advanced Search
Dubawa
4632
Ranar Isar da Sako: 2012/04/03
Takaitacciyar Tambaya
An samu ruwaya ginanniya kan cewa Allah (s.w.t) ya haramtawa yayan Fatima shiga wuta, ina rokon a warware min wannan Magana
SWALI
Ina rokon a bayyana min matsayin wannan hadisi ta fuskacin dangane daga Manzo (s.a.w) cewa: “hakika Fatima ta kiyaye farjinta sai Allah (s.w.t) ya haramtawa ya’yanta (zuriyarta) shiga wuta” bihar bolume 43 page 20, 23, 232
Amsa a Dunkule
Wannan ruwaya an rawaitota daga litattafan Shi’a da na sunna, ana kuma ganinta daga ingantattu sabida yawan rawaitatta da aka yi da kuma litattafan da tazo daga ciki, saidai yadda ake ganin yanayin da tazo da shi na farko wajan game sukkan yayan Fatima a ciki, zamu iya fahimta daga wata ruwaya cewar ya’yan Fatima da aka yi wa wannan busharar su ne wadanda suka kame kansu daga zunubi, sabo da tsarkinsu da kamewarsu, ko kuma saboda kamewarta suka zamo amana daga shiga jahannama, ko kuma wanzuwarsu cewa su zuriyarta ne ya zama suna da iyakar da ta kare musu azaba, idan sun kasance tasgatattu ne na daban.
Amsa Dalla-dalla
An samu ruwaya cikin bihar da wannan yanayin da cikckken dangane daga imam ridha (a.s) daga iyayensa ya ce: Manzo (s.a.w) ya ce: “Hakika Fatima ta kiyaye farjinta sai Allah (s.w.t) ya haramtawa ya’yanta (zuriyarta) shiga wuta”[1]. Haka wannan ruwaya akwaita cikin littafi uyun akhbarur Ridha (a.s) wanda yake a Bihar da wannan lafazi[2].
Hakanan wannan ruwaya an fadeta cikin litattafai da dama, hakanan daga marawaita hadisi daga Shi’a da sunna, kuma anyi duba tare da tambayoyi da yawa a kanta[3]. wanda wannan ma ke iya nuni zuwa ingancinta tare da sallama mata. Wasu daga mawallafan sunna a karni na goma bayan karatunsa game da ruwaya ya isa zuwa natijar ingancinsa da ya ciro daga wannan ruwaya cewa danganensa ingantacce ne, ita ba wai na daga duban da wasu ke yi bane, kamar yadda wasu suka bayyana a wasu litattafan[4], amma abin da ya cancanci bincike da tattaunawa cikin wannan ruwaya shi ne fadin maganarsa da gamewarsa. Shin ka samu ayyanannen daya na zuriyarsa ko ta hada da dukkansu? Amma abin da muka iya fitrwa daga ruwayar Shi’a kamar na nuni cewa wasu daga shuwagabanni na ganin ingancinsa da hasken da ya samu daga Allah (s.w.t) tare da sauwwara asasin wannan hadisi cewa an gafarta musu duk zunubansu ne, kuma bazai kaisu zuwaga azaba ba!!, amma imamai ma’asumai (a.s) sun tsaya kan wannan istinbadi da tsanani suka sanar cewa misalin wannan ruwaya dole kada ayi mummunan aiki da ita ta bangaren masu zargi ga Ahlul-bait (a.s) kuma sukayi nuni zuwa wasu daga wadannan ruwayoyi:
  1. Daga Hassan dan musa ya ce na kasance a khurasan tare da imam Ali ridha (a.s) a wajan zama (majlisi) tare da Zaid dan musa (dan uwan imam riza wanda aka fi sani da Zaidun nar) zaidu dan Musa ya fuskanci wasu mutane a mazaunin yana yi musu alfahari yana magana, a lokacin abul Hassan na magana ga wasu mutane, sai imam yaji maganar zaidu ya juyo ga zaidu ya ce dashi: ya zaid baka samu maganar da mutanen kufa suka rawaito ba cewa: Fatima (a.s) ta kiyaye farjinta sai Allah (s.w.t) ya haramtawa zuruyrta shiga wuta! Ba kan kowa take ba sai kan Hassan, Husain, da dan cikinta kawai, koda imam Musa (a.s) ya bi Allah (s.w.t) ya azumci rana, ya tsaya cikin dare, kai ka saba masa sannan kuzo ranar alkiyama daidai, ko kuma ma kafishi wajan Allah (s.w.t)? Hakika imam ya fadi wannan ne game da wadanda sukayi aiki na gari daga cikinmu[5]. An samu daga wasu ruwayoyi masu kama da wannan ruwaya[6].
  2. Daga hammadu dan Usman ya ce nace da abi Abdullah (a.s): raina fansa gareka mene ma’anar fadin Manzo (s.a.w) cewa “hakika Fatima (SA) ta kiyaye farjinta sai Allah (s.w.t) ya haramta wuta ga zuriyarta (ya’yanta)”? Sai Imam ya ce: ‘yantattu daga wuta su ne dan cikinta, Hassan da Husain (a.s), zainab da ummu kulthum (SA)[7].
  3. Wani mutum ya ce da Imam Ja’afar (a.s) kuna ganin fadin Manzo (s.a.w) cewa: “Hakika Fatima ta kiyaye farjinta sai Allah (s.w.t) ya haramtawa ya’yanta (zuriyarta) shiga wuta”. Shin wannan ba zai zama amana ga dukkan ya’yan Fatima a duniya ba kuwa? Sai Imam Ja’afar ya ce: kayi wauta, ana nufin Hassan da Husain (a.s) ne kawai domin su ne tushen Ahlul-bait (a.s), duk wanda ba su ba idan yaki yin aiki nasabarsa da Fatima (a.s) bazata kaishi ba[8].
na’am akwai wasu ra’ayoyi da zamu iya fahimtar wanin wadancen ukun da muka ambata[9]. Sai dai ba zamu iya karbaba domin ta sabawa usul da tsarin musulunci da kurani, domi ma’anarta shi ne yanci kai tsaye wajan zuwa da mummuna da kariya daga azaba, duk da cewa munyi imani an kebace wasunsu, sai dai wannan saki baiyi daidai da koyarwar addini ba, amma tsarin yayan Zahra (SA) na nufi tazgacewar da Allah (s.w.t) ya yi mata sakamakon kamewar babarsu Zahra (SA), suma suka kame kansu domin koyi da ita daga dukkan zunubi da sabo tare da zabinsu kan hakan (yin aikin alkhairi ko na sharri).
 

