hakika Kur’ani ya dogara da salo na ba da hujja da dalili, ta hakan ne yake kiran mabiya zuwa ga tafarkinsa “Ka yi kira zuwa ga tafarkin Ubangijinka da hikima da kyakkyawan wa’azi, kuma ka tattauna dasu da salo mafi kyatatuwa”[14]. Kana ya janyo hankalinsu da su nisanci hargowa da hayaniya kamar yadda Ya fada (s.w.t). Kuma yana kwabarsu da nisantasu daga hantara; kyara da zage-zage. Ubangiji (s.w.t) Ya ce: “Kuma kada ku zagi wadanda su ke kiran wanin Allah, sai su zagi Allah bisa adawa ba bisa sani ba”[15]. Za mu iya ganin yadda yake neman abokan hamayya da su zo da hujja a kan abin da suke kira na abin da su ke bi. “Ka ce ku kawo hujjoj inkun kasance masu gaskiya a bisa abin da kuke kira a kai”[16]. Da kuma “ To sai muka ce: to amma ku sani lalle ita gaskiya ta Allah ce. Amma sai suka bace bisa abin da suke kirkira na karya”[17].
- KWADAITARWA.
Bayan da Alkua’ani Maigirma ya kwadaitar da mutane da yin taikamako, kana sai ya hada da busharori masu yawa “Misalin wadanda ke ciyar da dukiyoyinsu sabo da Allah tamkar kwaya ce da ta fitar da zangarniya bakwai a kowace zangarniya akwai kwaya dari, kuma Allah Yana ninninkawa ga wanda ya so Kuma Allah Mai yawan yelwa ne Masani* Kuma wadanda ke ciyar da dukiyarsu a bisa tafarkin Allah ba tare da bibiyar abin da suka ciyar din da gori ko cutarwa ba suna da ladansu wajen Ubangijinsu kuma ba su da wani tsoro ko razani”[18].
- TSORATARWA DA GARGADI.
Lalle Kur’ani Maigirma ya kwadaitar da yin ayyuka na gari kana ya yi gargadi daga yin miyagun ayyuka na sonrai. Watakila fitattu daga cikin hanyanyoyi shiyarwar na Annabi su ne yin gargadi ga mutane da su guji sonzuciya da sakar wa rai ragama[19]. Ayoyi da dama sun yi bayanin abin da yake jiran kafurai da arna na narkon azaba a Ranar lahira “Hakika wadanda suka kafurce da ayoyin Allah suna da azaba mai tsanani, kuma Allah Mabuwayi ne Ma’abucin Daukar fansa[20].
- RASHIN TSORO A WAJEN ISAR DA SAKON ALLAH (s.w.t) DA KARANTARWAR ADDINI.
Hakika Kur’ani Mai girma ya kwadaitar da masu wa’azi na musulunci da kada su ji tsoran wani da ba Allah (s.w.t), kamar yadda ya zo a fadinSa (s.w.t) “Wadanda ke isar da sakonin Allah kuma suke tsoronSa basa tsoron wani sai Allah to Allah Ya isa Mai hisabi”[21].
Tabbas yin riko da wadanan kwararan dabarun da suka zo cikin Kur’ani Maigirma da hadisan Ma’asumai (a.s). da yin koyi dasu wani babban jigo ne na a aikace da ke yada Addinin Musulunci Mikekke dodar, kana jarrabawa ce kuma babbar hanya ce ta yin sahihin wa’azi.
[1] Ma’ida 15-16.
[2] Tarihin Ibin Jarir Dabari, j2, sh 882, tahakikin shaihin malami Naubakhti, bugun Mu’assasatul ilam Berut.
[3] Albakara, 44.
[4] Assaf, 2. Sai ka dubi littafin Alkur’an wattablig na shek Muhusin Karashi.
[5] Biharul Anwar j5, sh: 189.
[6] Kulaini Muhammad bin Ya’akub a littafin Furu’ul Kafi j4, sh 466, bugun Darul Kutub Islamiya, Teheran.
[7] Annuri Addabarisi Alh. Mirza Husaini. Mustadrikul wasa’il, j 3, sh 363, bugun Madba’atul Islamiya Tehran.
[8] Suratul Alkadir 1.
[9] Suratu Hujur 94.
[10] Ayatullahi Subahani Furu’uddin j 1, sh 326. bugun Intishara’atul Huda 1360 AH.
[11] Suratul Alak 1.
[12] Suratu Zukhruf 43.
[13] Suratu Najam 3-4.
[14] Suratu Nahal 125.
[15] Suratu An’am 106.
[16] Suratu Bakara 111.
[17] Suratu Kisas 75.
[18] Suratu Bakara 261-262.
[19] Suratu Bkara, 277.
[20] Suratu ‘Ali Imrana 4.
[21] Suratul Ahzabi, 39.