[1] Majlisy, Muhammad albakir, bihar bolume 43, page 20, mu’assasatul wafa’a Beirut 1404;
[2] Sheikhus saduuk uyun akhbarur ridha (a.s) bolume 2, page 63,nashr jihan, Dhahran, 1378;
[3] Ibn shahr aashuub, munakibu aali abi dalib, bolume 3 page 325, nashrul aammah; Kum, 1379;
[4] Assalihy, ashshamy, subulul huda war rushd fi sirstu khairul ibad, bolume 11 page 250, darul kutubul ilmiyya Beirut, 1414
[5] Sheikhus saduuk, uyun akhbarur ridha (a.s) bolume 2, page 232, bolume 1;
[6] Al irbily, Aliyyu dan Musa, kashful gumma, bolume bolume 2, page 310, maktabatu bany hashimy Tariz, 1381;
[7] Sheikhus saduuk, muanil akhbar, page 106nashru jama’atul madrasatain Kum, 1361,.
[8] Ibn abil hadeed, sharhi nahjul balagah, bolume 18 page 252, maktabatu ayatullahil mar’ashy, Kum 1404.
[9] Arrawandy, kutbuddeen, alkhara’ij wal jara ih, bolume 1 page 281, mu’assasatul imamul mahdy (AF), Kum, 1409
TARJAMA YA JAWABU KATIKA LUGHA NYENGINE
Mahanga
Idadi ya maoni 0
Tafadhali ingiza thamani
Imel : Yourname@YourDomane.ext
Tafadhali ingiza thamani
Tafadhali ingiza thamani

Tambayoyi Masu Fadowa

Mafi Dubawa